Waiwaye: Garuruwan da ke cikin haɗarin ambaliya a daminar bana, da zaɓen shugabannin Majalisa
Kamar yadda aka saba, wannan ma mun duba wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya a makon da muke bankwana da shi.
Yankunan da ke cikin haɗarin ambaliyar ruwa a Najeriya a daminar bana

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Tarayya ta fitar da sanarwar hasashen ambaliya a shekara ta 2023, inda ta ce jihohi 14 da al’ummomi 31 za su iya fuskantar ruwan sama kamar da bakin kwarya.
Hakan zai iya haifar da ambaliya daga ranar 4 zuwa 8 ga watan Yuli, a cewar gargaɗin.
Wata sanarwa da ma’aikatar kula da muhalli ta tarayya ta fitar ta lissafa wuraren kamar haka:
A cewar sanarwar, an gano jihohin da al’ummomin da suka hada da:
Filato- Langtang, Shendam
Kano - Sumaila, Tudun Wada
Sokoto - Shagari, Goronyo da Silame
Delta - Okwe
Kaduna - Kachia
Akwa Ibom - Upenekang
Adamawa - Mubi, Demsa, Song, Mayo-Belwa, Jimeta, Yola
Katsina - Katsina, Jibia, Kaita da Bindawa
Kebbi - Wara, Yelwa da Gwandu
Zamfara - Shinkafi, Gummi
Borno - Briyel
Jigawa - Gwaram
Kwara - Jebba
Neja - Mashegu, Kontagora
Wasu na ƙorafi, NNPP na murna da shugabancin Majalisar Najeriya

Asalin hoton, Other
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ra'ayoyi sun sha bamban musamman tsakanin jam'iyyun siyasar Najeriya bayan fitar da manyan jami'an Majalisar Tarayya ta goma.
Awanni bayan sanar da jagororin, manyan jam'iyyun APC da PDP da suka mamaye majalisun guda biyu, sun nuna rashin jin daɗi da sunayen da aka fitar a Majalisar Dattijai da ta Wakilai.
Jam'iyyar APC mai mulki ce ke da kujera takwas na ɓangaren masu rinjaye, inda Sanata Opeyemi Bamidele ya samu matsayin shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai.
Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta tashi da kujera huɗu: shugaban marasa rinjaye a duka majalisun guda biyu da mataimakin shugaban marasa rinjaye a majaisar dattijai, sai kujerar mai tsawatarwa na majalisar wakilai.
LP da NNPP kuma sun raba kujeru guda huɗu na ɓangaren marasa rinjaye. A majalisar dattijai, LP ta samu kujerar mai tsawatarwa, sai mataimakin mai tsawatarwa a majalisar wakilai. Inda NNPP take da kujerar mataimakin shugaban marasa rinjaye, amma a majalisar dattijai ta samu mataimakin mai tsawatarwa.
Sai dai, ba ƙuri'a aka kaɗa kafin fitar da sabbin shugabannin ba a ranar Talata, majalisun tarayyar dai sun ce matsaya ce 'yan majalisun daga rukunonin jam'iyyunsu kawai suka cimma.
Wannan dai wani sabon al'amari ne ga ƙananan jam'iyyun adawa a Najeriya. Wani jigo a jam'iyyar NNPP ya faɗa wa BBC cewa abin da suka samu a shugabancin majalisun biyu "wanda zai je sama ne ya taka leda".
Karanta cikakken labarin a nan:
Ni na kara wa kaina maki a jarrabawar JAMB - Mmesoma

