Makarantar da ɗalibai ke rayuwa tare da macizai da ƙaguwa a Najeriya

School children dey waka go dia class for one school for Rivers State
Lokacin karatu: Minti 6

A shekarar 1992 ne aka kafa makaratar firamare ta Migrant Fisherman School da ke ƙaramar hukumar Okrika a jihar Rivers da ke kudancin Najeriya.

Makarantar ta je-ka ka-dawo mai ɗalibai kimanin 150 da malamai 13, tana koyar da yara ne a matakin nazare da firamare daga kauyuka masu maƙwaftaka.

Gabanin kafa makarantar, yara na karatu ne a ƙasan bishiya, inda daga bisani ma'aikatar ilimi ta tarayyar Najeriya ta kai ɗauki, ta gina wa makarantar ajujuwa huɗu.

Picture show dilapidated state of St. Gabriel’s State School Oproama, Asari Toru LGA.
Bayanan hoto, Yawancin makarantu a jihar Rivers na cikin mummunan hali saboda lalacewar gine-gine

To amma a yanzu ajujuwan sun tsufa, kuma sun ji jiki, suna gab da rushewa.

Yayin da wakilin BBC, wanda ya yi amfani da kwale-kwale zuwa yankin ya isa, ya ga yadda rufin makarantar ya ɗage, ƙofofi da tagogi suke hankaɗe saboda rashin murfi sannan kuma simintin da aka yi a ƙasa ya dagargaje.

Malaman makarantar ba su da teburi ko kujerun zama, sai dai suna lallaɓawa ne da wani dogon benci da suka ajiye a kan baranda.

Pupils of Migrant Fishermen Children’s School Dic Fiberesima Ama, Okrika LGA of Rivers State with dia female teacher
Bayanan hoto, Many primary school pupils dey learn under dilapidated structures with leaking roofs and broken walls

A duk lokacin da aka samu ruwan sama mai ƙarfi, ruwa kan shafe makarantar, kuma kasancewar gishirin da ke ƙunshe a cikin ruwan teku na da illa, ya cinye ɓangarori da dama na bangon makarantar, wani ɓangaren kuma ya tsage, sannan wani ɓangaren ya dare, ya ɓangwale.

A duk lokacin aka kaɗa ƙaraurawar zuwa makaranta, ƙaguwa ce ta farko wajen amsawa, kasancewar makarantar na kusa ne da wani sunƙurun daji mai fadama, inda ɗalibai ke zuwa kamun kifi da halittun ruwa da zarar an tashi.

Haka nan a cikin dajin ɗalibai ke zagayawa domin yin ba-haya kasancewar babu ban-ɗaki a makarantar.

Wasu daga cikin ajujuwan kuma ba a iya shigar su sai an yi amfani da wata gadar katako, wadda aka haɗa da sanduna.

Haka nan kuma ajujuwan kan cika maƙil daruwa idan aka samu ruwan sama sanadiyyar ɗagewar rufi.

Wooden bridge wey dem dey call monkey bridge wey give access to some classroom blocks
Bayanan hoto, Ana amfani da gadar katako domin shiga waɗannan ajujuwa

Samuel, wanda yaransa ke halartar makarantar ya yi kira ga gwamnati ta kai musu ɗauki ta hanyar gyara makarantar, kasancewar suna fargabar cewa sauran ginin da ya rage a tsaye na iya faɗawa kan yaransu a kowane lokaci.

"Wannan ba wuri ne da duk wani mutum mai hankali zai zauna ba, to amma ba mu da zaɓi.

Wannan ce kawai hanyar da za mu bi domin yaranmu su samu ilimi, shi ya sa muke roƙon gwamnati ta taimaka ta gyara makarantar ta yadda ruwa zai daina dukan yaranmu idan sun je makaranta."

Back of one block of classroom for di Migrant Fishermen Children’s School, Dic Fiberesima Ama, e dey close to mangrove and water dey flow hit di clasrrom block.
Bayanan hoto, Yara na tsintar ƙananan dodon koɗi a ruwan da ke bayan makarantar a lokacin da aka tashi

Ƴaƴan Grace Minadiki uku ne suka kammala wannan makaranta, kuma a yanzu akwai yaranta biyu da ke makarantar.

Ta ce in ban da wasu mutane sun taimaka musu da kujeru da teburan roba, da yanzu duk yaran suna zama a ƙasa.

"Wannan makarantar za ta iya rushewa kowane lokaci daga yanzu, ba ma fatan hakan. Muna kuma tausaya wa malaman da ke shiga kwale-kwale a kowace rana suna zuwa domin koyar da yaranmu, amma a duk lokacin da aka yi ruwan sama to babu karatu domin ruwan na mamaye makarantar," in ji ta.

