Wanne abu ne ke ingiza mutane su yi wa kansu lahani?

...

Asalin hoton, GETTY IMAGES

    • Marubuci, Aisha Babangida
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
    • Aiko rahoto daga, Abuja

Rayuwa wani lokaci na iya jefa mu cikin mawuyacin hali na ƙunci da yanke ƙauna, da takaici da ƙin jini da matsi da baƙin ciki da dai sauransu, wanda hakan na iya sa mutane da dama su yi yunƙurin halaka kansu.

Kisan kai wani al'amari ne mai sarkakiya wanda ke fado wa mutum a tunaninsa a matsayin shi ne mafita.

Ko kuma mutum ya yi tunanin cewa shi ne zai kawo karshen wahalar ko matsin da suke ciki a rayuwa.

Duk da cewa yana da wuya a fahimci dalilin da zai sa wani ya yi yuƙurin kashe kansa, mutanen da ke wannan yunƙurin kadai suka san me ke faruwa a cikin zukatansu.

Wata kungiya mai rajin inganta harkokin kula da lafiya a Najeriya 'Nigeria Health Watch' ta ce mutane masu shekaru daban-daban suna jin yunƙurin kashe kansu wasu ma suna kashe kan nasu amma ƙimar hakan ya fi girma a tsakanin mutane da ke fuskantar rashin lafiyar kwakwalwa musamman na baƙin ciki da ƙunci, da nuna wariya, da mutanen da ke fuskantar rikici da bala'i da tashin hankali da zagi, da cin zarafi ko asara da kuma keɓancewa.

A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Fiye da mutum 700 000 ne ke mutuwa saboda kashe kansu a kowace shekara, kuma kisan kai shine na hudu a cikin abubuwan da suka fi haifar da mace-mace tsakanin ƴan shekara 15 zuwa 29.

Hukumar ta ƙara da cewa kashi saba'in da bakwai cikin dari na kisan kai a duniya na faruwa ne a kasashe masu karamin karfi da matsakaicin kuɗin shiga kuma shan maganin kashe ƙwari da rataye kai da harbe kai da bindigogi na daga cikin hanyoyin da mutane ke amfani da su wajen kashe kansu a fadin duniya.

Kisan kai babban ƙalubale ne ga lafiyar jama'a kamar yadda Hannatu mai shekara 33 ta shaida wa BBC yadda ƙunci da nuna wariya daga iyalin ta da kuma baƙin ciki ya haddasa mata yunƙurin kashe kan ta.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shekaru hudu da suka wuce, Hannatu ta tsinci kanta a cikin wani hali wanda mahaifinta, kasancewarsa babba a rayuwarta, ya dage da sai ta auri wanda ba ta so.

Hannatu ta ce matsin lambar da ta samu daga mahaifinta ya haifar mata da tunanin kashe kan ta wanda har tayi yunƙrin hakan.

"Wani sa'in idan ƙunci ya yi min yawa, da damuwa kuma na rasa mafita, sai na ji dama kawai na mutu, rayuwar ta ishe ni, tunanin da ke faɗo min kenan."

"Matsin lambar da ya sa min wannan yunƙurin kisan kan ya sa ni na ji kamar na mutu a ranar, ji nayi rayuwar ta ishe ni."

"Lamarin da ya faru game da aure ne kuma auren dole wanda mahaifi ne ke son ya hada ni da wani ɗan uwansa, ni kuma gaskiya ba son sa nake yi ba."

"Da yake kuma Allah ya ƙadarta da mahaifi na da mahaifyata ba sa tare, ita tana aure a wani waje, shima yana rayuwar shi a wani waje kuma ni a hannun mahaifiyata na tashi."

"Ƙwatsam sai baba na ya zo da maganar aure da ɗan uwan sa, kuma ya nuna laile dole wannan mutumin shi zan aura, ni kuma na roƙe shi na ce yayi haƙuri ya zaɓa min wani, amma ya ƙi."

"Haka dai aka ci gaba da wannan gwagwarmayar, ni na nuna ba na so, mahaifiyata ma ta goyi baya na, shi ya nuna dole sai na yi, kawai sai wata rana mu ka je garin da baba na yake, inda ya ce min cikin shi da mahaifiyata dole na zaɓi ɗaya."

"Ko in zaɓe shi ko mahaifiyata, na rasa ya zan yi da rayuwata, haka nayi shiru, na shiga cikin ƙunci, da tunani da damuwa, saboda ba zan iya zaɓa ba daga cikinsu kuma ya ce na ba shi amsa ba da jimawa ba."

