Me ya sa lafiyar hanji ke da amfani kuma ta yaya za ka inganta naka?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Onur Erem
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Bincike ya nuna lafiyar hanji na da alaƙa da abubuwan da suka shafi ma'aunin sinadaran da ake samu a jini da kitse da kuma cutuka da suka shafi ƙwaƙwalwa.
Kamar yadda ilimi ke bunƙasa kan tasirin lafiyar cikinmu, haka ma kan lafiyar hanjinmu.
A shekarar 2021 an yi cinikayyar sinadaran da ke taimaka wa lafiyar hanji na kusan dala biliyan 60, kuma ana sa ran cinikin zai ƙaru da fiye da kashi bakwai a kowace shekara har zuwa 2030, kamar yadda wasu alƙaluma daga cibiyar kasuwanci ta Polaris suka nuna.
Me ya sa lafiyar hanji ke da muhimmanci kuma ta yaya za ka inganta lafiyar naka?
Wanne ne lafiyayyen hanji?
Sakamakon yadda tsarin halittar hanji ke da sarƙaƙiya, gano lafiyayyen hanji ba abu ne mai sauƙi ba, ba kamar sauran sauran sassan jiki ba, kuma babu wata na'ura da ake amfani da ita wajen auna lafiyar hanji.
Hanjinmu cike suke da sinadarai masu tarin yawa, waɗanda idan da za mu saka su a ma'auni za su kai nauyin fiye da kilogiram 1.8.
Akwai ƙwayar cutar ta bacteria biliyan 100 a kowane giram na hanjinmu.
Lafiyayyen hanji na da sinadaran halittu mabambanta, in ji Dakta Katerina Johnson, wadda ta yi bincike kan alaƙar hanji da ƙwaƙwalwa a jami'ar Oxford.
''Ɓangaren ilimin kimiyyar ƙananan ƙwayoyin cuta, fanni ne da ba a yi zurfin bincike a ciki ba'', in ji ta, tana mai cewa don haka ne ''ba mu da cikakken bayanai kan yadda lafiyayyen hanji yake.
Me ya sa lafiyar hanji ke da muhimmanci?

Asalin hoton, Getty Images
Hanji kan shafi “kusan kowane sassa na jiki”, inji Dakta Johnson.
Ƙwaƙwalwa da hanji na da alaƙa mai ƙarfi tsakaninsu ta wata hanya da kimiyance ake kira ''layin hanji da ƙwaƙwalwa''.
Duka biyun kowannensu na da muhimmanci ga kowa - bincike ya tabbatar da cewa aikin ƙwaƙwalwa zai gamu da cikas idan aka samu matsalar ƙarancin ƙwayoyin sinadaran halitta a hanji.
A wasu lokutan akan kira hanji da ƙwaƙwalwa ta biyu, saboda ƙwayar cuta ka iya shafar mu'amalarsu ta hanyar ƙwayoyin halitta na neurons miliyan 100 da ke cikin hanjinmu.
Neurons ƙwayoyin halitta ne da ake samu a cikin ƙwaƙwalwarmu da kuma cibiyar da ke rarraba saƙonnni a cikin jikinmu.

Asalin hoton, Getty Images
Babban aikin hanji shi ne tace abubuwa masu amfani daga cikin abincin da muke ci.
“Ba a rasa ruwa da sinadarai a cikin ba-hayarmu,” in ji Dakta Venkatraman Krishna, ƙwararren likitan hanji a Indiya.
Dakta Megan Rossi, da aka fi sani da likitar hanji a Birtaniya, ta ce rashin samun ingantattun sinadarai a cikin hanjinmu na da alaƙa da cutuka masu tsanani daban-daban fiye da 70, kama daga cutukan da suka shafi zuciya zuwa cutuka masu alaƙa da numfashi da cutuka masu karya garkuwar jiki, da sauransu.
''Kusan kashi 70 na ƙwayoyin halittar da ke bai wa jiki garkuwa na zama ne a cikin hanji, kuma koyaushe suna cikin sadarwa da sashen kula da garkuwar jikinmu'', in ji Dakta Rossi.
Wannan ne ya sa ''mutanen da ke da lafiyayyen hanji, garkuwar jikinsu ke da juriya'', in ji ta.
Ta yaya za ka inganta lafiyar hanjinka?
Bayan wani bincike da aka gudanar a Amurka kan hanji a 2018, masana suka fara bai wa mutane shawara su riƙa cin 'ya'yan itatuwa daban-daban aƙalla 30 a kowane mako domin samun sinadaran da ke taimaka wa lafiyar hanji.
Wannan ba wai kayan marmari ko ganyayyaki kawai ba, har da wasu 'ya'yan cikin kayan marmari da kayan yaji da kuma waɗanda ake ɓarewa.

