Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane tasiri ficewar El-Rufai daga APC za ta yi?
Komawar da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ya yi zuwa jam'iyyar SDP, ya kawo karshen raɗe-raɗin da aka yi ta yi na jam'iyyar da El-Rufai zai koma, bayan da aka ga take-taken cewa yana shirin barin APC mai mulki.
A baya-bayan nan dai El-Rufai ya sha kokawa cewa jam'iyyar APC mai mulki ta sauka daga manufofin da aka kafata a kai.
Ana kuma hasashen watakila wasu ƴan siyasar ma za su iya bin sa zuwa jam'iyyar SDP da ya koma.
Masana harkokin siyasa dai na ganin ficewar El-Rufai daga APC za ta yi tasiri ganin cewa shi jigo ne a siyasar ƙasar.
Tasirin da ficewar El-Rufai za ta yi
"Wannan ficewa ta El-Rufai za ta yi tasirin gaske saboda shi hamshaƙin ɗan siyasa ne yana da ɗimbin goyon baya musamman a sassan arewacin Najeriya," a cewar Farfesa Abubakar Kari na jami'ar Abuja.
Ya ce kasancewar yana da alaƙa da manyan ƴan siyasa kuma ɗan boko - lamarin zai yi tasiri.
Masanin na harkokin siyasa ya ci gaba da cewa girman tasirin barin jam'iyyar APC da El-Rufai ya yi ba zai misaltu ba kasancewarsa kwararren ɗan siyasa wanda ya taɓa riƙe manyan mukamai da suka haɗa da ministan birnin tarayya Abuja da kuma gwamnan Kaduna.
"Za a ga tasiri mai girman gaske saboda El-Rufai ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa jam'iyyar APC," in ji Abubakar Kari.
Ya kuma ce ficewar tasa za ta zama share fage ga wasu gaggan ƴan siyasar da ke da jikakkiya da gwamnatin Bola Tinubu, inda ake hasashen da yawa za su bi bayansa nan ba da jimawa ba zuwa jam'iyyar ta SDP.
"Akwai waɗanda ke ganin ba a yi musu daidai ba ko kuma ba su samu abin da suke so, ba mamaki za su iya canza sheƙa," in ji masanin.
Ya kuma ce akwai raɗe-raɗen cewa ana son amfani da SDP a matsayin wata tunga ta adawa da gwamnatin Tinubu.
Sai dai ya ce ya yi wuri a san irin tasirin da hakan zai yi ga zaɓen 2027 da ke tafe.
"Tun da yanzu abubuwa suka fara faruwa zai wuri a faɗi irin tasirin ga zaɓe 2027, amma abin da ya fito fili shi ne ficewar Malam El-Rufai babban al'amari ne," in ji Farfesa Kari.
Sai dai a nasa ɓangare, Farfesa Tukur Abdulƙadir na Jami'ar jihar Kaduna ya ce ba za a iya gane tasirin da hakan zai yi yanzu ba sai nan gaba kaɗan.
"Yana cikin waɗanda suka kafa APC , tsohon gwamna ne kuma tsohon minista - sannan a baya yana cikin mutanen da suka goyi bayan Tinubu, wannan tabbas nakasu ne amma ba za a iya fayyace tasirinsa ba sai an yi zaɓe an gani," in ji Farfesa Abdulkadir.
Farfesa Tukur Abdulkadir ya ƙara da cewa a al'ada idan shekarar zaɓe ta zo za a samu masu sauya sheƙa saboda ba su samu abin da suke so ba.
"Ba abin mamaki ba ne idan waɗanda ke kusa da shi kuma suke goyon bayansa a jiharsa su bi shi zuwa inda ya je, sannan waɗanda ba su da ra'ayinsa kuma za su zauna," in ji shi.
'El-Rufai bai ji ɗaɗin abin da APC ta yi masa ba'
Dangane da dalilin da ya sa El-Rufa'i ya fice daga jam'iyyar APC, Farfesa Tukur Abdulƙadir ya ce sauya sheƙa na nuna alamun cewa Malam El-Rufai bai yi hakuri ba da abin da jam'iyyarsa ta yi masa, musamman kasa wucewa a lokacin tantance ministoci.
"Ba kowa za a yi wa haka ya ɗauki abin da daɗi ba, kuma hakan na cikin dalilan da suka sa ya bar APC," a cewar masanin."
To sai dai a sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X dangane da dalilinsa na ficewa daga jam'iyyar, Malam Nasir El-Rufai bai ambaci batun rashin samun muƙami ba, inda ya nuna ya bar APC ne saboda ta sauka daga kan turbar da suka ɗora ta.
"A ɓangarena na yi ƙoƙarin janyo hankali a ɓoye da kuma baya-bayan nan a bayyane game da inda jam'iyyar ta dosa.
"Saboda haka a wannan lokaci na yanke shawarar cewa ya zama wajibi na nemi wani wurin na daban a ƙoƙarina na tabbatar da manufofina na kawo cigaba." In ji Nasiru El-Rufai.