Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Komai nawa ya ƙare saboda tsare ni shekara 11 babu sharia'
Babbar Kotu a Jihar Jigawa ta ba da umarni ga gwamnati da kwamishinan ƴan sandan jihar su nemi afuwa a bainar jama'a ga wani mutum, Mallam Ja'o Sabo kuma su biya shi diyyar N10m saboda tsare shi a gidan yari sama da shekara goma ba tare da shari'a ba.
Lauyan Ja'o Sabo ya shaida wa BBC cewa tun a 2014 ne ƴan sanda suka kama magidancin bisa zargin fashi da makami da haɗa baki don aikata laifi amma ba a iya gurfanar da shi yadda ya kamata a kotu don yi masa shari'a ba.
A nashi ɓangaren Mallam Ja'o Sabo ya zargi jami'an tsaro da muzguna masa tare da tauye masa haƙƙnsa na dan'adam a yayin da suke riƙe da shi.
''Suna tambaya ne wai jiya wasu sun je sun yi fashi a wani wurin, wai ko ban yi ba dole na san waɗanda suka yi, ni kuma na ce babu yadda za a yi in sani babu yadda za a yi a ce duk wanda zai je sata sai na saka masa hannu.'' in ji shi
Ya ƙara da cewa a kan haka aka gurfanar da shi a gaban kotu daga nan kuma daga baya aka miƙa shi gidan yari inda aka haɗa shi da saurin tarin fursunoni da ke jiranm shari'a.
A bara dai, ministan cikin gida na Najeriya, Olubunmi Tunji-Ojo ya ce fiye da rabin ɗaurarru a gidajen yarin da ke faɗin ƙasar kimanin kashi 67% zaman jiran shari'a suke yi, inda aka yi ƙiyasin adadinsu ya kai tsakanin 50,000 and 57,000.
Wani rahoto da aka fitar a shekarar 2025 ya bayyana cewa da yawa cikin waɗanda ake tsare dasu ba da manyan laifuka ake tuhumarsu ba.
Gidajen yarin Najeriya sun yi ƙaurin suna wajen cunkoso da tsare mutane fiye da adadin da za su iya ɗauka inda ake samun kusa fursunoni 80,000 a gidan yari da aka tsara zai ɗauki mutane 50,000.
Ga mutane irinsu Mallam Ja'o Sabo da aka tsare na tsawon lokaci ba tare da shari'a ba, rayuwa a gidan yari na sanya rayukansu cikin babban haɗari sakamakon halin da suke rayuwa a ciki. Mallam Ja'o Sabo ya ce: ''Gidan yarin yadda ka san akurki haka ya ke, masifa daga wannan sai wannan. Ƙuraje, ƙwarƙwata babu abin da babu, cuta dai ga shi nan babu iyaka.''
Baya ga barazana ga lafiyarsu da suke fuskanta a gidajen yari sakamakon mawuyacin halin da suke rayuwa a ciki mafi yawan fursunoni sukan fuskanci ƙalubale bayan sun samu kuɓuta da wannan yanayi sakamkon rashin samun aikin yi.
Kamar yadda ya shidawa BBC, Mallam Ja'o Sabo ya bayyana cewa a halin da ake ciki ba shi da wata sana'a da ya dogara da ita domin ya ingata rayuwarsa.
Rashin aikin yi dai ya zame babban abin da ya ke ci wa mutane da dama ƙwarya a Najeriya.
Masana tattalin arziki na ƙiyasin cewa dole ne ƙasar ta samar da ayyukan yi miliyan 27.3 don ci gaba da daƙile yawan rashin aikin yi a kashi 4.3 cikin 100 daga shekarar 2025 zuwa 2030.
Msanan dai sun buƙaci a bunƙasa shirye-shiryen koyar da sana'o'i a gidajen yari domin a bai wa waɗanda suka fito daga kurkuku damar ci gaba da gudanar da rayuwarsu.
Mutane irin su Mallam Ja'o Sabo dai na fatan ganin an yi wa ɓangaren shari'a garambawul inda za a ƙara hanzarta yadda ake gudanar da shari'a a kotu domin magance matsalar cunkoso a gidajen yarin da ke faɗin ƙasar.