Asalin hoton, Daily Trust
Yarinyar nan da ake zargi da kara wa kanta maki a jarrabawar JAMB ta amince cewa da kanta da sauya sakamakon jarrabawar.
Ejikeme Mmesoma mai shekarar 19, wadda tsohuwar ɗaliba ce a makarantar 'Anglican Girls’ Secondary School' a jihar Anambra, ta bayyana yadda ta kara wa kanta maki a takardar sakamakon jarrabawar.
A 'yan kwanakin nan, batun ya janyo ce-ce-ku-ce, tun bayan da hukumar da ke shirya jarrabawar ta karyata makin da dalibar ta yi ikirarin samu a jarrabawar.
Ita dai hukumar JAMB ta ce dalibar ta samu maki 249, saɓanin maki 362 da take ikirarin samu, to sai dai a lokacin ɗalibar ta kafe cewa sakamakon da take ikirari shi ne na gaskiya.
Lamarin da ya sa gwamnan jihar Anambra Charles Soludo ya kafa wani kwamiti domin gudanar da bincike kan lamarin.
Kwamitin ya gayyaci ɗalibar da shugabar makarantar da kuma jami'an hukumar JAMB domin jin bahasin kowanne ɓangare.
Hukumar ta JAMB ta ce sakamakon da ɗalibar ke ikirarin samu wanda ke dauke da maki 362 sakamako ne na bagi, ba na gaskiya ba.
Haka kuma JAMB din ta bayyana yadda Ejikeme Mmesoma ta yi ta yunkurin neman samakamon jarrabawar tata a shafin hukumar cikin sa'o'i da dama, kuma a duk wadannan lokuta sakamako daya take samu daga hukumar wanda ke nuna cewa ta samau maki 249.
To sai dai Ejikeme Mmesoma ta shaida wa kwamitin cewa ta amince da wanna bayani da hukumar jami'an hukumar ta JAMB suka yi wa kwamitin.
Tana mai cewa da kanta ta kara makin sakamakon jarrabawar tata.
Ta ce ta yi amfani da wayarta wajen sauya sakamakon jarrabawar, kafin ta fitar da takardar sakamakon jarrabawar.
Kwamitin ya yi kokarin gano dalilin ɗalibar na aikata wannan laifi, to sai dai ta ce ba ta da wani kwakkwararn dalili.
Daga ƙarshe kwamitin ya bukaci ɗalibar ta gaggauta neman afuwa bisa wannan laifi da ta aikata, ta hanyar rubuta wasikar neman afuwa ga hukumar JAMB da hukumar Makarantar da ta kammala, sannan zuwa ga gwamnatin jihar Anambar.
Sannan kwamitin ya bukaci dalibar ta je a duba lafiyar kwakwalwarta, tare da yin kira da duka ɗaliban da ke rubuta jarrabawar da su tsaya inda dokokin hukumar ya iyakance musu.
Kotu ta dakatar da hukumar yaƙi da rashawa ta Kano daga kama Ganduje

Asalin hoton, Insied Arewa
Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta bayar da umarnin dakatar da hukumar yaki da rasahawa ta jihar PCACC da hukumar 'yan sanda da jami'an tsaron farin kaya na DSS da jami'an tsaro na Civil Defence daga kama tsohon gwamnan jihar Abdulahi Umar Ganduje.
Kotun ta bayar da umarnin hana waɗannan kama tsohon gwamnan ko iyalansa ko kuma jami'an tsohuwar gwamnatinsa.
Umarnin na zuwa ne bayan da hukumar yaki da rashawa ta jihar ta gayyaci tsohon gwamnan domin amsa wasu tambayoyi kan 'bidiyon dala' da jarida Daliy Najerian ta wallafa a shekarar 2018, wanda ya zargi tsohon gwamnan da karɓar kuɗaɗe daga hannun 'yan kwangila.
A ranar Laraba ne shugaban hukumar karbar korafi da yaki da rashawa ta jihar Muhuyi Magaji Rimingado ya ce bincike ya tabbatar da sahihancin bidiyon.
Yayin yanke hukunci kan ƙarar da Ganduje ya shigar gabansa, mai shari'a A Liman ya bayar da umarnin dakatar da hukumomin ko jami'ansu daga kama tsohon gwamnan, har zuwa lokacin da za a saurari karar ranar 14 ga watan Yuli.
Najeriya za ta rage magungunan da ake shigarwa ƙasar da kashi 20%
Gwamnatin Najeriya ta ce za ta rage shigaR da magunguna cikin ƙasar daga kashi 60 zuwa kashi 40 kawai cikin 100 domin bunkasa harkar sarrafa magunguna a cikin gida.
Mai bai wa shugaban kasa shawara ta musamman kan harkar lafiya, Salma Anas-Ibrahim ce ta bayyana hakan a wani taron ƙarawa juna sani da aka shirya domin karfafa dabarun hadin gwiwa tsakanin Hukumar Lafiya ta Duniya a Abuja.
A cewarta, wannan wani ɓangare ne na burin da Shugaba Bola Tinubu ya sanya gaba da nufin cike giɓin da ake samu a fannin kula da lafiya na ƙasar.
Sauran fannonin da sabuwar gwamnatin za ta fi bai wa fifiko sun haɗar da haɓaka damar samun ayyukan kula da lafiya ga kowa da kowa da shigar da al'umma cikin shirin inshorar lafiya na ƙasa da aƙalla kashi 40% don tabbatar da ganin duk 'yan Najeriya ciki har da rukunin al'umma masu ƙaramin ƙarfi.
INEC za ta gurfanar da waɗanda ake zargi da laifukan zaɓe a kotu

