'Muna maraba da kowa amma kada a karya dokokin addini da al'adunmu'

Qatar 2022

Asalin hoton, Getty Images

Yayin da ake fara gasar ƙwallon ƙafa ta duniya a Qatar, abin da aka fi mayar da hankali a kai shi ne batun haƙƙin bil'adama. Wasu ƴan ƙasar biyu sun faɗa wa BBC yadda tsauraran dokoki da al'adun ƙasar suka shafi rayuwarsu.

Aziz na ta zirga-zirga a tsorace yayin da muke tattaunawa ta intanet. Duk da yana son ya saki jiki ya yi magana amma a bayyane take cewar sai ya jajirce sosai, sai dai ya kasa skin jiki har zuwa ƙarshen tattaunawar tamu.

"Ba na son zaman da nake yi a ƙasata ya zama tamkar haramtacce." ya faɗa a cikin sanyayyar murya, daga Doha, babban birnin Qatar. "Zan so na ga sauye-sauye da za su ba ni damar zama ɗan luwaɗi ba tare da tsoron cewa za a kashe ni ba."

Aziz ya ce a kodayaushe yana a tsorace, yana gudun ya faɗi wani abu da zai sa a gane cewa da alama shi ɗan luwaɗi ne, wani abu da zai sa a kama shi ko kuma a ci zarafin shi.

"Banbanci kasancewarka a Qatar da kuma kasancewa a wata ƙasar ta daban shi ne, a ƙasashen ƙetare doka za ta kare ka," in ji shi. "Idan wani ya kai maka hari za ka iya zuwa ƴan sanda, kuma doka za ta kare ka.

Amma a nan idan wani zai faru da ni, to idan na kai kaina wurin ƴan sanda tamkar na sanya kaina cikin haɗari ne."

A rahoton da ta fitar a watan Oktoba, ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Human Rights Watch ta ce jami'an tsaro na tsare masu alaƙa ta jinsi ɗaya babu gaira ba dalili haka nan ana cin zarafin su.

Sai dai buga gasar kofin duniya a Qatar ya sanya kafafen yaɗa labaru na ƙasashen yamma yin bincike kan haƙƙin ƴan luwaɗi a Qatar. Yayin da hakan ke fito da matsalolin da ake fuskanta, Azizi ya ce lamarin na ƙara jefa mutane cikin haɗari.

Ya ce "Yanzu ina ganin mutane da yawa a nan suna sukar masu alaƙar jinsi guda, suna cewa sun tsane mu kuma ya saɓa wa addini.

Yana ganin kamar tattauna batun a ƙasashen ƙetare na masu illa. "Suna tambaya 'shin za mu iya zuwa Qatar mu yi rayuwarmu lafiya ba tare da an ɗaure mu ko an hukunta mu da dokokin Qatar ba?' amma ba su tunanin mutane irin mu, da kuma haɗarin waɗannan dokoki a kanmu."

Hukumomin Qatar dai na ta nanata cewar masoya ƙwallon ƙafa za su iya zuwa domin wannan gasa, amma sun ce ya kamata baƙi su girmama al'adar al'umma. Aziz na tsoron cewar samun nasarar gasar cin kofin da zai sanya da wuya Qatar ta sauya. Kuma yana jin tsoron abin da zai biyo baya a watanni masu zuwa.

Zainab amma ba sunanta ne na gaskiya ba

A Birtaniya mun tattauna da Zainab, wannan ba shi ne sunanta na gaskiya ba. Duk da cewa tana Birtaniya amma tana jin tsoron abin da zai faru ga iyalanta a can Qatar idan aka gane ta.

Ta ce tsauraran dokokin Qatar sun yi illa ga lafiyar hankalinta, ta yadda ta yi tunanin kashe kanta.

Ta ce yadda maza ke sanya wa mata ido a Qatar yana sanyawa mata su ji tamkar su yara ne a tsawon rayuwarsu.

Ta ce "dole ne ka samu rubutaccen izini daga namiji mai kula da kai, yawanci mahaifinka, kafin ka ɗauki duk wani mataki na rayuwarka, in mahaifinka baya nan dole ka nemi izinin kawunka ko kakanka."

"Idan har ba ka samu izini ba, to ba za ka iya aiwatar da komai ba, koda kuwa shiga jami'a ne ko karatu a ƙasar waje, ko tafiye-tafiye, ko yin aure. ko kuma rabuwar aure."

Amma ta ce wasu matan da iyayensu ba su da tsattsauran ra'ayi za su iya cewa abin ba haka yake ba.

Doha

Asalin hoton, Getty Images

Zainab ta ce tsarin ya sanya mata suna fuskantar danniya a hannun iyalai masu tsattsauran ra'ayi. Ta ce "sun yi amannar cewa batun haƙƙin mata wata maƙarƙashiya ce ta ƙasashen turai, kuma hakan zai ci karo da tanade-tanaden addini da al'ada."

Moselle, daliba a Qatar

Masu shirya gasar ƙwallon ƙafa da Qatar za ta karɓi baƙunci sun ce ana sukar ƙasar ce ba tare da wani hujja ba.

Wata ɗaliba a Doha, Moselle, ta ƙara tabbatar da wannan batu. Ta ce "Ba mu buƙatar hukumomin yamma su zo nan su rinƙa faɗa mana abubuwan da za mu yi ko waɗanda ba su kamata mu yi ba,"

"Kasarmu ce. Muna da damar tafiyar da ƙasarmu daidai da tunaninmu, ba daidai nasu muradin ba."

To amma ana sanya ido sosai kan ƴan Qatar masu sukar manufofin al'ummar ƙasar. Kamar yadda muka shaida cewar ana yi wa duk wanda ya soki lamirin ƙasar barzana.

Waɗanda muka tattauna da su ba wai suna kokawa ne kan banbance-banbance na al'ada, kamar shan barasa da sumba a bainar jama'a ba ne, suna magana ne a kan haƙƙoƙin bil'adama.