Saran macizai na karuwa saboda ambaliyar ruwa a Najeriya

Asalin hoton, PRATIBHA WALUNJ
Hukumomi a Najeriya na ci gaba da jan hankali game da matsalolin da kan faru, bayan gagarumar ambaliyar ruwan da aka yi fama da ita a sassan kasar.
Sun ce a baya-bayan nan, an samu karuwar saran macizai a wasu sassa da aka yi ambaliyar ruwan sama na damunar da ta wuce.
Dr. Nasir Sani Gwarzo, babban sakatare ne a ma'aikatar jin kai ta tarayyar Najeriya, ya shaida wa BBC cewa yadda mutane ke gudu suna neman mafaka ko tudun-mun-tsira saboda ambaliyar ruwa, haka ma dabbobi da kwari da ma dukkan wani abu mai rai dake cikin kasa ke yi.
Ya ce su ma macizai haka suke neman inda za su fake don haka duk inda aka samu ambaliyar ruwa to dole a samu karuwar saran macizai musamman idan garin mai macizai ne da yawa.
Dr Gwarzo ya ce “Bayan karuwar saran macizai, abin da zai biyo baya shi ne barkewar annoba, kamar su kwalara da zazzabin tepot da ma dai sauran cutuka.”
Babban sakataren ya ce kawo yanzu kusan yawancin garuruwan da aka samu ambaliyar ruwa su aiko wa da ma’aikatarsu karuwar saran macizai.
Ya ce “Macizan da ake samu suna saran mutane kuwa har da masu guba a tare da su da su mesa da ma wadanda ba su da wata guba a tare da su.”
Dr Sani Gwarzo ya ce saboda karuwar saran macizan ma’aikatarsu ke kira ga gwamnati da ma’aikatan kiwon lafiya a wadannan garuruwa, su gaggauta tanadar maganin saran maciji, da kuma kaddamar da wani shiri na fadakar da mutanen garuruwan da suka fuskanci ambaliyar ruwa a kan su rinka tafasa ruwan kogin garinsu kafin amfani da shi.
Kamar kowacce shekara ana fuskantar ambaliyar ruwa a Najeriya, amma a 2022, lamarin ya munana domin ambaliya ta shafi jihohi da dama na kasar inda aka samu asarar rayuwa da dukiya da dabbobi da kuma ta amfanin gona.











