Me ya sa ake yin aiki kwana biyar a mako?

Wata mace cikin matuƙar gajiya na aiki da kwamfuta tare da abokan aikinta a wani taro.

Asalin hoton, Getty Images/Skynesher

Bayanan hoto, Wani sabon binciken masana ya gano cewa aikin kwana huɗu a mako na inganta walwalar mutane- ba tare da ya shafi aikin da suke yi ba.
    • Marubuci, Sofia Bettiza, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 6

Yin aiki kwana biyar a mako, sannan ka huta na kwana biyu - domin wartsakewa kafin ka koma aiki sakayau. Amma me zai faru idan ba ta wannan hanyar aka bi ba?

Wani sabin bincike da aka wallafa a mujallar ɗabi'ar ɗan'adam ta 'Nature Human Behaviour' - mafi giram da aka yi a wannan fanni - ya nuna cwa rage kwanakin aiki zuwa huɗu a mako na matuƙar inganta walwalar mutane.

Masu binciken a jami'ar Boston sun yi nazarin manyan abubuwa huɗu da suka haɗa da gajiya da gamsuwar aiki da lafiyar jiki da ta ƙwaƙwalwa a faɗin kamfanoni 141 a Amurka da Birtaniya da Australiya da Canada da Ireland da kuma New Zealand.

"Mun samu gagarumin ci gaba a jin daɗin ma'aikata,'' kamar yadda jagoran binciken, Wen Fan ya shaida wa BBC.

"Haka kuma kamfanoni sun samu ƙari a abubuwan da suke sarrafawa da kudin shiga. A yanzu musu ya ƙare domin kashi 90 cikin 100 na waɗanda aka gudanar da binciken kansu sun zaɓi ci gaba da aikin kwana hudu a mako.''

Wannan bincike ƙari ne kan wani makamancinsa da aka yi kan alaƙar rage kwanakin aiki da lafiyar mutane da kuma ingancin aiki da rayuwa bayan ritaya.

A baya-bayan nan ne wani bincike ya gano cewa ɗaukar lokuta masu tsawo ana aiki na iya sauya tsarin ƙwaƙwalwa.

To indai akwai amfani ga lafiya - me zai hana mu rungumi tsarin aikin kwana huɗu amako?

Al'adar aikin da ya wuce ƙima

Wata mace na ɗinki

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ƙasar China ce kan gaba a ala'adar yin aiki fiye da ƙima, inda ma'aikata kan yi aiki daga ƙarfe tara na safe zuwa tara na dara, kuma kwana shida a mako.

A Indiya mai bunƙasar fannin fasaha da hada-hadar kuɗi, ma'aikatana fuskantar ƙaruwar matsin lamba don su yi aikim da ƙarin sa'o'i a wajen aiki domin cimma abin da duniya ke buƙata na fasaharta.

''A wurare irin su China da Indiya da Amurka da Birtaniya, ana kallon yin aiki fiye da ƙima a matsayin jarumta,'' in ji Farfesa Fan.

A Japan, rashin biyan kuɗin ƙarin lokaci ba wani baƙon abu ba ne, lamarin da ya sa kalmar mutuwa saboda aiki fiye da kima ta zama ruwan dare a ƙasar: karoshi.

"A japab, aiki tamkar nani nau'in ibada ne, ba sana'a kawai ba,'' in ji Hiroshi Ono, wani ƙwararre kan ayyukan ƙwadago a Japan.

"Mutane kan je wurin aiki da wuri, su kuma kasance a wurin har fiye da lokacin tashi, koda kuwa babu ainihin aikin da suke yi , don kawai su nuna son mayar da hankali ga aiki, kuma hakan abin burgewa ne a gare su."

Hatta hutun haihuwa da ake bai wa iyaye maza ƴan ƙasar ba su fiye amfani da shi ba.

"A tsarin aikin ƙasar, maza kan iya ɗaukar hutu har na tsawon shekara guda, amma ƙalilan ne kawai ke yin hakan - saboda ba sa son abin da zai taƙura wa abokan aikinsu," in ji Ono.

A ƙasar Iceland kusan kashi 90 cikin 100 na ma'aikata a yanzu sun rage tsawon sa'o'in aikinsu ko suna da damar gajarta lokutan aikinsu a mako.

Haka kuma ana ci gaba da gwada hakan a Afirka ta Kudu da Brazil da Faransa da Sifaniya da Jamhuriyar Dominican da Botswana.

A farkon shekarar nan ne, Japan ta fara rage kwanakin aiki zuwa huɗu a mako ga ma'aikatan gwamnati.

A baya-bayan nan ita ma kasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta ƙaddamar da wannan batu ga ma'aikatan gwamnati.

Haka ma daga Oktoban 2025, Koriya ta arewa za ta raba gwada amfani da kwana huɗu da rabi a faɗin kamfanoni 67 a ƙasar.

Aiki ba tare da ya shafi rayuwa ba

Ƴansanda maza biyu da mace guda sanye da tufafin ƴansanda a hoto a wabi wurin shaƙatawa a birnin Golden na jihar Colorado.

Asalin hoton, City of Golden PD

Bayanan hoto, Bayan mayar kwanakin aiki huɗu a mako, da dama cikin ƴansandan Colorado sun ajiye aikinsu

"Tun bayan annobar Covid, mutane da dama ba su koma yadda suek aiki kafin annobar ba,'' a cewar Karen Lowe, jagarar gangamin mayar da ranakun aiki hudu a mako.

