Yadda Taliban ke soke hukuncin kotuna da ke raba auren yara mata a Afghanistan

    • Marubuci, Mamoon Durrani
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Afghan Service
    • Marubuci, Kawoon Khamoosh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
    • Aiko rahoto daga, Kabul
  • Lokacin karatu: Minti 4

Akwai wata mata da ke zaman mafaka a ƙarƙashin wata bishiya tsakanin wasu hanyoyi biyu masu cike da cunkoso, tana kuma riƙe da tarin takardu.

Waɗannan takardu sun fi komai muhimmanci a wajen Bibi Nazdana.

Takardun saki ne da ta samu bayan gwagwarmayar zuwa kotu tsawon shekara biyu, domin ganin ta samu sararawa a matsayinta na matashiya.

Sakin da Nazdana ta samu na cikin gomman sakin aure da kotu ta yi wanda aka yi watsi da shi a wannan wata tun bayan da Taliban ta karɓi iko shekara uku da suka wuce.

A cikin kwana goma kaɗai, Taliban ta je ta samu mijin da Nazdana ta yi aure da shi da kuma buƙatar kotu ta soke takardar sakin da ta bayar.

Tun da farko Hekmatullah ya fito ya buƙaci a ba shi matarsa Nazdana lokacin da take shekara 15, shekara takwas tun bayan da mahaifinta ya amince da abin da aka fi sani da 'aure mara kyau', wanda ke buƙatar mayar da abokin gaba na iyali zuwa aboki.

Nan da nan ta nufi kotu - wanda a lokacin ke ƙarƙashin ikon gwamnatin Afghanistan da Amurka ke marawa baya - domin neman a raba su, inda ta sha faɗa musu cewa ba za ta auri manomin ba, wanda yanzu ke da shekara 20.

An shafe shkara biyu, amma daga baya kotun ta amince da buƙatarta: "Kotun ta taya ni murna da kuma cewa, 'a yanzu mun raba ku kuma za ki iya auren kowaye."

Sai dai bayan Hekmatullah ya ƙalubalanci hukuncin a 2021, an faɗa wa Nazdana cewa ba za ta iya sake yin wani abu kan hukuncin ba.

"A kotun, Taliban sun faɗa min cewa ka da na koma kotun saboda hakan ya saɓa wa Shari'a. Sun ce ɗan uwana ya wakilce ni maimakon ni," in ji Nazdana.

"Sun ce idan ba mu bi umarnin ba, za su tirsasa auren ƙanwata Nazdana zuwa ga Hekmatullah," in ji Shams ɗan uwanta.

Tsohon mijinta, wanda yanzu yake cikin Taliban, ya yi nasara a shari'ar. An ki saurarar bayanin Shams na cewa rayuwarta za ta shiga cikin matsala.

Daga bisani suka yanke shawarar tserewa.

Lokacin da Taliban ta karɓi iko shekara uku da suka wuce, sun yi alkawarin watsi da hukunce-hukunce na baya da aka yi domin yin komai bisa tsarin shari'a na addinin Musulunci.

Tun bayan nan, Taliban ta ce sun yi duba kan shari'o'i 355,000.

Yawancin shari'o'in sun kasance na manyan lafuka - kiyasi ya kuma nuna cewa kashi 40 sun shafi filaye sannan kashi 30 kuma kan matsaloli na iyalai ciki har da batun saki, kamar na Nazdana.

An fito da batun sakin da Nazdana ta samu ne bayan da BBC ta samu zuwa Kotun Koli a Kabul, babban birnin ƙasar.

Abdulwahid Haqani - jami'in yaɗa labarai a kotun kolin na Afghanistan - ya tabbatar da cewa an yanke hukuncin kuma an bai wa Hekmatullah nasara, inda ta ce an yanke hukuncin farko ne lokacin da ba ya nan.

Tsohuwar alkalin kotun kolin Fawzia Amini - wadda ta tsere daga kasar bayan da Taliban ta koma kan mulki - ta ce babu wani fata ta kare lafiyar mata a karkashin doka idan babu mata a kotuna.

"Mun taka muhimmiyar rawa," in ji ta. “Misali, dokar kawar da cin zarafin mata a shekarar 2009 na ɗaya daga cikin nasarorin da muka samu, mun kuma yi aiki da tsarin kula da matsuguni na mata, da kula da marayu da kuma dokar yaki da fataucin bil’adama da sauransu.

Har ila yau, ta yi watsi da batun soke hukunce-hukuncen baya da Taliban ta yi, kamar na Nazdana.

"Idan mace ta rabu da mijinta kuma takardun kotu sun kasance a matsayin shaida to hakan ya zauna. Hukunce-hukuncen shari'a ba za su canza ba saboda tsarin mulki ya canza," in ji Ms Amini.

Ta kara da cewa, "Dokokin mu sun wuce fiye da karni da yin su." “An yi su tun kafin a kafa Taliban.

"Dukkan ka'idojin dokoki, ciki har da na saki, an ɗauko su ne daga Alkur'ani."

Sai dai ƴan Taliban sun ce tsoffin shugabannin Afghanistan ba su da isashen ilimin addini.

Maimakon haka, sun dogara ne akan dokar addini, wadda ta samo asali tun ƙarni na takwas - duk da cewa an sabunta ta don "cika buƙatun yanzu", a cewar Abdulrahim Rashid.

"Tsoffin kotunan sun yanke hukunci ne bisa tsarin shari'a da kuma doka. Amma yanzu duk hukuncin yana kan Shari'a [dokar Musulunci]," in ji shi, yana nuna alfahari kan tarin shari'o'in da suka rigaya suka daidaita.

Ms Amini ba ta da sha'awar tsarin shari'ar Afghanistan.

"Ina da tambaya ga 'yan Taliban, shin iyayensu sun yi aure ne bisa waɗannan dokoki ko kuma bisa dokokin da 'ya'yansu za su rubuta?" Ta tambaya.

Ƙarƙashin bishiyar tsakanin hanyoyi biyu a wata ƙasa mai maƙwabtaka da ba a bayyana sunanta ba, babu ɗaya daga cikin wannan da ke da daɗi ga Nazdana.

Yanzu ta cika shekara 20, ta yi shekara guda a nan, tana rike da takardar saki da fatan wani ya taimake ta.

"Na buga kofofi da yawa ina neman taimako, ciki har da Majalisar Ɗinkin Duniya, amma babu wanda ya ji muryata," in ji ta.

"Ina goyon bayan? Ashe ban cancanci 'yanci a matsayina na mace ba?"

BBC ta kasa samun Hekmatullah domin jin ta bakinsa.