Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fargaba na ƙaruwa yayin da Isra'ila ke jibge dakarunta a kan iyakar Gaza
Babu abin da ake ji daga sama sai ƙugin jiragen yaki, amma jim kaɗan sai aka ga wasu abubuwa biyu sun yi sama, ashe na'urar tsaron Isra'ila ce ta Iron Dome ta fara aiki.
Makamai masu linzami biyu sun nutsa wajen neman wasu makaman roka biyu da Hamas ta harba sama, nan da nan wani wani hayaƙi ya cika samaniya.
Amma da yawan makaman rokar sun kai ga inda aka aika su.
A daren Talata, iyakar Ashkelon da wasu da ke kudancin Isra'ila sun fuskanci wani mummunan hari, bayan dakarun Hamas sun shaida wa mutanen da ke zama a kusa da teku su bar yankin da ƙarfe biyar na yamma.
Tabon harin da aka kai
Muna kusa da garin Nahal Oz, kimain kilomita biyu daga Zirin Gaza kusa da inda sojojin Isra'ila suke. Mun ga shaidar Hamas da shirin farmaki a ko'ina.
A ƙasa babu abin da ake gani sai kwanson harsasai inda mayakan suka kai hari a ranar Asabar.
A gefe guda kuma babu abun da ake gani sai jini a kan titi, ƙonannun motoci a kusa da wani shataletale da kuma gawar wani mayaƙin Hamas da aka bari yashe a ƙasa.
Waɗanda suka mutu sun kai 1,200 daga ɓangaren Isra'ila, yayin da ma'aikatar tsaron ƙasar ta ce mafi yawan su "fararen hula" ne.
Kai-wa da kawowa yake yi a ƙafa, da wayar salularsa a gefen kunnensa, wani ɗan Isra'ila ne da ake kira Israeli Dokarker.
Neman 'yarsa yake yi mai suna Kim.
Lokaci na ƙarshe da suka yi magana shi ne ƙarfe 7:50 na safiyar Asabar.
Kimanin kilomita 50 ne nisan da ke tsakanin garin Yavne zuwa arewa maso gabashi, kullum sai ya je wurin tun bayan harin da aka kai, yana dubawa ko zai ga alamun ƴarsa Kim.
Ta fita ne tare da ƙawayenta zuwa wani bikin kalankuwa na shekara-shekara a kusa da Gaza wanda aka bayar da rahoton mutum kusan 250 sun mutu a wajen.
"Har yanzu ba a kai ga gano ta ba; kuma ba mai iya ba da tabbacin ko ita ma ta mutu," in ji shi.
"Na zo nan ne neman ta."
Da misalin ƙarfe 6 na safe ne Kim ta tafi bikin tare da ƙawayenta, amma ƙarar jiniyar rokar da aka harba ta firgita su suka kama gudu suka koma tantin da aka kafa na gefen titi.
Ba su san cewa mayakan Hamas ne ke ƙaddamar da hare-hare kansu ba daga kan iyaka.
"Abin na ƙarshe da muka ji daga gare ta, shi ne ta tura mana inda take," in ji shi.
"Na yi ƙoƙarin bin inda ta tura min take amma intanet ya katse."
Kim ita ce babbar ƴan Israeli, cikin ƴaƴa uku da yake da su.
"Yarinya ce kyakkyawa," in ji shi "Tana girmama iyayenta kuma tana mana duk abin da muke so.
"Yarinya ce maɗaukakiya muka haifa. Ina da ƙwarin gwiwar tana nan a raye.
Girke dakaru
Ƴan mitoci kusa da iyakar Isra'ila wata ƙatuwar tankar yaƙi ce ke kai-kawo a gefen titi.
Akwai wasu biyar na daban a nan, sannan da muna tafiya mun ga gwammansu na tunkaro nan yankin.
Da alama irin raɗaɗin da aka dasa a zuƙatan mutane irin su Israeli zai haifar da wata mummunar mamaya a Gaza, wanda motocin yaƙi irin waɗannan za su yi.
Yankin ya yi kaca-kaca da harin wasu makamai ta sama masu tayar da hankali.
Wani birni da ake kira Al-Rima a Gaza ya zama ɗaya daga cikin wuraren da wannan fushi ya dirar wa.
Duka manyan gine-ginen yankin sun zama ɓaraguzai; wasu kuma na tsaye amma sun yi duhu saboda hayaƙi da ya mamaye su.
An wayi gari duka Zirin Gaza ya zama saniyar ware, an katse ruwa da wutar lantarki da ake ba shi daga Isra'ila, yayin da aka hana abinci da man fetur tsallakawa yankin daga kan iyaka.
Mazauna garin Al-Rimal da dama sun tsere, sun shiga jerin wasu dubban ƴan Gaza da ba su da wajen fakewa.
Hukumomin Falaɗinawa sun ce mutum sama da 900 sun mutu a harin da Isra'ila ke kai wa na ramuwa.
Amma an yi amannar adadin zai iya zarce haka, yayin da hukumomin ke ci gaba da bincike cikin ɓaraguzai domin gano waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzai.
Ana riƙe da wasu waɗanda aka yi garkuwa da su a wani wuri can a cikin Gaza, waɗanda aka kama a ranar Asabar.
Amma da alama wannan garkuwar da aka yi da mutanen za ta iya zama abin da zai daƙile mamayar da dakarun Isra'ila ke neman yi - wanda yawan dakarun da ake samu ya bayyana hakan ƙarara.
Zai zama wani aikin soji mafi wuya. Tun 2014, Ƙungiyar Hamas ta haƙa wasu gidajen ƙasa a faɗin Gaza, wasu sun yi zurfin mita 30 wasu kuma 40.
Fusatar da mayaƙan suka yi a yanzu za ta iya kai wa ga kashe ƙarin fararen hular Falasɗinawa.
Kuma yawan mutane da za su mutu bayan waɗanda aka kashe a yanzu, zai iya kawo ƙarshen ayyukan Hamas da ikon da take da shi a Gaza, wanda ta fara a 2007.