Ko zuwan sabon gero zai kawo sauƙin matsin rayuwa a Najeriya?

    • Marubuci, Aisha Shariff Bappa & Mukhtari Bawa
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Cinikin sabon gero ya buɗe kuma mutane na ta rububin kayan amfanin gona da ke fitowa baya-bayan nan a yankin kasuwar Kurugu cikin jihar Gombe, arewa maso gabashin Najeriya.

"Gaskiya ciniki haka, bana ya fi bara," in ji Mallam Ibrahim, wani mai aunar da hatsi a kasuwar ranar Laraba a kowanne mako.

"Yanzu haka, an fi ciniki, sosai ma."

Zuwan sabon amfanin gona kamar gero ya sanya mutane farin ciki da kyakkyawan fatan samun wadatar abinci da kuma sauƙin rayuwa .

Dillalai sun ce gero a yankin Kwami, ƙaramar hukumar da kasuwar Kurugu take, nisan kilomita 36 daga babban birnin jihar Gombe, ya yi amfani matuƙa a bana sannan ya fara zuwa kasuwa da daraja sosai.

Mallam Abbati Abba Kyari, wani babban mai hada-hadar hatsi a Kurugu ya ce a ƙiyasi an sayar da buhun sabon gero kimanin dubu a Larabar wancan mako, duk da yake ba a daɗe da fara karyo tumu ba. Masu saye, a cewarsa na rububin sabon amfanin.

Buhun sabon gero ɗaya, in ji shi an sayar da shi a kan naira 72,000 zuwa 65,000.

"Kuma ko a cikin sabbin, ana samu ɗanye(n gero) sharaf, a kan naira 55,000."

Ya ce buhun tsohon tsohon gero yana kai wa 80,000 zuwa 82,0000.

Zuwan sabon geron a wannan lokaci, wata babbar ni’ima ce. ‘Yan Najeriya a yanzu na kokawa da tsananin tsadar kayan abinci da matsin rayuwa.

Suna cike da fatan cewa zuwan sabon amfanin gona, zai taimaka wajen kawo sauƙi a halin tsananin da suke ciki. Kuma da yake baya ba ta da kaɗan, komawar da muka yi kasuwar Kurugu a Larabar baya-bayan nan, ya fara tabbatar da wannan hasashe nasu.

'Na yi niyyar sayen buhu huɗu amma na sayi bakwai'

Wani ɗan kasuwa mai awon hatsi, Ɗan Malikin Hamma Dukkuju ya ce ya ƙara yawan hatsin da yake saya saboda farashin gero ya sake faɗuwa.

"A yadda da muke sayen sabon gero, muna saya naira 70,000 - 72,000 amma yau gero ya dawo naira 67,000 ya dawo naira 60,000, yanzu ma muna samun gero a 55,000," in ji shi.

Ya ce a baya yakan sayi buhu uku ne zuwa huɗu, amma a Larabar da ta wuce, sai da ya sayi buhu bakwai.

A cewarsa, yakan sayi hatsi ne a kasuwa, sannan shi kuma sai ya je ya sayar wa masu shaguna a cikin gari, da ke aunar wa mutanen gari.

"A wancan mako, muna sayar da mudu naira 800, amma yanzu kam in muka koma ba zai wuce 700 ba."

Shi kuma, wani manomi da ya kawo geronsa buhu biyar don sayarwa, ga alama bai yi farin ciki da wannan sabon al'amari ba.

Muhammadu Jauro daga Daɓar Fulani ya ce ala dole zai sayar da geronsa a kan sabon farashin. "Satin da ya wuce ana sayar da buhu a kan 75,000 zuwa 70,000 amma yanzu 50,000, kuma dole a haka za mu sayar da shi."

Ya ce bashin da ke kansa da sauran hidindimun gida su ne suka tilasta masa sayar da geron a kan wannan farashi.

Ya kuma ce yanzu haka gonar shinkafarsa tana ta yaushi, saboda tana buƙatar taki, kuma bai tanadi komai ba.

