Yadda sojojin Isra'ila suka daure Bafalasdine a gaban mota

Rundunar sojin Isra’ila ta ce dakarunta sun karya ka’ida bayan da suka daure wani ba Falasdine mai rauni a jikinsa suka sanya shi a gaban mota a yayin da suka kai farmaki a Jenin.

Dakarun kasar sun tabbatar da afkuwar lamarin da aka dauki faifan bidiyon lamarin aka yada a kafar sada zumunta.

Cikin wata sanarwar rundunar sojin ta ce an raunata mutumin ne a yayin da ake musayar wuta inda aka zarge shi.

Iyalan mutumin sun ce sun bukaci a kawo musu daukin motar daukar marassa lafiya a nan ne sojojin na Isra’ila suka dauke shi tare da daure shi a gaban motarsu suka rinka tafiya.

Daga nan an mika mutumin zuwa hannun kungiyar agaji ta Red Crescent don ayi masa maganai.

Tuni rundunar ta ce zata gudanar da bincike kan lamarin.

Ganau sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa mutumin sunansa Mujahed Azmi.

Sojojin Isra’ilan da suka aikata wannan lamari sun ce a lokacin da suka kai farmaki sun akam wani da suke zargi dan tayar da kayar baya ne a yankin Wadi Burqin, a nan ne aka bude musu wuta su kuma suka mayar da martani.

A yayin musayar wutar ne suka kama mutumin da suke zargin na cikin masu tayar da kayar bayan.

Ana dai yawan samun tashe tashen hankula a Gabar Yamma da kogin Jordan tun bayan da aka fara yakin Gaza wanda kungiyar Hamas ta fara a watan Oktoba.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla an kashe Falasdinawa mambobin kungiyar Hamas din 480 a Gabar Yamma da Kogin Jordan.

Kazalika an kashe Isra’ilawa 10 ciki har da sojoji shida a wajen.