Yadda biyan ƴanbindiga kuɗin fansa ke illa ga tsaron Najeriya

Asalin hoton, icirnigeria
Wani rahoto na Kamfanin SB Morgen da ke sa ido kan harkokin tsaro a Yammacin Afirka, ya ce masu garkuwa da mutane a Najeriya sun nemi kusan naira biliyan 10.9 a matsayin kudin fansa daga iyalan wadanda suka sace daga watan Junin 2023 zuwa Yulin 2024.
Rahoton kamfanin wanda takensa shi ne yadda satar mutane ta zama kasuwanci a Najeriya, ya ce daga cikin kudaden da aka nema, ƴanbindigar sun yi nasarar karɓar kimanin naira biliyan daya.
Kusan kullum, 'yan Najeriya musamman mazauna yankin arewa maso yamma, na cikin fargabar sacewa ko kisa daga 'yan fashin daji da ke kai hare-hare a kullum.
Rahoton ya ce mutum 7,568 ne aka sace a sassan Najeriya tsakanin Yunin 2023 zuwa Yulin 2024.
Ƴanbindigar da ke satar mutane domin kuɗin fansa sun ƙunshi mayaƙan Boko Haram da ke arewa maso gabashi, da ƴanbindiga da ke cin karensu ba babbaka a arewa maso tsakiya da arewa maso yammaci da kuma ayyukan masu barazanar ɓallewa daga ƙasar a kudu maso kudu.
Rahoton ya ce jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna da ke shiyar arewa maso yammaci matsalar ta satar mutane domin kuɗin fansa ta fi yin ƙamari.
Kuma a jihohin guda uku ne aka fi satar kisan mutane, a cewar rahoton na SB Morgen.
Rahoton ya ce a shekarar 2024 kaɗai, an kashe mutum 1,056 ta sanadin ƙoƙarin sace su, yayin da kuma aka saci mutum 1,130.
Rahoton ya ce wani abu da ke ƙara haifar da barazana shi ne yadda ƴanbindigar ke saɓa alƙawali, inda suke kashe mutane duk da an biya su kuɗin fansa.
Ko a makon da ya gabata ƴanbindiga sun kashe Sarkin Gobir na Gatawa Isa Bawa, bayan kwashe makonni a hannunsu suna garkuwa da shi, lamarin da ya girgiza ƴan Najeriya.
Masana tsaro irinsu Malam Kabiru Adamu shugaban kamfanin Beacon Consulting ya ce dole akwai waɗanda ke da alaƙa da ƴanbindigar da suke aiki tare da ke taimaka masu a harkar satar mutane domin karɓar kuɗin fansa.
“duk lokacin da aka ce an samu matsala ta tsaro irin wannan, da wahala ka ga cewa shi ainihin wanda yake yi a ce shi kaɗai ne dole akwai waɗanda ke taimaka masa,” in ji masanin.
'Biyan kuɗin fansa ke ƙara girman matsalar'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Rahoton SB Morgen ya bayyana girman yadda matsalolin tsaron Najeriya ke ci gaba da dagulewa.
“A wannan yanayi na barazanar tsaro iri daban-daban, satar mutane domin kuɗin fansa na ci gaba da zama ruwan dare a sassan Najeriya,” a cewar rahoton.
Shugaban kamfanin Beacon Malam Kabiru Adamu ya ce ƴanbindigar kan yi amfani da kuɗin da suka karɓa na fansa wurin ci gaba da ayyukansu, "domin za su saye makamai."
"Sannan za su ci gaba da kula da waɗanda ke taimaka masu wajen gudanar da ayyukansu,"
“Za su ci gaba da ba waɗanda ke ba su kariya daga ɓangaren jami’an tsaro da gwamnati kuɗi don ci gaba da ba su kariyar,”
"Kuma za su ci gaba da amfani da kuɗin domin gudanar da harakokin rayuwar da suka saba ta shan ƙwaya da neman matan banza."
"Samun kuɗaɗen ne ke ƙara tunzura su domin su ci gaba da satar mutane,” in ji Kabiru Adamu.
Sannan masanin ya ce manyan illolin da biyan kuɗin fansar ke yi, su ne hana mutane walwala musamman kasuwanci da ayyukan noma, wata babbar matsala da ke barazana ga ƙarancin abinci a Najeriya.
Matsalar tsaro a Najeriya ta zama wata sana'a da ake samun maƙudan kaɗi, kuma ga alama matsalar na ci gaba da faɗaɗa.
Sau da yawa ƴanfashin kan kashe wanda suka kama, wasu kuma sukan sake su idan suka ga cewa babu alamar za a kawo kuɗin fansa.
Duk da dai iƙirarin jami'an tsaro kan cewa suna ƙoƙarin magance matsalar amma galibi waɗanda ake sacewa sai an biya kuɗin fansa ake sako su.
Akwai doka da ta haramta biyan kuɗin fansa a Najeriya, kamar yadda aka yi tanadi hukuncin kisa ko ɗaurin rai-da-rai ga duk wanda aka samu da laifin garkuwa da mutane domin kuɗin fansa
Amma ƴan Najeriya da dama na ganin tilas ke sa ana biyan kuɗin fansa saboda babu wani zaɓi.