Idan ba dole ba, in ji shi, da ya ajiye geronsa a gida har zuwa lokacin da zai yi daraja, kafin ya sayar.

Manoman Najeriya kamar Muhammadu Jauro na kokawa da tsadar takin zamani da kuma na sauran kayan amfanin gona. Suna cewa buhun takin da bai fi 5,000 zuwa 7,000 ba a ƴan shekarun baya, a yanzu sai ka zuba naira 40,000 kafin ka same shi.

Kamar manoma, su ma masu awo na kokawa

Wata dattijuwa mai suna Adama da ta ce ita ma ta je cin kasuwa ne sayen sabon geron da za ta yi fura.

Ta ce ta sayi mudu biyu na sabon gero a kan naira 900 duk mudu ɗaya. Duk da tsadarsa, ta ce ta gwammace sayen sabon a kan tsohon gero. Mudu ɗaya na tsohon gero, ana sayar da shi a kan naira 1,200.

"To, ya muka iya?" In ji Malama Adama.

Sabuwar masara da sabuwar gyaɗa ‘yar Taraba, su ma duk an fara kawo su kasuwa.

Ibrahim Saleh ya ce ya sayi mudun tsohuwar masara a kan naira 1,200, bambancin farashinta da na sabuwa, in ji shi bai taka kara ya karya ba.

"Sauƙi dai sai wajen Allah kawai."

Ya ce sabuwar masara ana aunar mudu ɗaya a kan naira 1,050, ga shi kuma ba da auki kamar tsohuwar masara da ta bushe idan an niƙa ta.

'Farashin masara da dawa ya tashi a kwanan nan'

Wani ƙaramin mai hada-hadar hatsi, Mallam Ibrahim da ke aunar da kwano-kwano a kasuwar Kurugu ya ce a ‘yan makonnin nan, kayan amfanin gona irinsu dawa da masara duk sun ƙara kuɗi.

Ya ce duk da haka bana sun fi samun ciniki, idan an kwatanta da bara. In ji shi: "Da ma ai babu ita take kawo tsadar".

Da yake yanzu ne sabon amfanin gona ya fara fitowa, mafi yawan al’umma na fatan cewa damunar bana za ta yi kyau. Kuma za a samu yabanya mai yawa da za ta karyar da farashin kayan abinci idan kaka ta zo.

Ko da yake, dillalan hatsi a kasuwar Kurugu kamar Mallam Abbati Abba Kyari ba su da ƙwarin gwiwa. Ya yi hasashen cewa wahalar da za ta sanya manoma da dama su zaɓi ajiye amfanin gonarsu a gida a kan sayarwa.

"Ko da sabon ta yi yawa, yadda wasu suka ajiye buhu goma, bana wani zai ajiye buhu 30. In ya ajiye a 30,000, kuma ya je 100,000, 80,000, ka ga mai buhu ɗaya zai ninka kuɗin amfaninsa."

Ya ce ba ya tsammanin amfanin gona zai faɗi ƙasa sosai ba, daga yadda ya nuna.

A cewar Abbati Abba Kyari kusan duk amfani gona sun ninka farashinsu idan an kwatanta da yadda ake sayarwa a baya.

"Ko gyaɗa, a baya farashin buhu ɗaya naira 50,000 zuwa 60,000, amma yanzu sabuwa ƴar Taraba na kai wa sama da 100,000."

Gwamnatin Nijeriya dai a baya-bayan nan, ta ce ta ɗauke wa ‘yan kasuwa harajin shigo da wasu kayan abinci zuwa ƙasar, da nufin cike giɓin abincin da al’ummar ƙasar ke buƙata.

Sai dai dillalan hatsi a kasuwar Kurugu na cewa kamata ya yi hukumomi su mayar da hankali wajen yin abin da zai kawo sauƙi ga farashin takin zamani da sauran kayan noma, matuƙar da gaske take yi a burin samun sauƙi ga kayan abinci a nan kusa.