"Haka dai na dinga kuka, na rasa me zan yi, a ranar na ji ina ma ba na raye da ban ga wannan ranar ba.

"Tabbas a ranar na yi tunanin dauke rai ne, wajen karfe 2:30 na dare na taso da ƙuncin yayi min yawa, na ce toh bari nayi sallah ko abun da nake ji zai ragu, amma a nan take ban ji komai ba, kawai sai na je na hau samar rijiya."

"Rijiyar kuma akwai santsi sosai saboda ko ruwa za mu ja sai anyi mana kasahidin karda mu hau saman rijiyar amma hakan na hau duk da na san zan iya faɗa wa ciki, fatar kenan lokacin."

"Wallahi ranar ban ji tsoro ba, saboda duk ƙunci da baccin rai sun riga sun mamaye ziciyata."

...

Asalin hoton, PA MEDIA

Karfin Imani

Hannatu dai ta ce tana cikin wannan yunƙurin, kawai sai tunanin Allah da tsoransa ya faɗo mata inda ta ce nan take ta tuna da wata fatawa da ya ce duk musulmin da ya kashe kansa da ganga, ɗan wuta ne.

"Na yi tunanin idan na kashe kai na wuta zan shiga, saboda a musulunce an ce idan mutum ya kashe kansa da gangan, wuta zai shiga, toh, zan sha wahala kafin na mutu, kuma idan na mutu, wuta zan shiga, sai kawai na ji babu amfani, abin da ya sa na sauka kenan."

"Kuma na kyautata zaton har da sallar da na fara yi kafin na je na aikata hakan, Allah ya taimaka min"

Hannatu ta ce har yanzu tana jin wannan yunƙuri na kashe kan ta saboda mahaifin har yanzu yana sa mata matsin lamba, sakamakon har yanzu ba ta yi auren ba kuma duk ƴan ƙannan ta sunyi har da yara.

Da BBC ta tambayi Hannatu ko ta taɓa tuntuɓar likita don neman taimako kan irin wannan tunani na ƴunƙurin kashe kai, ta ce a'a.

Amma ta ce kullum tana adu'a, tana karanta azkar wanda shi ne yake taimaka mata ko da ace ta ji yunƙurin dauke ran ta, ba ta aikatawa.

Neman Taimakon Ƙwararru

Dakta Nafisa Hayatuddeen, ƙwararriyar likitar ƙwaƙwale ce kuma ta shaida wa BBC cewa kashi 80 cikin 100 na masu yunƙurin kisan kai ko masu kashe kansu abu ne da ana iya daukan mataki domin kiyayewa daga faruwa.

Likitar ta ce cikin bincike na Najeirya, ya nuna cewa mutum 9 a cikin dukannin mutane 100,000 na da irin wannan tunani na kisan kai.

Ta ƙara da cewa a Najeriyar, ana kyari da ƙyamatan dangi da iyali na mutumin da aka ce ya dauki matakin kashe kansa shiyasa ba a fitowa a faɗi.

Likitar ta ci gaba da cewa akwai abubuwa daban-daban da ke iya sa mutum ya yi yunƙurin kashe kansa amma su suna hangen hakan ne ta mahanga guda uku

"Na farko, muna duba yanayin halittar mutum wata 'biological factors', domin mun sani akwai mutanen da a misali a cikin iyaye ko a kakanni akwai wanda ya kashe kan shi, ko da mutum bai rayuwa da su ba ko bai ji labari ba, to shima yana iya ya gaji wannan tunanin."

"Amma dai duk da haka, abin kaɗan ne a cikin al'umma."

"Na biyu, akwai abin da ya shafi 'psychological factors' wanda ya shafi ɗabi'u, da tunani na mutum ko yadda mutum yake duba rayuwa ko duba kan shi a cikin duniya."

"Irin wannan akwai mutanen da suna da ƙaramin abu su sa shi a cikin rai ko kuma suna da yawan nanata abu, ko irin idan abu ya faru su dauke shi da girma, su mai da shi wani babban matsala kamar ba su iya ganin wani abu fiye da wannan."

"To shi ma irin annan na iya sa mutum ya fi kamuwa da iri wannan tunani na cewa ko ya dauki ran shi ya fi mishi sauƙi."

"Mahanga ta uku shi ne muke cewa 'social factors' wanda abubuwa ne da ke faruwa ko a rayuwar mutum ko ba a cikin rayuwar mutum ba amma sun shafi rayuwar shi."

