Me ya sa jarabawar JAMB ta bana ta bar baya da ƙura?

Lokacin karatu: Minti 3

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu a Najeriya, JAMB ta ce daga ranar 16 ga watan Mayun bana ne, za ta bai wa wasu daga cikin ɗaliban da suka fuskanci matsala wajen rubuta jarabawar a bana damar sake rubuta ta.

Ta ce za ta yi hakan ne bayan binciken da ta gudanar wanda ya nuna cewa an samu tangarɗa yayin jarabawar lamarin da ya sa wasu ɗalibai da dama suka faɗi jarabawar.

A sanarwar da JAMB ta fitar ranar Laraba, hukumar ta tabbatar cewa akwai wasu matsaloli da tabbas suka ba da gudummawa wajen faɗuwar da ɗalibai suka yi a jarabawar ta bana.

Shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede dai ya nemi afuwar ɗaliban da suka samu matsala har ma da ƴan Najeriya inda ya ce ya ɗauki alhakin matsalolin da aka samu yana mai alƙawarta cewa za su yi duk mai yiwuwa wajen gyara kuren da aka samu.

Ya bayyana cewa ɗalibai 379,997 ne za su sake rubuta jarabawar ta bana sakamakon ƙorafe-ƙorafen samun tangarɗar na'ura da zargin rashin daidaito a tambayoyin jarabawar.

Jihohin da za a sake rubuta JAMB

JAMB ta ce ta gano cewa an samu matsaloli a cibiyoyin rubuta jarabawar 157 a shiyyar Legas da Owerri.

A shiyyar Legas, cibiyoyi 65 ne lamarin ya shafa a jihohin Legas da Oyo. A shiyyar Owerri kuma, cibiyoyin jarabawar 92 lamarin ya shafa a Imo da Abia da Anambra da kuma Ebonyi.

Ranar sake rubuta jarabawar

Farfesa Oloyede ya ce daga ranar Juma'a 16 ga watan Mayu ne, ɗaliban da suka fuskanci matsala za su fara rubuta jarabawar a karo na biyu. Ya ƙara da cewa ɗaliban da lamarin ya shafa za su samu saƙonni ta wayoyin hannunsu da kuma adireshin imel ɗinsu inda a jiki za a bayyana masu ranar da za su rubuta jarabawar da kuma inda za su rubuta ta.

"Za a kira wasu ta waya. Za a buƙaci su sake buga takardar rajistar jarabawar da za su yi amfani da iya wajen rubuta ta".

A ranar Litinin ne hukumar JAMB ta sanar cewa za ta yi nazari kan sakamakon jarabawar ta bana da aka saki a baya-bayan nan.

Cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Fabian Benjamin, ya fitar, ya ce hukumar za ta hanzarta yin nazari kan tsarin rubuta jarabawar da suke a kowace shekara.

Hakan ba ya rasa nasaba da yadda aka samu ƙorafe-ƙorafe da dama game da yadda jarabawar ta bana ta gudana.

Sanarwar ta kara da cewa hukumar ta damu matuƙa da yadda aka samu sabbin ƙorafe-ƙorafe da ba a saba ji ba musamman daga jihohi a Najeriya.

Ƴan Najeriya har da ɗaliban da suka rubuta jarabawar sun yi ta wallafa ƙorafe-ƙorafensu a shafukan sada zumunta game da yadda ɗalibai da dama suka faɗi jarabawar musamman waɗanda a baya suka samu maki mai kyau.