Hindu - An gano gawar yarinya ƴar Falasɗinu da ta tsinci kanta tsakiyar sojin Isra’ila

Hind Rajab ƴar shekara 6 na kan hanyar yin gudun hijira tare da ƴan'uwanta a lokacin da sojojin Isra'ila suka yi ruwan wuta kan motar da suke ciki

Asalin hoton, RAJAB FAMILY

Bayanan hoto, Hind Rajab ƴar shekara 6 na kan hanyar yin gudun hijira tare da ƴan'uwanta a lokacin da sojojin Isra'ila suka yi ruwan wuta kan motar da suke ciki

An gano gawar yarinya ƴar shekara 6, wadda ta ɓace a birnin Gaza cikin watan da ya gabata, tare da gawawwakin sauran ƴan’uwanta da kuma ma’aikatan lafiya biyu da suka yi ƙoƙarin ceto yarinyar.

Hind Rajab, wadda ke kan hanyar yin hijira domin tsere wa luguden wuta, tare da kawunta da sauran ƴan’uwanta huɗu, da alama sun yi gaba da gaba ne da tankokin yaƙin sojojin Isra’ila, waɗanda suka buɗe musu wuta.

Tattaunawar wayar hannu da aka naɗa tsakanin yarinya Hind da tawagar masu kai ɗauki a baya ya nuna cewa Hind ce kaɗai ta rage da sauran rai a lokacin da aka yi wayar, inda ta yi kwanto a tsakiyar gawawwakin ƴan’uwanta da kawunta domin ɓoye wa sojojin Isra’ila.

Roƙon da take ta yi kan a zo a cece ta ya zo ƙarshe ne lokacin da wayar da ake yi da ita ta katse daidai lokacin da ake jin ƙarin amon bindigogi.

Jami’ai masu aikin ceto na ƙungiyar Red Cross ta yankin Falasɗinawa sun samu nasarar isa yankin a ranar Asabar, inda a baya aka rufe a matsayin fagen daga.

Sun gano mota baƙa ƙirar Kia wadda Hind da sauran ƴan’uwanta suke tafiya a ciki - gilasan motar a farfashe, gaban motar ya yi kaca-kaca yayin da ɗaukacin jikin motar ya yi fata-fata da ramukan harsasan bindiga.

An gano motar da Hind take ciki ta yi raga-raga tare da ramuka na harsasai
Bayanan hoto, An gano motar da Hind take ciki ta yi raga-raga tare da ramuka na harsasai

Ɗaya daga cikin masu aikin ceto ya shaida wa manema labaru cewa Hind na cikin gawawwaki shida da aka gani a cikin motar, waɗanda dukkaninsu ke da rauni na bindiga da kuma alamun ruwan makamai.

Mitoci kaɗan daga wurin motar su Hindu akwai wata motar – wadda aka ƙona ta ƙurmus, injin motar na zaune a ƙasa. Ƙungiyar agaji ta Red Crescent ta ce ita ce motar jami’anta da aka tura domin su ɗauko Hind.

Mutanen da ke cikin motar – Yusuf al-Zeino da Ahmed al-Madhoun sun halaka a lokacin da dakarun Isra’ila suka jefa mata bam, kamar yadda ƙungiyar ta bayyana.

A cikin wata sanarwar da ta fitar, ƙungiyar agaji ta Red Crescent ta zargi sojojin Isra’ila da kai wa motar farmaki a daidai lokacin da ta isa wurin a ranar 29 ga watan Janairu.

Sanarwar ta ce “Masu mamaye (Isra’ila) sun kai farmaki kan jami’an Red Crescent duk da cewa ƙungiyar ta samu izinin shiga da motarta zuwa wurin domin ceto yarinya Hind.”

Ƙungiyar ta shaida wa BBC cewa ta kwashe awanni tana tattaunawa da jami’an Isra’ila domin samun izinin tura mota da ma’aikatan lafiya waɗanda za su ɗauko Hind.

Ƙarin labaran da za ku so ku karanta:
An ƙona motar jami'an Red Crescent da suka tafi da nufin ɗauko Hind - ƙurmus
Bayanan hoto, An ƙona motar jami'an Red Crescent da suka tafi da nufin ɗauko Hind - ƙurmus
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A farkon makon nan mai magana da yawun ƙungiyar ta Red Crescent, Nibal Farsakh ya shaida wa BBC cewar “Mun samu izinin yin aikin.”

“Lokacin da jami’anmu suka isa sun tabbatar mana da cewa suna iya hango motar da Hind ke ciki, kuma sun hango yarinyar. Abu na ƙarshe da muka ji shi ne rugugin bindiga.”

Lokacin da aka yaɗa tattaunawar jami’an kai agaji da na yarinya Hind, sai aka riƙa kiraye-kirayen ganin an gudanar da bincike game da abin da ya faru da yarinyar.

Mahaifiyar Hind ta shaida mana cewa, gabanin gano gawar ƴar tata, tana jira ne kawai ta ga dawowar ta “a kowane lokaci, a kowane daƙiƙa.”

A yanzu kuwa tana neman a yi adalci.

Ta ce “Duk wanda ya ji muryata da muryar ƴata lokacin da take roƙon a ceto ta, kuma ya hana a ceto ta, zan tuhume shi a gaban Allah a ranar tashin ƙiyama.”

“Netanyahu da Biden da duk waɗanda suka ƙulla maƙarƙashiya a kanmu, a kan Gaza da mutanenta, ina yin muguwar addu’a gare su daga cikin ƙoƙon zuciyata.”

A asibitin da take zaune tana jiran dawowar ƴarta, har yanzu mahaifiyar Hind, wato Wissam na riƙe da wata ƙaramar jakka mai launin ruwan hoda ta ƴarta. A cikin jakkar wani littafi ne da Hind ke koyon rubutu a cikin shi.

Wissam ta ce “Har iyaye nawa kuke son ku ga sun shiga cikin irin wannan ƙunci? Har yara nawa kuke son ganin an kashe?”

Sau biyu muna tuntuɓar sojojin Isra’ila game da bayani kan ayyukan da suka yi a yankin da aka kashe Hind a wannan ranar, da kuma ɓacewar Hind da motar agaji da aka tura ta ɗauko ta – sun ce mana suna bincike a kai.

A ranar Asabar mun ƙara tuntuɓar sojojin Isra’ila kan martaninsu game da zarge-zargen da ƙungiyar agaji ta Red Crescent ta yi.

Dokokin yaƙi sun ce dole ne a kare ma’aikatan lafiya kuma ba za a kai musu hari ba, kuma dole ne a bai wa mutanen da aka raunata kulawar da suke buƙata ba tare da ɓata lokaci ba.

A baya dai Isra’ila ta zargi Hamas da yin amfani da motocin asibiti wajen safarar makamai da mayaƙa.