Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƴanbindiga sun sace mata da ƙananan yara a jihar Zamfara
Al'ummar garin Gidan Zuma na ƙaramar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya sun shaida wa BBC cewa ƴanbindiga sun je bisa mashina kusan 250 inda suka fara kashe mutum biyar a kusa da garin tare da kashe mutum shida a garin Gidan Zuma, da yin garkuwa da mata 20 da kananan yara.
Rahotanni sun ce maharan sun kai hari ne a ranar Asabar da Lahadi, wanda hakan ya jefa al’ummar yankin cikin fargaba ta rashin sanin abin da zai je ya dawo.
Mutanen yankin sun ce suna cikin halin ƙa-ƙa-ni-ka-yi saboda a kowa ne lokaci maharan ka iya sake afka masu, kuma ko da jami'an tsaro suka isa domin kai dauki, maharan sun tafi.
Wani magidanci da ƴanbindigar suka tafi da matarsa da yaron da take goyo ya ce har cikin gida suka shiga suka tasa ta gaba, "Yaro ba ka san halin da yake ciki ba ballantana ita uwarshi ga yanayi na azumi ga zafin rana, shi ne tashin hankalin da muke ciki."
Shi ma wani da aka kashe ɗan uwanshi tilo da ya rage masa a duniya ya bayyana yadda ya ji da lamarin:
"An harbi ɗan'uwana wanda yana cikin masu fita zagayen unguwa cikin dare domin samar da tsaro, kuma kafin in je Allah Ya yi masa cikawa."
BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin rundunar ƴansandan jihar ta Zamfara sai dai kakakin rundunar bai amsa kiran da wakilinmu ya yi masa ba kuma bai bada amsar sakon da ya aika masa ba.
Jihar Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin da matsalar tsaro ta fi kamari a faɗin Najeriya, inda barayin daji ke afka wa garuruwa da kauyuka da kashe mutane da satar wasu domin neman kuɗin fansa, ga kuma sacewa ko kwace amfanin gonar da manoma suka shuka.
Sai dai gwamnatin jihar da ta tarayya da jami'an tsaro na cewa suna bakin kokari domin magance matsalar, a wasu lokutan ma jami'an tsaro kan sanar da nasarar kashe wasu daga cikin 'yan bindigar.
A baya-bayan nan gwamnatin Gwamna Dauda Lawan Dare ta kaddamar da rundunar 'yansakai da ta yi wa lakabi da Askawarawan Zamfara domin taimaka wa jami'an tsaro magance matsalar.