Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hare-haren Amurka sun kashe gomman ƴan ci-ranin Afirka a Yemen
- Marubuci, Jaroslav Lukiv
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Marubuci, David Gritten
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 3
Aƙalla 'yan ci-rani 68 daga Afirka ne suka mutu a harin jirgin saman Amurka a wani sansanin tsare mutane a yankin Houthi da ke arewa maso yammacin Yemen, kamar yadda gidan talabijin ta Houthi Al Masirah ta shaida.
Al Masirah ta kuma ruwaito cewa wasu 'yan ci-rani 47 sun samu rauni mai tsanani lokacin da aka kai harin a cibiyar da ke lardin Saada.
Ba a samu martani kai tsaye daga sojojin Amurka ba.
Amma wannan ya biyo bayan sanarwar da dakarun Amurka suka fitar, wadda ta bayyana cewa dakarunsu sun kai hare-hare sama da 800 tun lokacin da Shugaba Donald Trump ya umarci a ƙara zafafa hare-haren jiragen sama a kan Houthi a ranar 15 ga Maris.
Houthi ta ce hare-haren sun "kashe dubban mayaƙanta da kuma shugabanninta da dama," ciki har da manyan jami'an da ke kula da shirye-shiryen roka da jiragen sama marasa matuki.
Hukumomin da Houthi ke jagoranta sun ce hare-haren sun kashe dubban fararen hula, amma sun ruwaito cewa 'yan kungiyar ba su samu asarar rayuka da yawa ba.
Cibiyar tsare 'yan ci-rani a Saada na ɗauke da 'yan gudun hijira 115 daga Afirka lokacin da aka kai harin a daren Lahadi.
Duk da mawuyacin halin jin ƙai a Yemen sakamakon yaƙin da ya ɗauki shekaru 11, 'yan ci-rani suna ci gaba da shigowa ƙasar ta jirgin ruwa daga Afirka, mafi yawan su suna niyyar tsallakawa zuwa Saudiyya don neman aiki.
A madadin haka, suna fuskantar cin zarafi da tsarewa da tashin hankali, da tafiye-tafiye masu haɗari ta yankunan da ake ci gaba da yaƙi, kamar yadda Hukumar Kula da Ƙaura ta Duniya (IOM) ta bayyana.
A cikin shekarar 2024 kadai, an ruwaito cewa kusan 'yan ci-rani 60,900 ne suka isa Yemen sau da yawa ba tare da wani abin dogaro ba.
A farkon wannan watan, gwamnatin da Houthi ke jagoranta ta bayyana cewa hare-haren jiragen saman Amurka a wurin man Ras Isa da ke bakin tekun tekun maliya sun kashe aƙalla mutane 74 tare da jikkata wasu 171.
Gwamnatin ta ce wurin na Ras Isa cibiyar fararen hula ce, kuma hare-haren sun zama "laifin yaki".
Centcom ta bayyana cewa hare-haren sun lalata damar da Ras Isa ke da ita na karɓar man fetur, kuma hakan zai shafi Houthi ba kawai wajen gudanar da ayyukansu ba, har ma wajen tara miliyoyin daloli don ayyukan ta'addanci".
A watan da ya gabata, Trump ya umarci kai manyan hare-hare a wuraren da Houthi ke iko da su, tare da barazanar cewa za su "shafe su gaba ɗaya".
Haka kuma ya gargadi Iran da kada ta bai wa ƙungiyar Houthi makamai — wanda Iran ke ci gaba da musantawa.
A ranar Lahadi, Centcom ta bayyana cewa za su "ci gaba da ƙara matsin lamba har sai an cimma burin dawo da 'yancin zirga-zirgar jiragen ruwa da kuma karfafa matsayin Amurka na daƙile barazana a yankin."
Tun daga watan Nuwamba 2023, Houthi sun kai hare-hare kan jiragen kasuwanci da dama a Tekun maliya da Tekun Aden ta hanyar harba makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki da kuma ƙananan kwale-kwale. Sun kuma nutar da jirage guda biyu tare da ƙwace guda ɗaya, sannan kuma sun kashe matuƙa hudu.
Ƙungiyar Houthi ta ce tana kai hare-haren ne domin goyon bayan Falasdinawa a yaƙin da ke tsakanin Isra'ila da Hamas a Gaza, kuma sau da dama suna iƙirarin cewa suna kai farmaki ne kawai kan jiragen da ke da alaƙa da Isra'ila, Amurka ko Birtaniya.
Hare-haren sun ci gaba duk da kasancewar jiragen yaƙin ƙasashen yamma a Tekun maliya da Tekun Aden da nufin kare jiragen kasuwanci a bara.
Bayan karɓar mulki a watan Janairu, Trump ya sake sanya 'yan Houthi cikin jerin "Ƙungiyoyin ta'addanci na ƙasashen waje", matsayin da gwamnatin Biden ta cire a da, tana mai cewa hakan na da nufin rage tsananin bala'in jin ƙai a ƙasar.
A cikin shekaru goma da suka gabata, yaƙin basasa ya lalata Yemen, wanda ya ƙara muni bayan da 'yan Houthi suka ƙwace ikon arewa maso yammacin ƙasar daga hannun gwamnati da duniya ta amince da ita, sannan wata kawance da Saudiyya ke jagoranta tare da goyon bayan Amurka domin dawo da gwamnatin.
Rahotanni sun nuna cewa yaƙi ya hallaka mutane sama da 150,000, tare da haddasa mummunan bala'in jin ƙai, inda mutane miliyan 4.8 suka rasa matsugunansu, sannan kusan rabin al'ummar ƙasar wato miliyan 19.5 — ke buƙatar taimakon gaggawa.