Hotunan yadda Real Madrid ta gabatar da Endrick

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta gabatar da matashin ɗan wasan tawagar Brazil, Endrick a gaban magoya baya a Santiago Bernabeu ranar Asabar.
Shugaba, Florentino Perez ne ya tarbi ɗan wasan a birnin Madrid, daga nan ya je aka auna koshin lafiyarsa, sai ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka shida.

Asalin hoton, Getty Images
Bayan da aka gabatar da ɗan wasan ɗan kasar Brazil, ya kuma gana da ƴan jarida a Santiago Bernabeu.
Endrick Felipe Moreira de Sousa ɗan kasar Brazil, ɗaya ne daga matasan da suke haskakawa a fannin tamaula a duniya a wannan lokacin.

Asalin hoton, Getty Images
Ya lashe lik a Palmeiras, kuma shi ne matashin da ya yi fice a babbar gasar tamaula ta Brazil.
Da yake yana da karancin shekaru, ya samu damar kafa tarihi a fannin tamaula da yawa.
Shi ne na farko da ya buga wa Palmeiras tamaula mai shekara 16 da wata biyu da kwana 15 da cin ƙwallo yana da shekara 16 da wata uku da kwana hudu.
Kuma shi kaɗai ne da ya lashe kofuna a kungiyar da yawa mai karancin shekarun haihuwa.

Asalin hoton, Getty Images
Endrick ya taka rawar gani a 2022 da yin fice a babbar gasar tamaula ta Brazil, wanda ya ci ƙwallo uku ya bayar da ɗaya aka zura a raga a wasa uku, yana da shekara 16.
Ya kuma ɗauki Sao Paulo Junior Cup, wanda shi ne ya lashe ƙyautar fitatcen ɗan wasa a gasar kuma shi ne zakara a fafatawar matasa ƴan kasa da shekara 20 a Brazil da ta ƴan kasa da shekara 17 da cin ƙwallo uku.

Asalin hoton, Getty Images
Ya fara daga makarantar koyon tamaula a Palmeiras tun 2016 lokacin da yake shekara 10, wanda ya ɗauki Paulista Championship ta ƴan kasa da shekara 11 da ta ƴan kasa da shekara 13 da kuma ta ƴan kasa da shekara 15.
Ya fara buga wa tawagar Brazil tamaula a Nuwambar 2023, yana da shekara 17 da haihuwa.

Asalin hoton, Getty Images
Endrick ya cika shekara 18 ranar Lahadi 21 ga watan Yuli, wanda aka haifa ranar 21 ga watan Yulin 2006 a Brazil.
Ana sa ran zai fara buga wa Real Madrid wasanni a kakar 2024/25, wanda za a gabatar da shi a Santiago Bernabeu ranar Asabar 27 ga watan Yuli.











