Dalilan APC huɗu na neman kotu ta soke zaɓen Abba Gida-Gida

Asalin hoton, Gawuna Media
Jam'iyyar APC reshen jihar Kano ta shigar da ƙara gaban kotun ƙorafe-ƙorafen zaɓe, inda take ƙalubalantar nasarar Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan Kano a zaɓen 18 ga watan Maris ɗin 2023.
Cikin ɓangarorin da jam'iyyar mai mulki ke ƙara a gaban kotun, har da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ɗan takarar da aka ayyana a matsayin wanda ya ci zaɓen gwamnan Kano, da kuma jam'iyyarsa ta NNPP.
Ta ce Abba Gida-Gida, bai ci zaɓen gwamnan Kano da halastattun ƙuri'u ba.
Mashawarcin APC ta Kano kan harkokin shari'a, Barista Abdullahi Adamu Fagge, kuma ɗaya daga cikin lauyoyin da ke wakiltar jam'iyyar ya shaida wa BBC cewa sun nemi kotu ta ayyana ɗan takarar jam'iyyarsu na APC, matsayin wanda yake da rinjayen halastattun ƙuri'u.
"Saboda shi wanda aka ayyana ya ci zaɓe, bai ci da halastattun ƙuri'u ba, in ji lauyan.
Haka kuma, akwai soke-soken ƙuri'un da aka yi, kuma ƙuri'un da aka soke sun zarce tazarar da ke tsakanin ƙuri'un Abba Kabir Yusuf da mai biye masa Nasiru Yusuf Gawuna.
Jami'in sanar da sakamakon zaɓen gwamnan Kano na watan Maris, Farfesa Ahmad Doko Ibrahim ya bayyana cewa zaɓaɓɓen gwamnan ya samu nasara ne da ratar ƙuri'a 128,897.
Sauran ƙorafe-ƙorafen APC kan Abba Gida-Gida
Haka zalika, Barista Abdullahi Adamu Fagge ya kuma ce wani ƙarin ƙorafi da suke da shi, shi ne wanda aka ayyana cewa ya ci zaɓe na NNPP, sunansa ba ya cikin rijistar jam'iyyar NNPP.
Kuma Jam'iyyar NNPP ba ta gudanar da zaɓen fitar da gwani ga masu neman takara, kafin zaɓen gwamnan Kano ba.
Lauyan ya ce "waɗannan suna cikin dalilai da suka sa muka shigar da ƙara gaban kotu, muna ƙalubalantar zaɓen gwamnan Kano".
Shin me APC take so daga kotu?
Bar Abdullahi Fagge ya ce "Muna neman kotu ta ayyana mu a matsayin mu ne muka ci zaɓe da halastattun ƙuri'u mafi rinjaye".
Idan kuma haka ba ta samu ba, jam'iyyar APC ta buƙaci a ayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba, tare da ba da umarnin sake zaɓe a tashoshin zaɓen da aka soke.
"A sake zaɓe a guraren da muke maganar duk an sossoke a dalilin soke zaɓen wanda in aka sake shi, shi ne kuma za a ayyana waye ya ci zaɓen.
Wato maganar a ayyana inkwankulusib a wasu gurare, wanda hukumar zaɓe ce da kanta duk ta soke".
Jami'in na APC ya ce sun tanadi hujjoji, suna da su, abubuwa ne da suka faru
"Na farko ma wanda ya fito ƙarara, ga shi kowa ya ji, ya gani, shi ne guraren da aka soke zaɓukan.
Wanda kuma bambanci (na ƙuri'u) tsakanin wanda ya yi nasara, da kuma me biye masa, ya fi yawan da (ƙuri'un) da aka soke" mashawarci kan harkokin shari'ar na APCn Kano ya bayyana.
Yanzu mene ne mataki na gaba?
Lauyan na APC ya shaida wa BBC cewa kotun za ta fara zaman sauraron wannan ƙara ne bayan kowanne ɓangare ya gama shigar da buƙatunsa.
Ya ce a yanzu kotun tana zaman wucin gadi, don sauraren masu ƙorafe-ƙorafen da ke neman umarnin samun damar a ba su wasu takardu da suka danganci zaɓen.
"Zama na a fara sauraren shari'a sai kowanne ɓangare ya shigar da nasa takardu" in ji Barista Fagge.
Waɗanda ake ƙara dai wato Abba Kabir Yusuf da NNPP da kuma hukumar zaɓe ta INEC suna da tsawon mako don mayar da martani kan ƙorafe-ƙorafen da jam'iyyar APC ta shigar a kansu.











