Yadda hatsarin mota ya yi ajalin mata 'yan kai amarya 16 a Katsina

Lokacin karatu: Minti 2

Rundunar Yansanda jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya, ta yi karin haske kan wani mummunan hatsarin mota da ya yi sanadin mutuwar mata 16 'yan kai amarya bayan motar da suke ciki ta yi taho mu gama da wata motar.

Yansandan sun ce suna tunanin hatsarin ya rutsa da amaryar amma ba su tabbatar da ko har da angon ba a hatsarin da ya afku a tsakanin Dutsimma zuwa Karofi.

Motoci ne dai suka yi karo da juna inda kuma suke dauke da mutum 30 a cikin su.

Shamsudeen Babajo, kakakin hukumar kula da kiyaye hadura ta jahar Katsina, ya shaida wa BBC cewa, hadarin ya afku ne a ranar Asabar, 31 ga watan Janairun 2026.

Ya ce, bincike ya nuna cewa motar da ta dauki 'yan kai amaryar na kan gudu ne a lokacin da lamarin ya afku.

Ya ce." A cikin motocin da suka yi taho mu gama da juna akwai mutum 30, kuma 16 daga cikinsu duk mata sun rasu, sai kuma mutum hudu wadanda ba su ji ciwo ba, 10 kuma sun samu rauni inda tuni aka kai su asibiti."

Jami'in ya ce," Muna kyautata tsammanin amaryar na cikin mata 16 da suka rasu, tun da a cikin mutum 30 din da hadarin ya rutsa da su duk matan sun rasu, amma shi angon ba mu da tabbas ko yana cikin wadanda suka mutu.

Amma ya kara da cewa a cikin mutanen namiji ne guda ne ya rasu kuma shi ne daya daga cikin direbobin da suka yi hadarin."

Shamsudeen Babajo, ya ce, bayanan da suka samu na abin da ya janyo hadarin shi ne an cika mutane da yawa a cikin motar, sannan kuma direban na gudu sosai, kuma yadda ya wuce wata mota bai yi a kan ka'ida ba.

Hatsarin mota dai ya zama tamkar ruwan dare gama duniya a Najeriya, lamarin da ke haifar da asarar rayuwa da dukiya.

Mutane da dama dai na ganin ana samun hatsari ne idan hanya ba ta da kyau, sai dai a Najeriya hanyoyi masu kyau ɗin ma ana yawan samun haɗuran mota a kansu.

Hukumar kiyaye afkuwar hadura ta Najeriya dai ta lissafo abubuwa da dama da ke janyo yawan haɗura a kasar da suka hada da:

1. Gudun wuce sa'a ko tukin ganganci

2. Ɗaukar kayan da ya wuce ƙima

3. Rashin mutunta dokokin hanya

4. Tuki cikin maye

5. Barci

6. Rashin lafiyar idanu

7. Rashin bin ƙa'idar fitilar bayar da hannu (danja)

8. Bin ɓarauniyar hanya

9. Amfani da wayar salula lokacin tuki

10. Rashin gogewa wurin tuki