Magoya bayan Ingila sun yi wa 'yan wasansu ihu

Ingila

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wasa ɗaya Ingila ta ci cikin uku a wasannin cikin rukuni

Martanin da wasu magoya bayan Ingila suka mayar kan rawar da tawagarsu ke takawa a gasar Euro 2024 na jawo "yanayi na musamman" da ke "taɓa 'yan wasan", in ji koci Gareth Southgate.

Tawagar ta kammala wasannin rukuni a saman teburin Rukunin C ranar Talata duk da 0-0 da suka buga da Slovenia. Kafin haka sun buga 1-1 da Denmark.

Magoya baya sun yi wa 'yan wasan ihu kuma aka dinga jefa wa kociya Southgate fankon kofuna bayan tashi daga wasan na Slovenia.

"Ba zan kawar da kai daga wannan ba," a cewarsa. "Abu mafi muhimmanci shi ne magoya baya su ci gaba da mara mana baya."

Southgate ya ce ya fahimci dalilin da ya sa magoya bayan ke nuna ɓacin rai da sakamakon wasannin, wanda ya ƙunshi 1-0 da suka ci Serbia.

Magoya baya sun yi wa 'yan wasan ihu bayan hura hutun rabin lokaci, sannan shi ma Southgate ya sake fuskantar tsiya lokacin da ya je gode wa magoya baya bayan tashi daga wasan.

"Na fahimci abin da suke nufi da ni kuma hakan zai fi amfani gare ni sama da 'yan wasan," in ji shi.

"Amma hakan yana ta'azzara yanayin da ake ciki. Ban taɓa ganin tawagar da ta tsallake ba kuma ake yi mata irin wannan abin. Na fahimta kuma ba zan kawar da kai ba, amma dai ina alfahari da 'yan wasana a yanzu."