Manyan manufofin da Kwankwaso zai mayar da hankali a kansu

Asalin hoton, @KwankwasoRM
Kamar sauran ƴan takarar shugabancin ƙasa na Najeriya, shi ma Dr Rabi’u Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP ya ƙaddamar da manufofin yaƙin neman zabensa..
Tsohon gwamnan jihar Kanon kuma tsohon Sanata a majalisar dattijan ƙasar ya ƙaddamar da kundin manufofinsa ne a ranar Talata 1 ga watan Nuwamban 2021.
Kundin manufofinsa ya ƙunshi ƙudurce-ƙudurce da hanyoyin da zai bi wajen aiwatar da su idan ya samu nasarar zama shugaban Najeriya.
Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPPn, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya gabatar da kundin manufofin nasa mai shafi 151 ne a wani gagarumin taro a Abuja, da ya haɗa jiga-jigan jam’iyyar da dukkan manyan ƴan takarar jam’iyyar a matakai daban-daban a fadin Najeriya.
Cikin manufofin har da aniyar inganta tsaro ta hanyar kara yawan jami’an tsaron, da kula da lafiyar mata masu juna biyu kyauta da kuma tsawaita amfani da sakamakon jarrabawar shiga jami’a, wato Jamb.
Gwamnatin talakawa
Dan takarar ya ce idan ya samu nasarar zama shugaban Najeriya, gwamnati zai kafa irin ta talakawa.
Ya ce za a kafa kwamitoci tun daga matakin gunduma zuwa ƙananan hukumomi zuwa jihohi da kuma gwamnatin tarayya, waɗanda za su ƙunshi kowane nau’i na al’umma, waɗanda su ne za su yanke shawara a kan irin ayyukan da suke buƙatar a aiwatar musu.
Su za su dinga yanke shawarar abubuwan da suke buƙata gwamnati ta yi musu kama daga kan inganta tattalin arziki da fannin lafiya da ilimi da tsaro da sauran su.

Asalin hoton, @KwankwasoRM
Kudin jarrabawa kyauta
Kazalika ɗan takarar shugaban ƙasar ya yi alwashin kawo ƙarshen wadansu abubuwa da ke yi wa mata da matasa cikas a rayuwa.
Waɗannan abubuwa sun haɗa da
Ba yaro dan makarantar da zai sake biyan kudi na WAEC ko NECO ko JAMB ko NABTIB.
Sannan jarrabawar JAMB za ta dinga kai wa shekara hudu tana amfani ba shekara ɗaya kamar yadda aka saba ba.
Tsaro
A fannin tsaro kuwa dan takarar ya sha alwashin ƙara yawan jami’an tsaron ƙasar.
A yanzu dai Najeriya tana da jami’an soji kusan 250,000 ne kawai, amma Sanata Kwankwaso ya ce zai ƙara yawansu zuwa miliyan ɗaya.
A ganinsa wannan na daga cikin manyan hanyoyin magance matsalar tsaro a ƙasar.
Kazalika ya ce zai tabbatar da yawan ƴan sandan ƙasar ma ya kai miliyan ɗaya.
Ya kuma ce sojojin da suke da ƙwarewa afannin injiniya ne za su dinga jagorantar gyara da faɗaɗa titunan ƙasar don gano tare da lalata maɓoyar ƴan ta’adda.

Asalin hoton, @KwankwasoRM
Cin hanci
Duk da irin kukan da ake yi cewa Najeriya na fama da rashin kudi ko matsi, Injiniya Kwankwaso ya ce yana da yakinin cewa idan aka toshe wasu kafofin sata, gwamnati za ta samu wadataccen kudin da za ta inganta rayuwar al’umma ba tare da ciwo bashi ba.
A don haka ya ce zai samar da ingantattun hanyoyi na toshe duk wata kafa da za a dinga sace kuɗaɗen gwamnati.
Manoma
Kwankwaso ya ce yana da burin taimaka wa manoma da tallafi ta hanyar sayar musu da bashi a farashi mai rangwame.
Sannan za ta dinga sayen amfanin noman manoma ta yadda ba za a bari ƴan kasuwa su saye musu babu daraja ba.
Hakan zai sa harkokin nomansu ya inganta su kuma dinga samun riba mai fa’ida, kamar yadda manufofin nasa su nuna.
Maganin ƴan ta’adda da ƴan bindiga
Ya sha alwashin mayar da dukkan ƙungurman dajin da ƴan ta’adda da ƴan bindiga suka mayar da su maɓoya, ƙarƙashin gwamnati, ta yadda za a mayar da su gonaki ko wasu wurare na musamman da gwamnati da al’umma za su dinga amfana da su.
Za a samar da ƙwararrun jami’an soji a kan iyakoki da dakarun kare dazuka da na bakin ruwa don kare dukkan ɓangarorin ƙsar daga muggan laifuka kamar shiga da fitar da ƙwayoyi da makamai da sauran laifuak.
Za a haɗa kai da ƙasashe maƙwabta don tabbatar da samar da tsaro ta kowane fanni.
Za a yi amfani da fasaha sosai wajen inganta samun bayanan sirri da gano yadda ake kitsa mugayen ayyuka.
Tattalin arziki
Abubuwan da ya sha alwashin yi a wannan fannin sun haɗa da:
- Zama da duk masu tayar da ƙayar baya a fannin samar da man fetur
- Fitar da adadin man da ƙungiyar ƙasashe masu arzikin fetur ta OPEC ta iyakancewa Najeriya
- Inganta tsarin karɓar harajiMagance hauhawar farashi
- Faɗaɗa da inganta harkokin kasuwanci, da sauran su.