'Muna fama da macizai a makaranta'

Broken down ceilings, doors and windows for St. Gabriel’s State School Oproama, Asari Toru LGA
Bayanan hoto, Makarantar firamare ta St. Gabriel State School, Oproama a jihar Rivers
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A makarantar firamare ta St Gabriel State School Oproama da ke ƙaramar hukumar Asari Toru ta jihar Rivers ɗin kuwa, komai ya lalace.

Makarantar na amfani ne da ɗaya daga cikin gine-ginen makaranta da gwamnatin jiha ta gyara a shekarar 2013, to amma a yanzu a lalace take.

Akasarin kwanukan rufin makarantar sun cire, wasu kuma sun faɗa cikin ajujuwan.

Murafen ƙofa da tagogi sun lalace sannan mafi akasarin ajujuwan ba su zaunuwa, kuma gansa-kuka ce kawai ke yaɗuwa a ciki.

Babu teburin rubutu, babu kujerun zama, babu allon rubutu, kuma macizai da sauran ƙwari ne kawai suka mamaye makarantar.

Makarantar na da ɗalibai 68 da malamai 2 sai kuma wasu matasa ƴan balantiya da ke taimakawa.

Okinaye Otonye, daya daga cikin iyayen da yaranta ke zuwa makarantar na son ganin gwamnati ta gyara makarantar kasancewar akwai iyaye da dama da ba su amince su bar yaransu su halarci makaranatar ba.

Ta ce wasu iyayen sun gwammace su tura yaransu makarantu a wasu ƙauyukan da ke maƙwaftaka, kamar Buguma.

Bayan gyara ginin, ta kuma buƙaci a samu ƙarin malamai, kasancewar malamai biyu ne kacal a makarantar a yanzu.

Pupils and dia teacher inside classroom for St. Gabriel’s State School Oproama, Asari Toru LGA, Rivers State
Bayanan hoto, Macizai da ƙadangaru na hana koyarwa cikin kwanciyar hankali a makarantar, lamarin da ya sa iyaye da dama ba su son kawo yaransu

Wani dattijo a ƙauyen Oproama, Joshua Ikiriko ya ce kusan kullum sai sun kashe macizai, kuma da zarar aka ga macizai to dole ne a dakatar da karatu.

"Haka nan ma idan ruwan sama ya fado dole a tashi saboda babu inda yara za su fake. Dubi yadda makarantar take, babu wanda zai so ya kawo yaronsa wannan makaranta, saboda haka muna roƙon gwamnati ta gyara makarantar."

Dr. Anne Briggs-Famuyiwa ta ƙungiyar Readcycle, mai haɓɓaka ilimi da faɗakarwa kan sauyin yanayi ta ce sun lura cewa makarantu da dama sun lalace a jihar Rivers.

Ta ce suna ganin hakan ne sanadiyyar aikin da suke yi na bayar da gudumawar litattafai da kayan koyarwa a makarantu.

"A wasu lokutan za ka ga makaranta babu malamai, saboda haka yara sukan zo su yi ta wasa har zuwa lokacin tashi. Idan ka tambaye su, me ya sa ba za su koma gida ba? Sai su ce ba su son su koma gida saboda za a tura su aiki, sun gwammace su zauna a makarantar."

Ta ce hakan na jefa yara cikin hatsarin fadawa hannun waɗanda za su koya musu miyagun abubuwa ko kuma su ci zarafinsu.

Wide shot of Migrant Fishermen Children's School Dic Fiberesima Ama, Okrika LGA
Bayanan hoto, Ƙaguwa da kifaye na shiga makarantar kasancewar ruwan da ke fitowa daga teku kan mamaye harabar makarantar

'Za mu gyara makarantu a kasafin shekara ta 2026' - Fubara

Gwamnatin jihar Rivers ta ce za ta gyara makarantu a cikin kasafin kuɗinta na shekara ta 2026.

A lokacin da yake magana kan mummunan halin da ilimi ke ciki a jihar, ya ce matsalar ta samo asali a tsawon shekaru.

Sai dai ya ce za su saka batun gyara harkar ilimi a cikin kasafin 2026, musamman makarantun sakandare, kasancewar makarantun firamare na ƙarƙashin kulawar ƙananan hukumomi ne.

Tuni gwamnatin jihar ta sake amincewa da ɗaukar malaman firamare sama da 1,000 wadanda aka dakatar, sannan ya ce za su ɗauki wasu sabbin malaman.