NEMA ta yi Gargadin fuskantar ambaliyar ruwa a Najeriya

Asalin hoton, other
Hukumar Bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta yi gargadin samun gagarumar ambaliyar ruwa a fadin kasar, sakamakon shirin Kamaru na sako ruwa daga madatsar Lagdo.
NEMA, ta ce lamarin zai fi shafar garuruwan da ke kusa da kogin Benue da na Niger, don haka ta ba da shawarar a dauki matakan gaggawa don kaucewa tafka asara.
A shekarar da ta gabata ma dai an tafka gagarumar asara da ta hada da ta dukiya da rayukan jama'a sakamakon sako ruwa daga madatsar da Lagdo ta Kamaru.
Dr Mustapha Habeeb, shi ne shugaban hukumar ya shaida wa BBC cewa Mahukunta a Kamaru za su fara sako ruwan Lagdo da kadan-kadan, kuma tuni ya ja hankalin ofisoshin hukumar na jihohin Kogi da Binuwe da kuma Niger wadanda sune suka fi zama cikin hatsari idan aka sako ruwan.
A shekarar 2022, sakin ruwan ya haifar da mummunar ambaliyar ruwa.
Wane mataki NEMA ta dauka tun bayan samun sanarwar daga Kamaru?
Dr Mustapha Habeeb, ya ce '' Na gana da gwamnonin jihohi yayin taron gwamnoni inda na yi musu bayani, bayan wannan na sake zama da gwamnoni a lokacin taron majalisar zartaswa inda na bukaci su kasance cikin shiri tare da daukar matakan da suka hada da kafa hukumar agajin gaggawa a kananan hukumomi da mazabu''.
An shawarci gwamnoni su share magudanun ruwa, tuni wasu gwamnonin suka yi nisa a aikin.
A na ta bangare ma`aikatar harkokin ruwa da tsaftar muhalli ta kasa ta tsoratar game da yadda kogin Benue ya cika ya batse bayan ta shawarci gwamnonin jihohin da suke makwabtaka da kogin na Benue su gaggauta daukar matakai kafin ambaliyar.
Matakan da mazauna yankin za su dauka
A shekarar da ta gabata wata kididdiga da hukumomi suka fitar a Najeriya ta bayyana cewar akalla mutane 1,500 ne suka jikkata yayin da kusan mutane 500 suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan wacce ta raba mutane sama da miliyan daya da muhallansu, bayan sako ruwa daga madatsar Lagdo da ke Kamaru.
Ruwan dai ya fi yin barna a jihohi 11 da suke bakin kogin Benue.













