Masu jiran a zartar musu da hukuncin kisa na ƙaruwa a Najeriya

Conviction

Ɗaurarru fiye da 3200 ne a gidajen yarin Najeriya ke jiran a zartar musu hukuncin kisa, kamar yadda hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya ta bayyana.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ambato mai magana da yawun hukumar Abubakar Umar yana cewa ba ko yaushe, ake zartar da hukuncin kisa nan take da zarar kotu ta yanke hukunci ba.

Ya ce sau da yawa, fursunonin da aka yanke wa hukuncin kisa kan shafe tsawon lokaci a halin rashin tabbas, daidai lokacin da ake ɗaukaka ƙararraki.

A watan Yulin bara, jaridar Punch ta ambato hukumar kula da gidajen yarin Najeriya na cewa adadin waɗanda ke zaman jiran a zartar musu da hukuncin kisa ya kai 3,145.

Hakan dai na nufin a cikin wata tara kawai, mutum 153 kotuna suka sake yanke wa hukuncin kisa a Najeriya.

Wani rahoton Amnesty International na 2021, ya sanya Najeriya a matsayin ta uku a duniya cikin jerin ƙasashen masu yawan ɗaurarru da ke jiran a kashe su.

Mai magana da yawun hukumar gidajen yarin Najeriya ya ce "Ɗaurarrun da ke zaman jiran kisa na rayuwa ne a ɓangarensu daban, yayin da wasu kan kwashe fiye da shekara 15 suna jiran a zartar musu da hukunci, bayan kotu ta yanke shari'a.

A cewarsa mutum 3,298 ne suke jiran hauni ya aiwatar da hukuncin da aka yanke musu bayan kotuna sun same su da laifi.

Ya kuma ce adadin masu jiran a zartar musu da hukuncin kisan ya kai kashi 4.5 na illahirin ɗaurarrun da ke tsare a ƙasar.

Abubakar Umar ya ƙara da cewa ana ɗaure da wasu masu zaman jiran a zartar musu hukuncin kisa tun lokacin da aka kama su, har zuwa lokacin da ake yi musu shari'a, kafin a yanke musu hukunci.

Ya ce da yawan mutanen sun aikata laifuka ne kamar kisan kai da fashi da ta'addanci da sauransu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rahoton Amnesty International dai ya nuna cewa ƙasashen Iraƙi da Pakistan ne kawai suka fi Najeriya yawan fursunonin da ke jiran a aiwatar da hukuncin kisa a kansu.

Kuma ƙasashen waɗanda suka haɗar da Amurka da Bangladesh da Malaysia da Vietnam da Algeria da kuma Sri Lanka, su ne ke da kashi 82% na ɗaukacin fursunonin da aka yanke wa hukuncin kisa a duniya.

Sai dai, Abubakar Umar ya ce wani abu shi ne a gidajen yarin Najeriya suna shigar da irin waɗannan fursunoni cikin harkokin da za su canza rayuwarsu da gyara musu hali.

Haka zalika, suna sanya su cikin wasu shirye-shiryen kyautata rayuwa kamar tausasa zuciya da ilmin sanin haƙƙoƙin da suka rataya a kan ɗan ƙasa da kuma sana'o'i.

Ya ce suka ba da shawara ga hukumomi don a yi rangwame ga wasu da suka nuna himma da ƙwazo da aiki tuƙuru da kuma ɗa'a.

Mai magana da yawun hukumar kula da gidajen yarin ya ce ana kashe irin waɗannan fursunoni da yawa a shekarun baya, kafin ƙaruwar ƙungiyoyi da hukumomin kare 'yancin ɗan'adam.

A cewarsa, yanzu akwai kamar wata taƙaitacciyar dakatarwa kan zartar da hukuncin kisa.

“Ƙaruwar ayyukan ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam ta sa gwamnatoci da yawa suna gujewa sa hannu kan takardun shari'a don kashe irin waɗannan masu laifi", in ji jami'in hukumar gidan yarin ta Najeriya.

Abubakar Umar ya ce karo na ƙarshe da aka aiwatar da hukuncin kisa shi ne cikin shekara ta 2016 a jihar Edo.

Ya ce suna ƙarfafa gwiwar gwamnonin da ke ɗari-ɗari wajen sa hannu kan takardun hukuncin kisa, su yi musu rangwame a hukuncin da aka yanke musu.