'Yar Afirka ta farko da za ta yi alkalancin wasa a gasar cin Kofin Duniya a Qatar
'Yar Afirka ta farko da za ta yi alkalancin wasa a gasar cin Kofin Duniya a Qatar
Sauran kwanaki kadan a soma gasar cin Kofin Duniya a kasar Qatar kuma tuni ake shirin kafa tarihi, saboda, a karon farko, za a samu mata da za su yi alkalancin wasa.
Daya daga cikinsu ita ce Salima Mukansanga daga kasar Rwanda. Wakilin BBC Celestine Karoney ya tattauna da ita lokacin atisaye gabanin tafiyarta Qatar.