Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko sojojin Venezuela za su iya fito-na-fito da na Amurka?
- Marubuci, Norberto Paredes
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Mundo
- Lokacin karatu: Minti 4
Zuwan katafaren jirgin ruwa na yaƙi mallakar Amurka mai suna Gerald R Ford, tekun da ke kusa da yankin Latin Amurka na ƙara fito da ƙaruwar zaman tankiyar da ke tsakanin Amurkar da ƙasar Venezuela.
Wannan ne lokacin da Amurka ta bayyana a yankin da ƙarfinta tun bayan 1989 lokacin da ta kutsa Panama.
Kamar yadda shekaru 30 da suka gabata aka zargi Manuel Norriego da safarar muggan ƙwaya, yanzu kuma ana zargin shugaban ƙasar ta Venezuela, Nicolas Maduro da irin zarge-zargen da iyalansa suka musanta.
Amurka ba ta fayyace matsayinta ba dangane da aikewa da jirgin yaƙin kusa da ruwan Venezuela.
Amma kuma alamu na nuna kamar Venuzuela ɗin tana shirin ko-ta-kwana.
A makon da ya gabata ne ministan tsaron ƙasar, Vladimir Padrino Lopez ya sanar da ɗaukar manyan matakan soji a ƙasa da ruwa da sama da kuma ƙarfin makamai masu linzami tare da amfani da sojojin sa-kai na farar hula da ke faɗin ƙasar domin tare abin da gwamnatin Maduro ta bayyana da "barazana".
A wani jawabi ta kafar talbijin, Pdrino Lopez ya ce Maduro bai wa rundunar soji kusan 200,000 umarnin zama cikin shiri.
Ana dai yi wa kasancewar jirgin ruwan yaƙin Amurka kallon wani ɗan ba na ɗaura ɗamarar yaƙi ga gungun masu safarar ƙwaya da ke gudanar da al'amuransu a Venezuela - ɗaya daga cikin hare-haren da Amurka ta ƙaddamar dai ya janyo rasa rayuka fiye da 80 da ke cikin jirgin kwale-kwale da jiragen ƙarƙashin ruwa.
Sai dai wasu masu fashin baƙi na yi wa matakin na Amurka kallon wani shirin kifar da gwamnatin Maduro wanda Amurka ke yi wa kallon ba halstacce ba tun bayan zaɓen bara da ƙasar ta yi da masu hamayya ke yi wa kallon mai cike da maguɗi.
Yaya ƙarfin sojin Venezuela yake?
Shin ko sojojin Maduro za su iya fafata wa da sojojin ƙasa mafi ƙarfin soji a duniya?
A watan Satumba, Maduro ya yi iƙrarin cewa mutum fiye da miliyan takwasu sun sanya hannu domin kare Venezuela sannan ya nuna yiwuwar bai wa ƙungiyoyin masu tayar da ƙyar baya miliyan takwas makamai.
Sai dai ƙwararru sun musanta alƙaluman.
"Ba gaskiya ba ne. Ƙididdigar ba ta kai haka ba. Maduron da bai ma iya samun ƙuri'a miliyan huɗu ba a zaɓen bara," in James Story, tsohon jakadan Amurka a Bogota daga 2020 zuwa 2023, ya shaida wa BBC Mundo. " Sannan kuma alƙaluman sojojin da ke barin aikin soja na da yawa."
Wani rahoto da cibiyar nazarin dabaru ta ISS ta ƙiyasta cewa Venezuela na da sojoji 123,000 da kuma masu ɗauke da makamai 220,000 sai kuma sojoji 8,000 da ke jiran ko-ta-kwana.
Anti-aircraft missiles and drones
A ƙarshen watan Oktoba, a tsaka da tankiyar da yake yi da Amurka, Maduro ya sanar da cewa Venezuela ta kakkafa na'urorin ƙirar Rasha da ke hana makamai masu linzami tasiri, a wasu wurare masu muhimmanci.
Venezuela tana kuma da motoci masu sulke ƙirar VN-4 na Chana sannan kuma a ƴan shekarun nan, Venezuela ta zama ƙasar farko a yankin Latin Amurka da ta samu jirage marasa matuƙa da ka iya kai hare-hare waɗanda kuma Nicolas Maduro ya nuna su a 2022.
Venezuela ta samu jiragen ruwa na yaƙi masu gudu da ke iya harba makamai masu linzami ƙirar Peykaap-III ƙirar ƙasar Iran
Sannan rahotanni na nuna cewa Venezuela ta samu na'urorin da ke kama makamai masu linzami daga ƙasar Rasha ƙirar Pantsir-S1 da Buk-M2E wanda kamar yadda wani ɗan majalisar Rasha, Alexi Zhuravlev ya yi iƙrari, an kai su ne ƙasar ta jirgin sama daga Rashar.
Tsarin tsaron sararin samaniyar Venezuela
A daidai lokacin da rahotanni ke cewa ƙara ta'azzara rikicin tsakanin ƙasashen biyu ka iya janyo kai hare-hare zuwa cikin Venezuela, hakan ya janyo hankali ya karkata kan tsarin kariyar sararin samaniyyar Venezuelar.
Sai dai kuma Dr Serbin Pont ya shaida wa BBC cewa mafi yawancin na'urorin tsaron tsofaffi ne da aka yi su tun a shekarun 1960 sannan kuma kodai yanzu haka ba sa aiki ko kuma ba bu wahala fasahar Amurka ta illata su.
Yaƙin sunƙuru
Masu fashin baƙi da dama sun yi amannar cewa Maduro da ƴan kanzaginsa na shirin ƙaddamar da yakin sunƙuru.
A watan Satumba ne ministan cikin gida na ƙasar, Dioadado Cabello ya yi gargaɗin cewa ƙasarsa a shirye take ta shiga "yaƙin na dogon zango".
Kuma jim kaɗan bayan kalaman ministan cikin gidan ne shi da kansa Mista Maduro ya umarci sojojin ƙasar da su horar da masu sakai yadda za su yi amfani da makamai.
Masani mista Story ya yi watsi da tunanin ƴan Venezuela da ke son goyon bayan Maduro a yanayin yaƙi.
"Maduro ba a son shi sosai -sojoji ba sa son shi haka farar hula ma - kuma hakan ne ya sa ba na tunanin mutane za su bi ra'ayinsa su shiga yaƙin sunƙuru."
Duk da cewa gwamnatin Venezuela ta ƙara yawan abubuwan da ke nuna kishiyantar Amurka, kamar yadda Dr Serbin Pont ya ce sojojin ƙasar ba su shirya yaƙi da Amurka ba.