Yadda wata mata ta kashe kanta bayan an samu kuskuren rage mata fansho

Tamara Logan

Asalin hoton, Handout

Lokacin karatu: Minti 2

Wata mata da ta ke da rauni ta kashe kanta bayan da ta samu wasika cewa an rage mata kudin fansho da alawus din da ake bata inda daga baya kuma aka gano cewa kuskure ne.

Tamara Logan, mai kimanin shekaru 28 da haihuwa, ta mutu ne a babban asibitin da ke Tameside a ranar 20 ga watan Mayun 2025, kwanaki biyu bayan an same ta a gidanta a halin rai kwakwai mutu kwakwai inda aka garzaya da ita asibiti daga bisani kuma ta ce ga garinku nan.

Jami'ai a ma'aikatar shari'a ta Birtaniya sun gano cewa dama can Tamara tana da tarihin cutar da kanta.

Hukumar kula da 'yan fansho, ta dauki bayanan jami'an da muhimmanci daga baya ta bayar da cikakken bayani akan matar da mutuwarta.

Tun da farko an gano cewa an samun matsaloli wajen biyan Tamara kudaden alawus dinta domin wnai lokaci akan yanke mata wani abu daga ciki, irin hakan ne ya fara sanya mata damuwa a zuciyarta har ta dauki matakin kashe kanta a ranar 18 ga watan Mayun 2025.

Bayan sauraron shari'ar da aka yi akan mutuwat matar, jami'in ma'aikatar shari'ar ya rubutawa hukumar kula da 'yan fansho akan ta yi karin haske akan irin abubuwan da suka dami Tamara saboda a kiyaye sake afkuwar wani abu makamancin wannan.

A ka'ida dai Tamara, wadda 'yar asalin Glossop da ke Derbyshire a Manchester ce, cikakkiyar ma'aikaciya ce wadda ta cancanci biyanta cikakken albashi da kuma kara yawan alawus din da ake bata akai-akai.

A farkon 2025 ne aka yi kuskuren cire ta daga biyan alawus alawus din da ake bata wanda daga bisani aka gano kuskuren.

Anan ne aka aike mata da wasika cewa an rage yawan kudin alawud din da ake bata abin da ya sanya ta fara shiga damuwa saboda amfanin da ta ke yi kudin wajen byan wasu bukatunta na yau da kullum.

Ta fara sake-sake kan yada zata tafiyar da rayuwarta, daga na ne kuma ta yanke shawarar daukar matakin kashe kanta.

Tuni dai mai magana da yawun hukumar kula da 'yan fanshon ta ce nemi afuwar kuskuren da ta yi da kuma mika sakon ta'aziyyarta ga iyalan Tamara.