Darussa biyar da za a koya daga siyasar Buhari

Asalin hoton, Fadar shugaban Najeriya
Masana da masu sharhin al'amuran yau da kullum sun fara tsokaci game da rayuwar tsohon shugaban Najeriya, Marigayi Muhammadu Buhari.
Buhari - wanda ya rasu ranar Lahadi ya mulki Najeriya a ƙarƙashin mulkin soji da na farar hula.
Shi ne ɗan siyasar da ya kafa tarihin kayar da shugaban ƙasa mai ci, yayain da yake jam'iyyar hamayya.
Tsohon shugaban ƙasar ya kasance mafi farin jini tsakanin ƴansiyasar ƙasar.
Rayuwar Muhammadu Buhari - wanda ya shafe shekaru yana gwagwarmaya a fagen mulki da siyasar Najeriya - na cike da darussan da za a iya koya daga gareta, kamar yadda Farfesa Abubakar Kari na Jami'ar Abuja ya bayyana.
''Akwai darussan manya-manya da dama waɗanda ƴan Najeriya za su iya ɗauka daga rayuwar Buhari'', in ji Farfesa Kari.
Ya kuma zayyano darussan kamar haka:
Jajircewa
Farfesa Abubakar Kari ya ce tsohon shugaban ƙasar ya kasance mutum mai jajircewa da naci kan duk abin da ya sanya gaba.
Mutum ne da ba ya yarda gwiwarsa ta yi sanyi kan duk wani ƙudirin da yake son cimmawa, kamar yadda Farfesa Kari ya yi bayani.
''Hakan ne ma ya sanya ya yi takara a baya har sau uku bai yi nasara ba ,amma duk da haka bai sare ba, har sai da ya cimma burinsa a karo na huɗu a 2015'', in ji masanin siyasar.
''A duka waɗannan lokuta uku da ya yi takara bai yi nasara ba, yana zuwa kotu tun daga kan ta ƙorafin zaɓe har zuwa kotun ƙoli, sannan ya haƙura'', in ji Farfesa Kari.
Masanin siyasar ya ce wannan ba ƙaramin darasi ba ne a rayuwa da ake son kowane ɗan'adam ya siffanta da shi.
Gaskiya da riƙon amana

Asalin hoton, Fadar shugaban Najeriya
Duk wanda ya san Buhari ya son ana kiransa da ''Mai gaskiya''.
Farfesa Kari ya ce za a iya cewa na kusa da shi sun aikata ba daidai ba, ''Amma dai shi har yanzu babau wanda zai ce maka an zargi Buhari da cin hanci da rashawa ko wadaƙa da dukiyar ƙasa ba'', in ji shi.
''Wannan kuma abin mamaki ne saboda mutumin nan ya yi gwamna, ya yi ministan man fetur, ya yi shugaban ƙasa na soja, ya yi shugaban hukumar kula da kuɗaɗen rarar man fetur ta PTF, sannan ya yi shugaban ƙasa na farar hula tsawon shekara takwas''.
Farfesa Kari ya ƙara da cewa ''kuma duka waɗannan lokatuka a ce ba a taɓa zarginsa da aikata ba daidai ba ta fuskar almundahana ko ta'annati da dukiyar ƙasa a tsawon lokacin da ya kwashe a kan mulki''.
Bin doka da ƙa'ida
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wani babban darasi da ya kamata a koya game da rayuwar siyasar Buhari shi ne bin doka da tsari musamman ga ƴan siyasar ƙasar a cewar Farfesa Kari.
''Wani abin mamaki shi ne Buhari tarbiyyarsa ta gidan soja ce, amma kuma halinsa na dimokraɗiyya ne, ya ma fi waɗanda suke iƙirarin cewa su ne ƴan dimokraɗiyyarma'', in ji masanin siyasar.
A lokuta da dama Buhari ya sha faɗa yana nanatawa cewa shi ba ya son yin katsalandan a ayyukan da ba nasa ba.
''Shi ya sa ma ya ƙi sanya baki a zaɓukan shugabannin majalisun dokokin ƙasar a zamanin mulkinsa'', in ji shi.
Farfesa Kari ya ce kuma wannan hali nasa ya taimaka wa ƴan siyasa wajen samun nasara, kasancewar ba ya tsoma baki a batun da bai shafe shi ba, ballantana ya yi ƙarfa-ƙarfa wajen saka ɗan takara.
Ko saƙon ta'aziyyar da tsohon gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki ya yi kan rasuwar Buhari, ya ce Buhari ya yi masa rana a lokacin da jam'iyyar APC ta juya masa baya, har shugabanninta suka ce ba za a ba shi takara ba, amma Buhari ya hana aka kuma ba shi.
''Akwai mutane da dama da suka ci zaɓe suka samu muƙamai saboda Buhari ya amincewa a yi ƙarfa-ƙarfa'', in ji shi.
Ya kuma ce dimokraɗiyya za ta ginu ne kawai idan aka bai wa mutane dama su zaɓi abin da suke so.
Wasu ma na ganin ko nasarar da Shugaba Tinubu ya samu a zaɓen fitar da gwani, ta samu ne saboda Buhari ya ce a je a yi zaɓe duk wanda ya ci a ba shi, a cewar Farfesa Kari.
''Amma akwai hujjoji da alamun da ke nuna cewa wasu makusantan Buharin za binsu ba Tinubu ba ne'', in ji masanin siyasar.

Asalin hoton, Fadar shugaban Najeriya
Son zaman lafiya
Farfesa Kari ya ce za a iya bayyana marogayin da mutum mai son zaman lafiya, wanda ya ba son tashin hankali.
''A duka lokutan da yake tsayawa takara, bai taɓa kiran magoya bayansa su yi tashin hankali saboda bai amu nasara ba'', in ji Farfesa Kari.
''Bai taɓa yin barazana ba , bai taɓa cewa mutane su ɗaga hankali ba, ko barazana ga ƴanci da zaman lafiyar ƙasa ba'', kamar yadda Farfesa Kari.
Wannan babban darasi ne a cewar masanin siyasar.
Rashin tsawatarwa
Masanin harkokin siyasar ya ce wani darasi da shugabanni ya kamata su koya a tsarin siyasar Buhari shi ne rashin tsawatarwa.
''Shi Buhari mutum ne da idan ya yarda da kai, to shikenan ya yarda da kai, komai za a ce a kanka zai yi wahala ya yarda'', in ji shi.
''Shi idan ya ba ka aiki, to shikenanan ba zai riƙa bibiyarka yana ganin abubuwan da kake yi ba'', in Farfesa Kari
A baya wani daga cikin tsoffin ministacinsa ya taɓa bayyana cewa idan Buhari ya ba ka aiki ba zai riƙa bibiyarka don sanin matakin da ake ciki.
Farfesa Kari ya ce wannan babban darasi ne da ya kamata shugabannin da za su zo nan gaba su riƙa la'akari da shi.











