Abin da ya sa nake cinikin kuɗin fansa tsakanin ƴanbindiga da iyalai

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Priya Sippy
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Wani mai shiga tsakani wurin biyan kuɗin fansar mutanen da ake yin garkuwa da su ya shaida wa BBC cewa duk da cewa biyan kuɗin fansa laifi ne a Najeriya, amma ita ce hanya ɗaya tilo da iyalai za su samu damar karɓo ƴan'uwansu daga hannun ƴanbindiga waɗanda ke addabar arewacin Najeriya.
Sulaiman, wanda muka sakaya wa suna domin kariya, na zaune ne a jihar Kaduna, inda a kwanakin nan ƴan fashin daji suka sace yara ƴan makaranta aƙalla 280 daga wata makaranta a ƙauyen Kuriga.
Ya kwashe shekaru yana shiga tsakani domin karɓo mutane daga hannun ƴanbindiga, wani abu mai haɗarin gaske - tun lokacin da aka yi garkuwa da wasu ƴan'uwansa.
Ya shaida wa BBC cewa "Dole ne mu yi ciniki da su. Ba za ka iya amfani da ƙarfi wajen karɓo wadanda ake garkuwa da su ba, domin hakan zai jefa rayuwarsu cikin haɗari".
Sulaiman ya fara shiga tsakanin iyalai da masu garkuwa da mutane ne a shekarar 2021 - shekara ɗaya kafin a yi dokar haramta biyan kuɗin fansa a Najeriya.
A tsawon shekara uku, Sulaiman ya ce ya shiga tsakani domin sakin sama da mutum 200 - wanda hakan kaɗan ne a cikin dubban mutanen da aka sace a cikin shekara 10 da ta gabata.
Tattaunawa da masu garkuwa da mutane lamari ne da ke buƙatar haƙuri da ƙwarin gwiwa.
"Gwamnati na ganin kamar ina taimaka wa ƴan fashin daji ne," in ji shi, lokacin da yake magana da BBC daga wani wuri da bai bayyana ba.
"Su kuma ƴan fashin na ganin cewa kamar ina karɓar kuɗi ne daga gwamnati, ni kaina ban tsira daga a yi garkuwa da ni ba."
Lokaci na farko da ya tattauna da ƴan fashin shi ne lokacin da yake ƙoƙarin haɗa kuɗin fansa naira....($12,500) domin karɓo ƴan'uwansa biyu da aka sace.
Ya ce "A lokacin ban san me nake sa kaina a ciki ba. Kawai ina magana da su ne - ina roƙon su".
To amma haƙurin da ya nuna wajen tattaunawa da ƴan fashin dajin ya yi amfani, inda hakan ya taimaka aka saki ƴan'uwan nasa - duk da cewa sai da ya sayar da gonarsa a ƙauye domin haɗa kuɗin fansar da aka biya.

Asalin hoton, AFP
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Lokacin da aka ji labarin cewa an sako ƴan'uwansa, sai wasu iyalan waɗanda su ma aka sace wa ƴan'uwa suka neme shi domin ya taimaka musu. Daga nan ne ya ci gaba da tattaunawa da ƴan fashin ta waya.
"Kusan kowa a ƙauyenmu an ɗauke masa ɗan'uwa," in ji shi, ya ce ya na taimaka musu wajen ciniki da ƴan fashi ba tare da an biya shi ko kwabo ba.
Kuma duk da cewa an haramta biyan kuɗin fansa a Najeriya, mutane na ci gaba da zuwa wajen shi domin ya taimaka musu wajen yin ciniki da ƴan fashi.
Sulaiman ya ce lamari ne mai cike da haɗari: "Gwamnati ba ta son a tattauna da ƴan fashin, kuma za a iya ɗaure mutum a gidan yari saboda hakan."
Ya ɗora laifin abin da ke faruwa na garkuwa da mutane kan talauci da rashin aikin yi tsakanin matasa.
Sulaiman ya ce: "Idan ina magana da su ina ƙara fahimtar su," ya ce yawanci ana cinikin ne da harshen Hausa duk da cewa a mafi yawan lokuta yanayin maganar na nuna cewa masu satar mutanen Fulani ne.
"Nakan ce musu na san cewa ku na rayuwa cikin wahala a daji, babu lantarki. Na san cewa su na ganin cewa gwamnati ta manta da su."

