Abin da Obasanjo ya faɗa wa ƴan ƙungiyar Malam Shekarau

..

Asalin hoton, OTHERS

Lokacin karatu: Minti 3

A ranar Talata ne wata tawagar mutum 20 ta shugabannin arewacin Najeriya ƙarkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Malam Ibrahim Shekarau suka gana da tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo a gidansa da ke Abeokuta.

Tawagar dai ta je gidan tsohon shugaban na Najeriya da manufar lalubo hanyoyin magance matsalolin da suka dabaibaye arewacin Najeriya da ma faɗin ƙasar baki ɗaya.

Me Obasanjo ya faɗa wa tawagar?

..

Asalin hoton, Others

Da farko dai sai da tsohon shugaban na Najeriya ya bayyana rashin jin daɗinsa dangane da yadda rarrabuwar kai tsakanin ƴan ƙasar ya jawo wa ƙasar komabaya wadda ita ce jagora ga ƙasashen baƙaƙe.

Sai dai kuma Cif Obasanjo ya ce duk da waɗannan matsaloli da ƙasar ke fuskanta har yanzu yana da kyakkyawan fata a kan Najeriyar "idan dai har za mu iya yin waiwaye mu kalli abin da ya ɓaci sannan mu gyara."

Cif Obasanjo ya ɗora tsarin shiyya-shiyya wanda ta hanyarsa ne aka samu ƴancin kan Najeriya da babban dalilin da ya jawo matsalar rarrabuwa a tsakanin shiyyoin ƙasar "gaskiya ita ce a bayan samun ƴancin kai, Najeriya ta samu shugabanni guda uku kuma tun wancan lokacin har zuwa yanzu ake tafiya da tsarin ƙasashe uku a cikin jamhuriya guda ɗaya."

"E, kun ayyana kanku a matsayin ƙungiyar masu son dimokraɗiyya ta arewacin Najeriya, amma na so a ce kun kira kanku ƙungiyar cigaban dimokraɗiyya ta Najeriya. Zan ci gaba da kasancewa ɗan Najeriya fiye da ɗan jamhuriyar Oduduwa."

"Ina matuƙar alfaharin kasancewata Bayarabe amma kuma bai kamata kasancewar tawa Bayarabe ta kishiyanci zamana ɗan Najeriya ba...Dole ne mu sami mutumin da zai fi kowa iya jagorancin Najeriya ba tare da nuna banbanci dangane da inda ya fito ba. Dole ne mu yi aiki tare." Kamar yadda Cif Obasanjo ya yi ƙarin haske.

Me Malam Shekarau ya faɗa wa Obasanjo?

..

Asalin hoton, Others

Tsohon gwamnan Kano, Sanata Malam Ibrahim Shekarau ya shaida wa Obasanjo cewa "mun kafa wannan ƙungiya ne da manufar lalubo hanyar cigaban Najeriya a matsayinta ta ƙasa ɗaya al'umma ɗaya.

"Mun kafa wannan ƙungiya ne domin magance matsalolin da Najeriya ke fuskanta da suka haɗa da rarrabuwar kai da rashin aikin yi a tsakanin matasa da matsalar ilimi da shugabanci da tsaro da kuma samar da nagartattun mutane a tsarin shugabancin Najeriya." In ji Shekarau.

Malam Shekarau ya bayyana rashin jin ɗaɗinsa dangane da abin da ya kira "yadda mutum miliyan 93 na masu rijista a Najeriya suke kasa zaɓar nagartattun mutane a matsayin shugabanni waɗanda dukansu ba su fi 11,000 ba.

"Daga gwamnonin jihohi 36 da mataimakansu da shugaban ƙasa da mataimakinsa da ƴan majalisar dattawa da wakilai 469 da ciyamomi da kansiloli dukkansu da kaɗan suka fi 11,000 amma abin mamaki masu rijista miliyan 93 ba za su iya zaɓar shugabanni nagartattu ba." In ji Shekarau.

Daga ƙarshe Sanata Ibrahim Shekarau ya shaida wa Obasanjo cewa za su yi duba dangane da sunan ƙungiyar tasu domin duba yiwuwar sauya shi.

Wace ƙungiyar ce Shekarau ke jagoranta?

A watan Agustan 2024 ɗin nan ne dai tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce shi da wasu gogaggun ‘yansiyasa a arewacin Najeriya, sun fara lissafin samar da mafita ga yankin.

Sun kira wannan yunƙuri nasu da taken ''League of Northern Democrats'', a turance - wani taron dangi na wasu masu fada a ji na areawacin Najeriya, da suka hada da tsofaffin gwamnoni da ma'aikatan gwamnati da 'yansiyasa da tsofaffin sojoji da 'yan sanda, da sauran masu ruwa da tsaki na yankin.

Kuma a taron da suka gudanar a Abuja a lokacin ƙungiyar ta amince da naɗa tsohon gwamnan jihar Kanon kuma tsohon ministan Ilimi Sanata Malam Ibrahim Shekarau a matsayin jagora.