Asalin hoton, Getty Images
Dakta Rossi ta bayar da shawarar yawaita dafa abincin da ke ƙunshe da kayan ƙanshi da na yaji tare da cin kayan marmari domin inganta lafiyar hanjinmu.
“Shin za mu iya musanya kayan karin kumallonmu ya ƙunshi abubuwan da aka dafa da kayan ƙanshi da ganyayyaki domin inganta sinadaran lafiyar hanjinmu?” in ji ta.
“Shin za ka iya sauya abincin da kake ci mako-mako zuwa waɗannan nau'ikan abincin?”
Abincin da ke ƙunshe da abubuwan da ba sa narkewa wato na fibre, kan taimaka wajen ba-haya da narƙar da abincin da muke ci, kamar yadda hukumar lafiyar Birtaniya ta bayyana, wadda ta bayar da shawara ga manya su riƙa cin giram 30 na abincin da ba sa narkewa a kowace rana.
Su koma cin abincin da aka yi da alƙama irin su biredi da taliya domin samun ƙarin abinci marasa narkewa a jiki.

Asalin hoton, Getty Images
Sauran nau'ikan abinci masu ɗauke da fibre sun haɗa da dankali - wanda ke ɗauke da sinadarin fibre mai yawa a jikin ɓawonsa da wake da sauran kayayyakin da ake zubawa cikin miya, irin su sinadarin kori, har ma da ganyen salat.
Akwai kuma wasu nau'ikan abinci da ke taimaka wa lafiyar 'ya'yan hanji a cikinmu.
Irin waɗannan nau'ika sun haɗa da ayaba, da albasa mai ganye, ga tafarnuwa da kabeji da albasa da tuffa da lemo da sauransu.
Dakta Hanisha Khemani, ƙwararriyar likitan hanji a Pakistan ta ce cin abinci mai ɗauke da sinadaran duka azuzuwan abinci a lokacin da muke tsakanin shekaru 20 zuwa sama na da matuƙar muhimmanci, ga lafiyarmu..
Wane abinci ne ke da illa ga lafiyar hanjinmu?
Abincin da kamfanoni suka kammala sarrafa shi ta hanyar amfani sinadaran taskancewa masu yawa, da barasa da taba na da illa ga lafiyar hanji, in ji Dakta Dr Krishna.
Abincin da aka sarrafa sosai na ɗauke da sinadaran da ko dai su cutar da lafiyar ƙwayar cuta ko kuma su ƙara cutar da ita.

Asalin hoton, Getty Images
Dakta Krishna ta ce akwai buƙatar mutane su kauce wa abincin da ake sayarwa a gefen titi sannan a wanke kayan marmari da ganyayyaki kafin a yi amfani da su domin kauce wa haɗuwa da ƙwayoyin cuta masu hatsarin gaske.
Wani abu shi ma da ke shafar lafiyar hanji shi ne gajiya, wanda ke ƙara sinadarai masu illa ga hanjinmu.
Dakta Johnson ya ce mutanen da suka gaji da yawa ka iya rasa ƙwayoyin halittar da ke inganta lafiyar hanji.

Asalin hoton, Getty Images
Abin da ya kamata ku yi don kauce wa matsalar
"Kuna buƙatar ɗaukar matakan da suka dace, a lokacin da ya dace, don inganta lafiyar hanjinku,'' in ji Dokta Megan Rossi.
A wasu ƙasashe, kamfanoni kan ɗauki nauyin gwaje-gwajen lafiyar hanji, wanda galibi ake yi ta hanyar yin gwaji kan ba-hayar mutane.
Dakta Rossi ya ce waɗannan gwaje-gwajen ba sa bayar da fa'idojin da wasu kamfanoni ke da'awar samu, amma suna iya ba da ɗan haske game da bambance-bambancen da ke tsakanin sinadaran da ke ƙara wa hanji lafiya.
Likitan Burtaniya da mai gabatar da shirye-shiryen TV Dakta Xand ya yarda cewa rashin isassun kuɗi na kawo cikas ga ire-iren waɗanan gwaje-gwaje.
"Za su ba ku shawara, amma hakan ai bai wadatar ba, kana buƙatar samun kuɗin yin gwaje-gwajen," in ji shi.
"Don haka abin da zan ce, shi ne ku adana kuɗinku, kuma idan kuna da matsala da hanjinku, ku yi ƙoƙarin zuwa asibiti domin ganin likita.