"Misali, yanayin talauci da rashin aikin yi da rashi abinci da wahala da ciwo da dai sauran su, duka irin waɗannan matsaloli na yau da kullum na iya haddasa wa mafi akasarin jama'a tunanin kashe kansu."

Likitar ta kuma ce akwai tunane-tunane ko kuma lissafi da mutum kai yi a cikin kan sa kafin ya yanke hukuncin kisan kai.

"Tunani na farko shine wanda mutum zai ji kawai rayuwansa babu wani abun daɗi a cikin ta, jin kamar haka rayuwar za ta dangwama, cikin ƙunci, da baƙin ciki, toh kuma idan mutum yana irin wannan tunanin, ya fidda rai kenan da tsammanin zai samu gobe me kyau."

"Daga wannan ne wani zai fara burin da ma kawai ya mutu ya huta, shi zai fi ma kowa sauki."

"Daga wannan sai mutum ya fara adu'a ma Allah ya dauki ransa ko ya fara tunanin abubuwan da zai yi ya kashe kansa

"Wasu kuma za su ce sunyi adu'a, sun roƙi Allah, amma jinkirin biyan baƙatun ya daɗe, sai kawai su fara tunanin kisan kai shine kawai matakin da za su dauka, sai ya fara bincike, kan abin da zai iya kashe shi."

Ta ƙara da cewa aƙalla kashi 80 cikin 100 na aɗanda suke yunƙurin kashe kansu suna tattare da wata lalura ta ƙwaƙwaluwa ne, wanda shine yake iya sa mutum yayi tunanin dauka matakin kisan kai.

Ta ce kuma mafi akasari wanda ya fi yawa shine 'depression', lalura ta ƙunci sai sauran da suka biyo baya kuma yana da kyau a gane irin waɗannan lalura wanda idan akayi hakan kuma aka dauki mataki a kan ta, kuma akayi abin da ya dace, ana bibiya, ana dubawa kuma ana auna tunani ko yunƙurin kashe kai, za a iya daukan matakai kan yadda za a maganace matsalar.

...

Asalin hoton, getty images

Mene ne shawara ga masu tunanin kisan kai?

Likitar ta ce akwai dauki ko taimako da mutum zai iya samu idan yana jin kamar ya kashe kansa.

Ta ƙara jaddada cewa irin wannan tunanin lalura ce wadda akwai magani da mutum zai iya amfani da shi ko shawarwari daga likitan ƙwaƙaluwa zai bai wa mutum domin mutum ya samu sauƙin wannan ƙunci da har zai samu burin ya mutu ya huta.

"Akwai dokoki da NAFDAC ta fito da su da ke hana hanyoyi da ake iya bi ko abubuwa da ake iya amfani da su kamar su maganin ƙwari ta hana samun sayansu hakan nan kawai, wannan yana da tasiri kuma yana da amfani."

"Amma ban da shi kuma, akwai gudumawa babba da jami'an labaru suke dauka don kiyaye irin wannan lamari."

"Mafi akasari idan aka samu wani ya kashe kan shi, ko yunƙurin kashe kan shi, za a gani a labaru da social media ana ta yaɗa wa, toh abin da ya kamata shine, masu daukan irin waɗannan rahotannin su dinga ƙoƙarin ƙiyasce me za a faɗi game da wanda ya kashe kansa."

"A mai da hankali kan faɗakarwa kan lalurai da matsaloli da ke iya jawo wa mutum ya iya irin wannan yunƙurin kisan kai."

"Idan akayi haka aka mayar da hankali akan faɗakarwa a maimakon ba da labarin abin da ya yi ya kashe kansa ko yunƙurin kashe kansa, saboda idan ba a faɗa ba, mutane ma ba za su ji labari yanda za su iya kashe kansu ba."

"Saboda haka akai ƙa'idoji da ya kamata masu ba da rahoto su bi kafin bayar da labarin wani ya kashe kansa.

Likitar ta ce yana da matuƙar muhimmanci ga al'umma gaba daya su fahimci cewa akwai lalurai na ƙwaƙwaluwa ko na damuwa daban-daban wanda ke iya bayyana ta yanayi iri-iri a mutum da zai sa musu yunƙurin kisan kai saboda sanin yadda za a tafi da irinsu.

Ta jaddada cewa al'umma su cire ƙyama da ƙyari da akeyi wa mutane masu lalura na yunƙurin kashe kansu inda ta ƙara da cewa cuta na ƙwaƙwalwa na iya kama koma waye saboda haka idan hakan na faruwa, a dinga faɗakar da juna kuma a san cewa akwai magani.