'Ya kamata a biya al'ummar Mokwa diyya'

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar nan mai rajin farfaɗo da ruhin dimokraɗiyya a arewacin Najeriya wato League of Northern Democrats ta bukaci gwamnatin ƙasar da ta biya diyya ga wadanda iftila'in ambaliyar ruwa ta abka wa a jihar Neja.
Kungiyar ta ce duk da gwamnatin tarayya ta ziyarci yankin, amma akwai bukatar ta fara tunanin biyan diyya.
Ladan Salihu, shi ne mai magana da yawun kungiyar ya shaida wa BBC cewa idan aka duba yadda wannan iftila'i ya zo bagatatan ga asarar rayuka da dukiya da aka yi, to ya kamata gwamnati ta tausaya ta bude baitul malin kasa ta fito da kudi a biya diyya domin tausayawa.
Ya ce, "Diyyar da gwamnati zata biya ta hada da ta agaji da kyautatawa saboda idan aka yi la'akari da halin da ake ciki a ƙasar nan na tsadar rayuwa sannan ace na samu irin wannan iftila'i to dole akwai bukatar a dauki matakai da zasu kawo sauki ga mutanen da abin ya shafa."
Mai magana da yawun kungiyar ta League of Northern Democrats, ya ce, " Ba wai gwamnatin tarayyar ba tayi kokari ba, ta yi kokari sosai amma har yanzu akwai sauran rina a kaba don haka dole ne gwamnati ta koma ta sake tunani ta duba yadda wannan iftila'i na ambaliyar ruwa ya tsayar da komai a wannan gari."
" A gaskiya ya kamata gwamnati ta duba iyalan wadanda wannan ambaliya ta shafa domin wasu sun rasa mazajenzu wasu matan suka rasa, to dole gwamnati ta dauki kudi ta taimaka wa irin wadannan mutanen da suka tagayyara don wasu hatta gidajensu sun rushe basu da matsugunni to ta in aza su fara?."in ji shi.
Ladan Salihu, ya ce " Ba wai gwamnati ce kadai ke da alhakin wannan taimako ba, dole ne a hada karfi da karfe tsakanin masu hannu da shuni da 'yan siyasa da kungiyoyi da bankuna da ma gwamnatocin da ke makwabtaka da jihar ta Neja domin a tallafawa mutanen da wannan iftila'i ya shafa."
Hukumomi a Mokwa inda aka samu ambaliyar ruwan sun ce adadin mutanen da suka mutu sun haura mutum 230 yayin da har yanzu ake neman sama da mutum 400.
A ranar Laraba da daddare ne wata ambaliya ta afka wa garin Mokwa na jihar Neja, inda ta yi sanadiyar rayuka da dama tare kuma da lalata gidaje.
Lamarin ya ɗimauta mutanen yankin saboda irin ɓarnar da ambaliyar ta yi.
Rahotanni sun bayyana cewa an shafe tsawon dare ana tafka mamakon ruwan sama, wanda daga bisani ya janyo ambaliyar.
Tun da farko dai, hukumomi sun yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar samun ambaliya a aƙalla jihohi 15 cikin 36 na faɗin Najeriya.

Asalin hoton, Mikail Musa











