Abu takwas game da Abba Kabir Yusuf zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano

Abba

Asalin hoton, Twitter/Abba Kabir

A ranar Litinin ne hukumar zaɓe mai zaman kanta ta sanar da Abba Kabir Yusuf wanda ake yi wa laƙabi da Abba Gida-Gida a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano.

Ga abu takwas da ya kamata ku sani a kansa:

  • An haife shi ranar 5 ga watan Janairu, 1963 a ƙaramar hukumar Gaya ta jihar Kano.
  • Ya yi karatun firamare a makarantar gwamnati da ke Sumaila Primary School sannan kuma ya yi karatun sakandire a makarantar gwamnati ta Lautai a Gumel da ke jihar Jigawa.
  • Abba ya yi karatun difloma a Kwalejin Kimiya da Fasaha ta Mubi sai kuma babbar difloma a kwalejin kimiya da fasaha ta Kaduna watau Kaduna Polytechnic.
  • Ya yi karatun digirinsa na biyu a jami'ar Bayero ta Kano a fannin harkokin kasuwanci.
  • Tsohon kwamishinan ayyuka a jihar Kano a zamanin mulkin Rabi'u Musa Kwankwaso.
  • Abba gida-gida ya yi takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Kano a shekarar 2019 amma bai samu nasara ba.
  • Yana da mata biyu da ‘ya’ya da dama.
  • Ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kano a ranar 20 ga watan Maris na 2023.