Wane ƙalubale ne ɓangaren shari'a a Najeriya ke fuskanta?

Asalin hoton, Supreme Court
Alkaliyar Alkalan Najeriya mai shari'a Kudirat Kekere Ekun, ta bayyana takaicinta kan yadda wasu alkalai a kasar ke bata wa ɓangaren shari'ar kasar suna.
Yayin da take jawabi a wajen wani taro a Legas a karshen mako, Kekere Ekun, ta ce darajar bangaren na zubewa a idon yan Najeriya, don haka dole ne alkalan su kaucewa wannan dabi'a.
A Najeriayar dai an jima ana zargin cin hanci da rashawa a bangaren shari'ar kasar, da kuma yadda yan siyasa da masu karfin fada a ji ke tasiri a hukunce hukuncen da ake yankewa.
A cewar Mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun, akwai alkalai da dama da ke iya bakin kokarinsu wajen kamanta adalci bisa gaskiya, sai dai kalilan daga cikinsu, da ke biyewa son duniya na bata wa bangaren shari’r kasar suna, wani abua da ke haifar da rashin yadda daga jama’a, musamman masu neman adalci da ke kallon bangaren a matsayin mataki na karshe na samun adalci.
A don haka ne ma ta roki alkalan su dubi Allah su tuna cewa za su tashi gaban ubangiji, don bada ba’asin kowane hukunci da suka yanke a nan gidan duniya.
Comrade Kabiru Sa’idu Dakata, shugaban kungiyar CAJA mai fafutukar tabbatar da adalci da daidaito a Najeriyar, ya ce kalaman alkaliyar alkalan sun tabbatar da abun da suka jima suna fadi, sai dai a yanzu wannan matsalar ta wuce intaha.
Kabiru Dakata ya ce tasirin da mafi akasarin ƴan siyasa suka yi a wasu fannonin, yanzu sun doshi ɓangaren shari'a domin shi ma su lalata shi.
"Wani alƙali ya bada umarni ko oda, amman sai ka samu wani alƙalin da yake da irin matsayinsa, ya bada wata odar ko umarni da ya sha banban da wannan, a junan su ma suna lalata martabar aikin."
Barista Bello Galadi, tsohon shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya NBA reshen jihar Zamfara, wanda ɗaya ne daga cikin masu mu'amala da alƙalan, ya ce " Duk wanda yake da alaƙa da ɓangaren shari'a ya san gaskiya ce ta faɗi, sai dai wanda abin ya shafa ya zama maganar ba ta mashi dadi ba."
A Najeriya dai ba safai aka fiye jin irin wannan daga bakin mahukunta a bangaren shari’ar kasar ba, ballantana ma shugabar alkalan baki daya, duk da cewa mutane da dama a kasar sun jima suna zargin ana tafka cin hanci da rashawa a bangaren, har ta kai ga masu neman adalci na fidda rai.
Wani batu da a baya bayan nan ya kara zafafa irin wadannan zarge zarge, shi ne yadda wasu alkalai suka yi ta bayar da hukunce hukunce masu cin karo da juna a wasu jihohi, har ta kai majalisar shari’ar kasar na gayyatar wadannan alkalai don bada ba’asi.











