Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa har yanzu Tinubu bai naɗa ministoci ba?
- Marubuci, Mukhtari Adamu Bawa & Yetunde Olugbenga
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Broadcast Journalist
Kwana arba'in da huɗu tun bayan rantsar da shi a matsayin shugaban Najeriya, ƙasa mafi girman tattalin arziƙi a Afirka, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da tafiyar da gwamnatinsa ba tare da muhimman ministoci ba.
'Yan Najeriya na jira cike da ɗoki su san irin mutanen da za su taimaka wa sabon shugaban ƙasar da shawarwari da ƙulla al'amuran aiki da saita alƙiblar manufar gwamnatinsa ta “sabunta kyakkyawan fata”.
Nau'in mutanen da zai naɗa ministoci, mai yiwuwa yana iya nuna ko Tinubu ya iya darje zaɓi, da kuma ƙarfi ko raunin shirin sabuwar gwamnatin na tunkarar ɗumbin ƙalubalen da ta yi alƙawarin magancewa 'yan ƙasar.
Wannan dogon jira ya kai ga har wasu sun wallafa jerin sunayen ministoci na jabu, suna kuma ta yayatawa a shafukan sada zumunta.
Muhammadu Buhari dai, shugaban da ya gabaci Tinubu, sai da ya shafe wata shida kafin ya ƙaddamar da majalisar ministocinsa.
Yayin da ake ta wannan nuna damuwa da zaƙuwa, Dele Alake, mai magana da yawun shugaba Tinubu, a lokacin wani taron manema labarai a fadar shugaban ƙasa farkon wannan mako, ya yi watsi da jerin sunayen da ya ce duk ƙirƙirar su ake yi kuma ta yaɗawa a shafukan sada zumunta.
“Babu ƙamshin gaskiya a duk waɗannan sunaye. wannan batu, shawara ce shugaban ƙasa, shi kaɗai ya fitar da sunayen ministocinsa,” kamar yadda Alake ya tabbatar.
Tuni dai Majalisar Dokoki ta gyara tsarin mulki, inda aka wajabta wa shugaban ƙasa naɗa ministocinsa a cikin kwana 60, bayan an rantsar da shi a ofis, sannan ya aika wa 'yan majalisar don su amince.
Raɗe-raɗin da 'yan Najeriya ke yi bai tsaya a kan sunayen da suke jin sun cancanci zama ministocin Tinubu ba, ana ma tattaunawa a kan nagarta da alaƙa da ƙwarewar irin mutanen da suke sa ran ganin shugaban ya naɗa a gwamnatinsa.
Wani ɗan Najeriya, Rotimi TC ya wallafa a shafinsa na Tuwita cewa zai so ganin sabbin fuskoki a matsayin ministocin Tinubu, maimakon 'yan siyasar da suka daɗe ana damawa da su.
Shi kuma Wakili Faruƙ Bello, yana cewa kamar yadda wata majiya ta ambata majalisar ministocin Tinubu za ta kasance babba, ƙunshe da ministoci da masu ba da shawara na musamman.
Kuma a cewarsa, mataimakan na musamman za su riƙa ba da gudunmawa wajen tattauna al'amura a tarukan Majalisar Zartarwa ta Tarayya, saɓanin abin da aka saba gani a baya.
Shi kuwa wani mai suna Otumba, shaguɓe ya yi wa shugaban Najeriyar a kan abin da ya kira ɗumbin ƙwarewar shugabancin da ya nuna wajen cimma nasarori cikin 'yan kwanaki na mulkinsa tun ma kafin ya naɗa ministoci.
"Dala ɗaya = N800", ya rubuta.
Naɗa majalisar ministoci a Najeriya, al'amari ne mai sarƙaƙiya, da ke neman tabbatar da daidaito.
Jazaman ne shugaban ƙasa ya yi nazari cikin tsanaki a kan buƙatar daidaito a tsakanin ƙabilu da mabiya addinai daban-daban a ƙasar, wajen naɗa ministoci. Sai ya haɗa batun ƙwarewa da cancanta ga buƙatar biyan abokan siyasa da magoya bayan da suka wahalta wa takararsa.
Shugaban dai ya nuna wasu alamomi na cewa mai yiwuwa zai yi aiki da 'yan adawa ta hanyar kafa gwamnati bisa muradin haɗa kan ƙasa.
Wani muhimmin al'amari kuma shi ne buƙatar tabbatar da ganin kowacce, cikin jihohin Najeriya 36, sun samu wakilci a majalisar ministocin.
Wani masanin kimiyyar siyasa a Jami'ar Abuja, Dr. Abubakar Kari a zantawa da BBC ya ce fitar da jerin sunayen na iya zama wani babban zakaran gwajin dafi na farko ga Shugaba Tinubu da kuma jam'iyyarsa ta APC.
“Manuniya ce ta irin wahala da sarƙaƙiyar da ke cikin wannan aiki, sannan ana iya kallon shugaban a matsayin wanda tamkar ya ɗauko salon magabacinsa wato Buhari,” in ji Kari.
A cewarsa, matuƙar jinkirin ya ci gaba, yana iya shafar ƙoƙarin fitarwa da aiwatar da manufofin gwamnatin Tinubu.
Tinubu da tsoffin shugabanni
Masharhanta da yawa na rubutu a dandali iri daban-daban game da lokacin da tsoffin shugabanni a Najeriya suka ɗauka kafin naɗa ministocinsu tun bayan komawar ƙasar kan tsarin dimokraɗiyya a 1999.
