Me ya sa wasu ke kokawa da ɗaukar baƙuncin kofin duniya na Qatar?

..

Asalin hoton, Getty Images

Masoya ƙwallon ƙafa miliyan ɗaya da rabi ne ake sa ran za su ziyarci Qatar domin kallon wasannin gasar ƙwallon ƙafa ta duniya da za a fara a ranar 20 ga watan Nuwamba.

Sai dai ƙasar ta yankin Gulf, wadda ke bin tsari na Musulunci sau-da-ƙafa na shan suka kan matsayarta game da alaƙar soyayya ta mutane masu jinsi guda.

Mece ce matsayar Qatar kan haƙƙin ƴan luwaɗi?

Luwaɗi da maɗigo haramun ne a Qatar kasancewar abubuwa ne da shari'ar musulunci ba ta amince da su ba.

Ana yanke wa waɗanda aka kama da waɗannan laifuka hukuncin ɗauri na shekara bakwai ko kuma na kisa.

Masu shirya gasar cin kofin duniya da Qatar za ta karɓi baƙunci sun ce 'ana maraba da kowa' domin kallon wasannin da za a buga, kuma ba za a ci zarafin kowa ba.

Sai dai, shugaban shirya karɓar baƙuncin na Qatar, Nasser al Khater ya ce gwamnatin ƙasar ba za ta sauya dokokinta da suka shafi auren jinsi guda ba kuma ya buƙaci waɗanda za su je ƙasar su "martaba al'adun al'ummar ƙasar".

Ya ce ayyukan baɗala a bainar jama'a, tsakanin mutane masu jinsi guda ko ma waɗanda ba jinsi guda ba lamari ne da ba za a lamunta ba.

A kwanan nan ne ƙungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta fitar da wani rahoto inda ta ce jami'an tsaron Qaatar na kama ƴan luwaɗi, da maɗigo, da masu sauya jinsinsu a ƙasar, inda a wasu lokuta ake tursasa masu ɗaukan darussan sauya hali.

Gwamnatin Qatar ta ce akwai zarge-zarge na ƙarya a cikin rahoton.

Rayuwa a Qatar

Yadda mutane ke nuna adawa

Tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙatar ta wallafa wani bidiyo tana neman Qatar ta yi watsi da dokokinta na alaƙar soyayya ta masu jinsi guda.

A cikin bidiyon, ƴan ƙwallon sun soki masu ɗaukar ma'aikata na Qatar kan zargin takura wa baƙi ma'aikata kimanin 30,000 waɗanda suke aikin gina filayen da za a buga wasannin na gasar kofin duniya.

Ana zargin cewa leburori da dama ne suka rasa rayukansu sanadiyyar rashin ɗaukar matakan kare lafiyar ma'aikata a wuraren gina filayen wasanni.

Ƴan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Denmark sun ce za su yi wasa ne da kaya masu launin baƙi domin adawa da zarge-zargen take hakkin bil'adama na Qatar.

Kyaftin ɗin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ingila Harry Kane da na wasu ƙasashe tara na nahiyar Turai, za su sanya ƙyallen 'One Love' a damtsensu domin nuna adawa da dokokin auren jinsi guda na Qatar.

...

Asalin hoton, Getty Images

Paris da wasu biranen asar Faransa ba za su haska wasannin gasar a allunan nuna wasa ba, duk da cewa Faransa ce ta lashe gasar da ta gabata.

Mai hanoron kare hakkin masu auren jinsi guda na Birtaniya, Peter Tatchell ya ce an kama shi aka tsare sa'ilin da yake zanga-zangara adawa da take hakkin masu auren jinsi guda a Doha, babban birnin Qatar.

Gwamnatin Qatar ta ce zargin tsare shi da ya yi ba gaskiya ba ne.

humidity in Qatar

Me ya sa aka zaɓi Qatar a matsayin wadda za ta karɓi baƙuncin kofin duniya?

A shekara ta 2010 ne Qatar ta yi nasarar samun damar karɓar baƙuncin gasar kofin duniya bayan ta samu ƙuri'u 22 na shugabannin Fifa.

Ta yi nasara a kan Amurka, da Koriya ta kudu, da Japan, da kuma Australia, waɗanda su ma suka nemi karɓar baƙuncin gasar.

Ita ce ƙasar Larabawa ta farko da za ta ɗauki baƙuncin gasar.

An zargi Qatar da laifin bai wa jami'an Fifa cin hancin kuɗi dala miliyan 3 domin samun gyon bayansu, sai dai an wanke ta bayan wani bincike da aka gudanar na shekara biyu.

Shugaban Fifa na wancan lokaci Sepp Blatter ya nuna goyon bayansa ga Qatar a wancan lokacin, amma yanzu ya ce da alama Fifa din ta tafka kuskure.

Me masoya ƙwallon ƙafa ke tsammanin gani a Qatar?

Qatar, wadda ke da yawan mutane miliyan 2.9, na daga cikin ƙasashe mafiya arziƙi a duniya.

Ƙasar na da ɗinbin arziƙin man fetur da gas.

Ƙasar ta gina sabbin filayen wasa guda bakwai domin wannan gasa.

Ana kuma aikin gina sabbin otal otal 100 da sabuwar hanyar dogo da kuma hanyoyi.

Qatar

A matsayin ta ta ƙasa mai bin tsari na addinin musulunci, an taƙaita shan barasa, sai a mashaya ta musamman da kuma manyan otal otal. Leda ɗaya ta barasa za ta iya kai kuɗi dala 10.

Masu shirya gasar sun ce za a samar da barasa ga masu son sha a wani ɓangare na filayen wasa na tsawon awa uku kafin fara wasa, da kuma awa ɗaya bayan kammala wasa.

Haka nan za a iya samun barasa a dandalin masoya ƙwallon ƙafa mai iya ɗaukar mutum 40,000 da ke Doha, haka nan za a samar da wuraren da waɗanda suka bugu da barasa za su je su sarara.

Me ya sa ba za a yi gasar a lokacin zafi kamar yadda aka saba ba?

Doha

Za a buga wasannin ne tsakanin 20 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan Disamba - lokacin da yanayi a Qatar zai kasance kimanin digiri 25 na ma'aunin salshiyas.

Idan aka ce za a yi wasanni a watannin Yuni da Juli kamar yadda aka saba, za a yi ta ne a lokacin da yanayi ke kai wa sama da digiri 40 ko 50 a ma'aunin salshiyas.

A baya Qatar ta ce za a iya gudanar da gasar a ƙasar a lokacin zafi a cikin rufaffun filayen wasa masu na'urorin sanyaya yanayi, sai dai ba a amince da hakan ba.

Wace wahala za a fuskanta kasancewar za a yi wasanni a ƙarshen shekara?

Filayen wasa na Qatar

Wasanni kan yi wa ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƙasashen Turai yawa a watannin Nuwamba da Disamba. Za a kira manyan ƴan wasa da dama domin buga wa ƙasashensu wasa a gasar ta Qatar.

Manyan gasanni na Turai, kamar Premeir League na Ingila, da Serie A na Italiya, da La liga na Spain za su dakatar da wasanni mako guda gabanin fara gasar.

Za a ci gaba da gasannin ne bayan kammala gasar.