Ƙungiyarta na taimaka wa kamfanoni da dama a faɗin duniya gwada aikin kwana huɗu a mako a ƙasashen Brazil da Namibia da Jamus.

Ɗaya daga cikin nasarar da ta yi shi ne a sashen kula da aikin ƴansanda a birnin golden na jihar Colorado, mai ma'aikata 250.

Tun bayan fara amfani da amfani da tsarin aikin kwana huɗu a mako, kuɗaɗare da ake kashe domin tafiyar da rundunar suka ragu da kusan kashi 80 cikin 100.

Wasu ata biyu abokan aiki na murmushi da dariya yayin da suke zaune suna hutawa.

Asalin hoton, Karen Lowe

Bayanan hoto, Karen Lowe (daga hagu) ta ce tsarin aikin kwana huɗu a mako zai rage ayyuka marasa amfani.

Lowe ta ce ɗaya daga cikin abubuwan da mutane ke yaɗawa game da rage kwanakin aiki shi ne yana rage yawan aikin da ake yi.

To amma ta ce sam ba haka lamarin yake ba, hasalima an fi aiki mai inganci a kwana huɗu, a cewarta.

A 2019 kamfanin Microsoft a Japan ya gwana aikin kwana huɗu a mako, kuma ya samu ƙarin sayar da kayyaki da kashi 40 cikin 100 idan aka kwatanta a shekarar da ta gabata.

Kodayake kamfanin bai ci gaba da matakin a matsayin na dindindin ba.

Binciken Fan ya gano cewa ba a samun rage a aikin da ake yi a mako idan aka yi na kwana huɗu, saboda kamfanoni kan rage ɓata lokaci a ayyukan marasa muhimmanci, misalin yawan taron da ba shi da muhimmanci, akan tattauna batun ta waya.

Taimakon lafiyar da za a iya yi

Tawagar ma'akatan, na kusan mutum 45 da karensu na cikin jin daɗi da walwala.

Asalin hoton, Charl Davids

Bayanan hoto, Charl Davids ya ce komawa aikin kwan ahudu a mako ya taimaka wa ma'aikatansa.

Ga Charl Davids, daraktan cibiyar bayar da shawarwari a Jami'ar Stellenbosh a birnin Cape Town, komawa tsarin aikin kwana huɗu a mako ba sauya tsarin aiki kawai yake yi ba, har da inganta lafiya.

Tawagar ma'aikatansa na bayar da shawarwarin kula da ƙwaƙwalwa ga ɗalibai fiye da 30,000.

Afirka ta Kudu na cikin ƙasashen duniya ke mutanenta ke fuskantar damuwar ƙwaƙwalwa.

Tawagar ma'aikatan Charl mai mambobi 56 na da ƙwarewar da suke bai wa mutane shawarwar yadda za su rabu da damuwa da tsoro da razani.

Ta yake shawarar yin aikin kwana huɗu a mako duk kuwa da turjiyar da ya fuskanta daga wasu manyan shugabaninsa, kuma hakan ya yi wa tawagar ma'aikatansa daɗi.

Ba komai ne ke yi wa kowa daidai ba

Duk da alfanun aikin kwana huɗu a mako da ake yi, ba ko'ina ne hakan ke faruwa ba.

"Ya danganta da kamfanin da kake aii da kuma ƙasar da kake zaune, da irin ci gaban da ƙasar ke da shi," in ji Farfesa Wen Fan.

"A nahiyar Afirka mafi yawan ma'aikata a gonaki suke da wuraren haƙar ma'adinai da sauran wuraren da ke saki barkatai,'' in ji Karen Lowe.

Ta ƙara da cewa "a irin waɗannan wurare da wuya a riƙa zancen sassautawa ko rage aiki''.

Ƙananan ayyuka na da wahalar sauya wa fasali, kuma ma'aikata a irin waɗannan wurare sun fi fifita kuɗin da suke samu fiye da tunanin sake fasalin aikinsu, a cewar Lowe.

To amma ana samun sauyi a wasu fannonin.

Binciken Farfesa Fan inciken ya haɗa da kamfanonin gine-gine da na sarrafa kayayyaki da na ayyukan jin ƙai, kuma wasu daga ciki sun bayar da rahoton samun nasara.

Matasa na ƙoƙarin kawo sauyi

Wata matashi mace riƙe da wani allo mai ɗauke da rubutun da ke cewa ''Matasa ba sa son yin aiki kawai don albashi ga ƴanjari hujja da masu mulkin mallak''.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Matasa na ƙoƙarin sake fasalin aiki, suna fifita samun sukuni fiye da albashi a karon farko

Masana sun yi amanna cewa babban abin da zai kawo sauyin zai fito ne daga matasa.

A 2025 wani bincike da aka gudanar a faɗin duniya ya gano cewa masu yin aiki domin sama wa kai sukuni ya zarce masu yi don samun albashi, wani abu da ke da muhimmanci.

A Koriya ta Kudu, matasa da dama sun ce sdun amince a rage albashinsu domin rage musu kwanakin aiki a mako.

A Japan, Hiroshi Ono ya ce tuni an fara samun sauye-sauye.

"Kashi 30 cikin 100 na mazan Japan ayanzu na ɗaukar hutu idan an yi musu haihuwa, amma a baya ba a samu ko da kashi ɗaya,'' in ji shi.

Ya ƙara da cewa ''hakan ya nuna cewa mutane na fifita walwalarsu fiye da kuɗi''.

Karen Lowe ta yarda cewa. "A aron farko, ma'aikata sun fara turjiya. Kuma kasancewarsu matasa, sauyin zai fi samuwa.''