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) a ranar Talata ta ce za ta gurfanar da wasu da ake zargi da aikata laifukan da suka jiɓanci zaben 2023 a gaban kotu.
Hukumar ta ce mutanen da za ta gurfanar kan irin waɗannan laifuka sun kai 215 daga ɓangarori daban-daban na kasar.
Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga daukacin kwamishinonin zabe a babban ofishin hukumar da ke Abuja.
Ya kara da cewa hukumar zabe za ta hada hannu da kungiyar lauyoyin Najeriya NBA wadda a cewarsa a shirye take ta gurfanar da masu laifin a gaban kotu ba tare da an biya komai ba.
“Dole ne mu yarda cewa akwai wasu ƙalubale - wasu na rashin kayan aiki, wasu na rashin isassun ma'aikata. Muna duba bayanan wadanda suka aikata laifuka,” in ji Yakubu.
“Akwai kararraki 215 daga ‘yan sanda kan laifukan zabe, muna aiki tare da NBA don gurfanar da masu laifi. Tuni Hukumar NBA ta gabatar da jerin sunayen lauyoyi 427 wadanda a shirye suke su gurfanar da wadancan kararrakin kyauta.”
Cutar mashaƙo ta kashe mutum ɗaya a Abuja

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Talata, hukumar kula da babban birnin tarayya, Abuja ta sanar da bullar cutar mashaƙo ko kuma diphtheria a wasu sassan birnin.
Jaridar Punch ta ruwaito daraktan sashen kula da lafiyar jama'a a hukumar, Dakta Sadiq Abdulrahman yana sanar da ɓullar cutar.
Abdulrahman ya ce tuni cutar ta kashe wani yaro ɗan shekara hudu, inda ya kara da cewa ɓullar ta tun farko a jihohin Legas da Ondo da kuma Kano a watan Janairu, cutar ta sanya cibiyar yaƙi da cutuka (NCDC) ta Najeriya kai ɗauki a matakin ƙasa gaba ɗaya.
Diphtheria, cuta ce da ke janyo ƙwayoyin cuta masu guba kuma suna sarƙe numfashi, da janyo matsalolin bugun zuciya, har ma suna iya kaiwa ga mutuwa.
Daraktan ya ce an tabbatar da bullar cutar ne bayan gwaje-gwajen da aka yi wa samfuran wadanda ake zargin sun kamu a wani yanki da ke kusa da Dei-Dei.
“Makonni biyu da suka wuce, mun samu bayanai daga wani yanki na birnin Abuja inda aka yi zargin mutum takwas na ɗauke da alamomin cutar kuma hakan ya sa hukumarmu ta dauki samfuran wasu mutane.