A cewar wata jaridar intanet, The Cable - tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ne ya fi naɗa ministocinsa cikin sauri idan aka kwatanta da sauran takwarorinsa.
- Muhammadu Buhari 2015 – 2023
Shugaban ƙasa na baya-bayan nan, Muhammadu Buhari ya shafe kimanin wata shida kafin ya kafa majalisar ministoci a wa'adinsa na farko cikin 2015.
Amma dai lokacin da ya ɗauka bai kai haka ba a 2019 sa'ar da ya zo sake naɗa mafi yawan ministocin da ya yi aiki da su a wa'adin farko, bayan ya ci zaɓe a karo biyu.
An riƙa yi masa laƙabi da "Baba Go-slow" saboda tsawon lokacin da yake kwashewa kafin ya yanke shawara ko ya yi wasu naɗe-naɗe a gwamnatinsa.
- Goodluck Jonathan 2010 - 2015
Shugaba Goodluck Jonathan wanda ya mulki Najeriya daga shekara ta 2010 zuwa 2015 ya gabatar da sunayen ministocinsa ga majalisar dokoki ta tarayya a cikin kwana talatin bayan rantsar da shi a kan karagar mulki cikin shekara ta 2011.
- Umar Musa ‘Yar’adua 2007 - 2010
Alhaji Amaru Musa ‘Yar’adua ya ɗauki lokaci mai tsawo idan aka kwatanta da shugaban da ya gabace shi, kafin naɗa ministocinsa a shekara ta 2007.
Bayanai sun nuna cewa ya kai sunayen ministocin da ya yi ƙudurin naɗawa ga 'yan majalisa kwana 59, bayan rantsar da shi a kan mulki.
- Olusegun Obasanjo 1999 - 2007
Shugaba Olusegun Obasanjo ga alama shi ne ya yi fintikau a tsakanin duk shugabannin da ke cikin wannan rukuni.
A cikin kwana shida kacal, ya iya sanar da sunayen ministocinsa bayan ya karɓi rantsuwar kama aiki ranar 29 ga watan Mayun 1999. Amma kuma a karo na biyu, sai da ya ɗan yi jan ƙafa da (ƙarin kwana 19) kafin naɗa ministocin da ya yi aiki da su a wa'adin da ya fara daga shekara ta 2003.
Wane ne ya cancanci zama minista a Najeriya?
Da yake zantawa da BBC, wani lauya masanin tsarin mulkin Najeriya, Jiti Ogunye ya bayyana cewa shugaban tarayyar Najeriya shi ne jagoran ɓangaren zartarwa kuma tsarin mulki ya ba shi ƙarfin iko na ya zaɓo ministocin da za su yi da shi a wannan ɓangare na zartarwa.
Sai dai ya nunar da cewa sashe na 147 na tsarin mulkin Najeriya da ya bai wa shugaban wannan iko ya kuma taƙaita ikon nasa a wani ƙaramin sashe da ya zo daga baya, inda ya zayyana buƙatu da abubuwan da ake la'akari da su kafin naɗa wani mutum minista.
“Sashe na 147 ƙaramin sashe na 5 ya ce: “Babu mutumin da za a naɗa minista har sai ya cika ƙa'idar tsayawa takarar ɗan Majalisar Dokoki ta Ƙasa musamman dai Majalisar Wakilai.”
Waɗanne ne matakan cancantar zama minista?
- Sai mutum ya zama ɗan ƙasa a Najeriya.
- Sai mutum ya kai shekara 30.
- Matsayin ilmin da ake buƙata shi ne Takardar Shaidar Halartar Makaranta ko makamanciyarta kamar dai ofishin shugaban ƙasa.
- Sai mutum ya zama ɗan wata jam'iyyar siyasa kuma jazaman ne sai jam'iyyar ta ɗauki nauyinsa.
Abubuwan da ke rushe cancantar zama minista
Game da abubuwan da ke janyo rashin cancantar zama minista kuma, lauya Ogunye ya ce mutumin da aka ba da sunansa “kada ya kasance wanda jarinsa ya karye.
Jazaman, ba zai kasance ɗaurarre da ke zaman gidan yari ba (kuma idan tsohon ɗaurarre ne bayan kotu ta same shi da laifi, sai ya kasance tsawon sama da shekara 10).
Ba zai kasance mai taɓin hankali ba.
Ba zai kasance ma'aikacin gwamnati ba (sai dai fa idan ya yi ritaya wata uku kafin a naɗa shi).”
Ya kuma ce akasari, tsari mulki ya ce wajibi ne shugaban ƙasa ya naɗa aƙalla minista ɗaya daga kowacce jiha, kuma ya kasance ɗan wata ƙabila a wannan jiha, kamar yadda sashe na 147 ƙaramin sashe na 3 ya ce.
Sai dai, bisa raɗe-raɗi da batutuwan da ake nunarwa yayin da 'yan Najeriya ke ci gaba da jiran sunayen ministocin, Barista Ogunye na da ra'ayin cewa shugaba Tinubu na iya zuwa ya naɗa 'yan jam'iyyar adawa ko wata jam'iyyar.
Ko kuma ya zaɓo ƙwararru a wani fanni da ba su da alaƙa da wata jam'iyyar siyasa kamar yadda doka ta ce, amma saboda yana jin za su iya yin aikin fiye da wasu, idan wani ɗan ƙasa ya so, yana iya bijiro da wannan batu a kan shugaban ƙasar ta hanyar garzaya wa gaban kotu don neman a yi masa fashin baƙin tsarin mulki.