'Dariyar yarana tamkar azabtarwa ce gare ni'

Karen
    • Marubuci, By Katie Walderman & Monica Rimmer
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC North West Tonight

Karen Cook ta shafe wata goma sha tara tana rayuwa da wata irin larura mai muni da ba kasafai ake samunta ba inda duk wani sauti ke haifar mata da matsanancin zafi.

"Wani abu mai faranta rai kamar dariyar 'ya'yana, jin muryoyinsu - kamar azabtarwa ne a gare ni," kamar yadda ta faɗa wa BBC.

Matar mai shekara 49 ba ta iya jure ƙara ko sauti, wata larura da ke nufin tana tilasta wa kan yin nesa da mai gidanta da 'ya'yanta maza.

"Sauti na ko ina - kamar iska ce, ba ka iya guje mata," in ji Karen, daga Southport, Merseyside.

Ƙara kamar iskar da ke kaɗa ganyen bishiya ko motoci da ke wucewa ta gidanta na iya sa wa Karen matsanancin ciwo.

Gargaɗi: Wasu masu karatu na iya ganin abin tada hankali a labarin

Yanayin ya yi tsanani sosai da a ranar kirsimeti, ta keɓe kanta a wani ɗaki tana kallo yayin da yaranta maza masu shekara bakwai da 11, suke buɗe kyaututtukan da aka basu.

Karen ba ta kai ga samun maganin da zai sauƙaƙa mata ciwon da larurar ke sa mata wanda ke faruwa saboda ƙara na yau da kullum da kuma "tinnitus" - saututtukan da take ji a kunnenta.

Ta ce larurar ta "hyperacusis" ta same ta ne baga-tatan a 2022 kuma da sannu tana yin muni.

Duk da cewa larurar na iya faruwa saboda tsoron sauti, bincike ya nuna wasu mutane na nuna wasu ɗabi'u sakamakon fama da larurar.

Mece ce larurar rashin jure sauti kuma ta ya ta banbanta da "tinnitus"?

Akwai ire-iren larurar "hyperacusis" da suka bambanta.

Shafin intanet na NHS ya ce "kana iya fama da larurar rashin jure sauti idan sautukan yau da kullum suka zarce ƙarar da saba da ita. Yana iya yin zafi.

"Kana iya samun damuwa saboda ƙarar tsaba da haushin kare da ƙarar injin mota da sautin mutum yana tauna da injin kwashe dauɗa."

"Tinnitus" na nufin jin saututtuka a kunnen mutum.

Karen watches her children open presents

Asalin hoton, Karen Cook

Bayanan hoto, Karen ba ta iya zama tare da yaranta ba a ranar kirsimeti

A yanzu Karen tana sa soson toshe kunnuwanta ko da tana gida ita kaɗai kuma hanya tilo ta take iya isar da saƙo shi ne ta hanyar yin raɗa ko kuma rubutu.

"Gidana gidan yari ne," in ji ta. "Ƙara na mayar da ni fursuna."

Da take bayyana irin zafin da take ji, Karen ta ce: "Kamar mutum ya zuba min garwashin wuta sannan kaina yana ciwo, ko ina a kaina yana zafi, musamman bayan idanuna.

"Kamar ciwon kan ɓarin guda - kamar za ka buɗe kanka domin rage zafin."

Da aka tambaye tasirin da larurar take da shi kan rayuwarta, ido cike da ƙwalla ta ce abin ya yi mata illa sosai.

"Na yi kewar zama uwa, na yi kewar ragwabniyarsu idan sun koma gida daga makaranta.

"Na yi kewar rayuwa, na zauna ina kallon su ta taga suna buɗe kyaututtukan kirsimeti, saboda ƙarar ta yi min yawa na kasance da su a ɗaki, suna zuwa ta wurin taga don su nuna mani.

Karen Cook

Asalin hoton, Karen Cook

Bayanan hoto, Mai gidan Karen, Nick ya ce yana rasa "babbar ƙawarsa"

Karen ta ce sau da yawa ba ta shiga al'amuran rayuwa.

"Ina kewar sauraron waƙa da kallon talabijin ko fim da hira da ƙawayena a waya," in ji ta.

"Ina kewar sanya kaya masu kyau da yin kwalliya da fita shaƙatawa da mijina, Nick."

Karen ta ce a baya "ta kasance mai matuƙar hidima" kuma tana son yn balaguro don hutu.

"A koyaushe ina tafiya," in ji ta. "A zahiri rayuwata ta tsaya."

Nick ya ce yana rasa "abokiyarsa" na fiye da shekara 20.

"Rayuwa ta kasance abin sha’awa," in ji shi. "Ba sai mun tsara komai ba, kawai za mu fita ne kuma duk inda muka sami kan mu daidai ne. Babu irin balaguron da ba mu yi- mun sayi babbar mota a lokacin cutar korona - muna kuma tafiya da ƙafa da zuwa kallon wasannin ƙwallon ƙafa,muna amfani da dalilai daban-daban domin mu yi balaguro."

Ya kara da cewa "duk abin" da suka sani na rayuwarsu na baya ya canza.

Karen Cook and her family

Asalin hoton, Karen Cook

Bayanan hoto, Karen ta ce "ta kuduri aniyar" neman sauki

Karen ta kwashe shekara 25 a matsayin ma'aikaciyar jirgin sama na, sana'ar da ta ce "ba aiki ne kawai ba, wani muhimmin bangare ne na rayuwata".

A nan ne kuma ta hadu da Nick.

Akasarin yanayin rayuwarsu ya yi matuƙar canzawa.

“Kowace rana iri daya ce. in ji Karen

“Gaskiya da ban haihu ba, da na hakura.

"Amma za mu yi matuƙar ƙoƙari don nemo ko ma waye da zai iya taimakawa."

Ken Devore
Bayanan hoto, Ken Devore ya ce abubuwa kamar su bukukuwan aure da tafiye-tafiye da zuwa kallon fina-finai da wasannin kaɗe-kaɗe na iya zama masa kalubale sosai
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ken Devore ya kwashe shekara 30 yana fuskantar irin wannan ƙalubalen kuma ya ce wasu mutane na iya samun sauƙi bayan wani lokaci.

Mista Devore, wanda mamba ne a ƙungiyar bayar da agaji ta Amurka, Hyperacusis Research, ya ƙara da cewa: “A gaskiya babu magani.

"A gani na, samun lokacin kaɗaici da yanayi maras hayaniya da kuma guje wa duk wani abu da zai kawo akasin haka shine muhimmin matakin lallaɓa wannan lamarin, kuma hakan zai tabbtar da cewa abin bai ƙara taɓarɓarewa ba."

Ga wasu marasa lafiya, hukumar NHS ta kan ba da shawarar cewa su fara sauraron amon sauti a hankali, wanda zai taimka musu wurin sabawa da hayaniya.

Amma hakan bai yi wa Karen aiki ba.

Ta gwada magunguna daban-daban da hanyoyin kwantar da hankali, amma babu abin da ya taimaka.

Duk da haka, Karen ta ce ta "ƙuduri aniyar" neman magani saboda 'ya'yanta maza, waɗanda sukan faɗawa mutane cewa kunnuwan mahaifiyarsu ba su ƙarasa girma ba .

"Wata rana za a iya samun magani kuma na yi wa kaina alƙawari zan yi iyakacin ƙoƙari na wajen ganin na sami sauƙi."