Asalin hoton, AFP
Ƴan fashin waɗanda akasarin su ke tafiya a saman babura sukan kai hari ne kan gidajen mutane, a mafi yawan lokuta bayan samun bayanai daga wasu mutane da ake kira infoma.
Matsalar ta zamo wata sana'a da ake samun maƙudan kaɗi ta hanyar ta.
Kimanin ƴan fashin daji 30,000, waɗanda ke da dabobi kimanin 100 suke aikata ta'asa a arewa-maso-yammacin Najeriya, in ji Cibiyar bunƙasa mulkin demokuraɗiyya - wata ƙungiyar ƙwararru da ke Abuja, babban birnin ƙasar.
Sulaiman ya ce samun nasararsa wajen ciniki da ƴan fashin ya danganta ne ga shugaban ƴan fashin da suka yi garkuwa da mutanen: "Wasu daga cikin ƴan fashin da muka yi ciniki da su na ci gaba da riƙe waɗanda suke garkuwa da su duk kuwa da cewa an biya su kuɗin fansa, su na son sai an ƙara musu kuɗi.
"Amma wasu kan saki mutane da zarar aka biya su kuɗin fansa."
Lamarin na da wahala sosai a wani lokaci, wani lokaci sai a kwashe kwana 50 ana ciniki kafin a saki wanda aka sace, kuma za a iya yin kiran waya 20 zuwa 30.
"Dole ne sai an yi amfani da kalamai masu taushi. Za su iya yi wa mutum rashin mutunci ko ma su zage ka, to amma dole ne ka kwantar da hankalinka," in ji shi.
Duk da cewa ana ƙarancin takardun kuɗi a Najeriya masu garkuwa da mutane kan buƙaci a biya kuɗin fansa da tsabar kuɗi saboda ba su son a tura musu ta banki domin za a iya gano su cikin sauƙi.
Sulaiman ya ce a mafi yawan lokuta mahaifi ko kuma ɗan'uwan wanda aka kama ne ke kai kuɗin fansar.
"Ƴan fashin su ne za su kira su kwatanta wa mutum inda zai same su a cikin daji. Idan aka isa wurin sukan ƙirga kuɗin dalla-dalla."

Asalin hoton, Getty Images
Wani lokaci ƴan fashin kan buƙaci a saya musu babura ko giya da taba sigari a matsayin cikin kayan da za a aki domin fansar wanda suka kama.
Lokacin da aka sace wani na kusa da Sulaiman daga wata jami'a tare da sauran ɗalibai - gabanin lokacin da aka haramta biyan kuɗin fansa - ya ce gwamnati ta biya kimanin naira miliyan 3.5 ($2,370) a kan kowane ɗalibi kafin a sake su - duk da dai hukumomi ba su tabbatar da gaskiyar hakan ba.
"Gwamnati ba za ta taɓa faɗin cewa ta biya kuɗin fansa ba domin hakan zai nuna cewa ta gaza. Amma mu da muka sani mun sani domin kuwa mu ba mu da irin waɗannan kuɗaɗen," in ji shi.
Sulaiman na cikin waɗanda suka yi cinikin fito da ɗaliban kuma ya ce da farko ƴan fashin sun buƙaci a biya su kimanin naira miliyan 50 ($32,000) a kan kowane ɗalibi, amma daga baya aka yi ciniki.
Yanzu da aka ƙyale mutane su biya kuɗin fansa da kansu, mutane ƙalilan ne suke iya haɗa kuɗin fansar ƴan'uwansu. Yawanci kan ɓuge da neman taimako daga al'umma, duk da cewa hakan ma a yanzu na yin wahala saboda matsi na tattalin arziƙi.
Sau da yawa ƴan fashin kan kashe wanda suka kama, wasu kuma sukan sake su idan suka ga cewa babu alamar za a kawo kuɗin fansa.
Sulaiman na ganin cewa dawowar sace-sacen ɗalibai daga makarantu da barazanar kashe su wata dabara ce ta sake janyo hakalin gwamnati: "Su na ganin cewa gwamnati za ta ce za ta biya kuɗin."
Akwai wasu rahotanni da ke bayyana cewa gwamnati ta biya kuɗin fansa a lokuta da dama - duk da dai gwamnatin ta sha musawa.
Kuma shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa "ba za a biya ko kwabo ba" domin a karɓo yaran da aka sace kwanan nan a makarantar gwamnati da ke Kuriga, inda ya umarci jami'an tsaro su yi duk mai yiwuwa wajen ceto su.
Rahoton wani kamfani mai nazari kan tsaro, SBM Intelligence, ya nuna cewa ƙungoyoyin ƴan fashin daji sun buƙaci a biya kuɗin fansa da ya kai dalar Amurka miliyan shida tsakanin watan Yulin 2022 zuwa Yunin shekara ta 2023.
Sulaiman ya amince da bayanin gwamnati cewa ci gaba da biyan kuɗin fansa zai ci gaba ne kawai da "iza wutar sana'ar garkuwa da mutane. Ƴan fashin na neman kuɗi ne ido rufe."
Amma ya ce ya na da yaƙinin cewa amfani da ƙarfin soji kawai ba zai maganace matsalar ba: "Idan zan bai wa gwamnati shawara, zan ce mata ta tattauna da waɗannan mutanen."
Amma kafin a samu mafita, Sulaiman na fargabar cewa kiran waya da zai samu na gaba, wani batun ne na satar wasu mutanen.
Amma duk da haka ba zai ƙi amsawa ba saboda ya na son ya taimaki mutanensa.







