Jam'iyyar adawa ta Labour ta samu gagarumar nasara a zaɓen Birtaniya

Jam'iyyar Labour ta lashe babban zaben Birtaniya kuma tana kan hanyar samun gagarumin rinjaye.
Tuni Firaiminista mai ci Rishi Sunak na jam'iyyar Conservatices ya rungumi kaddara, tare da taya abokin karawarsa Keir Starmer da zai gaje shi murna.
A jawabinsa na nasara a kwaryar birnin London, Mista Stermer, ya ce bayan shekaru goma sha hudu na mulkin 'yan mazan jiya, yanzu yan kasar sun rabu da alakakai.
Ya ce ''Kun yi yakin neman zabe, kun kada kuri'a, kun yi zabe, yanzu Allah ya kawo sauyi, don haka canji ya fara nan take''.
Yan Conservatives sun fara sukar juna
A jam'iyyar Conservatives ta Firaminista mai barin gado Rishi Sunak kuwa an fara ce-ce-ku-ce kan gagarumin kayin da jam'iyyar ta sha a zaben.
Wasu fitattun 'yan jam'iyyar na ƙunƙunin cewa rikicin cikin gida ne ya kayar da su.
Ɓangarorin da ke adawa da juna na ta neman ɗora wa junansu alhaki, sai dai kamar yadda tsohon sakataren tsaron kasar Grant Shapps ya bayyana, jam'iyya ba ta cin zabe sai yayanta sun zama tsintsiya madaurinki daya.
Shi kansa, da karin wasu ministocin gwamnati bakwai sun rasa kujerunsu.
Jagoran jam'iyyar Reform mai ra'ayin kawo sauyi Niger Farage, ya ce siyasar Birtaniya, ta gamu da wani gagarumin juyin waina.
Wane ne Keir Starmer?
Keir Starmer ya shiga siyasa ne shekaru goma kacal da suka gabata bayan ya shafe tsawon lokaci yana aikin lauya ciki har da wanda ya taba zama babban mai gabatar da kara na Ingila da Wales.
Ya yi rawar gani da suna sosai wajen shari'o'in kare hakkin bil'adama.
Kamar yadda ya yi ta ƙoƙarin tunatar da masu jefa ƙuri'a a kai-a kai, iyayensa basu da karfi sosai, domin mahaifinsa malamin jiyya ne a asibiti, kana shine na farko a danginsa da ya samu sukunin zuwa jami'a.
Yayin da ake yi masa ba'a da rashin kwarijini a jaridun Burtaniya, da alama masu kada kuri'a sun ce sun gani, domin sun ba shi nasarar da aka shafe shekaru da dama ba a ga irinta ba.
Keir Starmer yana da 'ya'ya biyu kuma mai kishin kwallon kafa ne.
Duk da ya zama shugaban jam'iyyarsa ta Labour, hakan bai sa ya yi watsi da tsaffin abonkansa ba, domin yana yawan haduwa da su a wata majalisa da ke tsakiyar Landan a duk karshen mako.







