Fifa ta nemi kasashe su mayar da hankali 'kan kwallon kafa'

'Yan wasan Norway sun sanya riga da ke magana kan hakkin dan dama a ciki da wajen filin kwallo, ko da yake tawagar ba ta yi nasarar halartar gasar da za a yi a kasar ba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan wasan Norway sun sanya riga da ke magana kan hakkin dan dama a ciki da wajen filin kwallo, ko da yake tawagar ba ta yi nasarar halartar gasar da za a yi a kasar ba

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta aike wa duka kasashe 32 da za su halarci gasar cin duniya wasika, tana neman su mayar da hankali kan kwallon kafa, biyo bayan ce-ce-ku-cen da ake ta yi daf da fara gasar.

Mai masaukin baki Qatar na ta fama da suka kan matsayarta game da auren jinsi, da yancin dan adam da kuma yadda take tafiyar da lamarin ‘yan cirani da ke aikatau.

Za a fara gasar ne a ranar 20 ga watan Nuwamba.

Wasikar ta yi gargadin cewa bai kamata a a rika jayayya akwallon kafa ba, kan wani tunani ko kuma siyasa, kuma ba a amfani da ita wajen gyaran halayya.

Wasu ‘yan wasa sun shirya gudanar da zanga-zangar lumana gabanin fara wasannin.

Kyaftin din Ingila Harry Kane da wasu kyaftin tara na kasashen Turai za su sanya kambi nuna kauna.

‘Yan wasan Australia sun saki wai bidiyo suna shawartar Qatar da ta yi watsi da dokarta an sha’anin auren jinsi.

Birnin Paris na Faransa da wasu sauran birane sun ce b aza su haska wasannin kofin duniyar ba a manyan majigi, duk da cewa Faransan c eke rike da kofin.

'Yan wasan Norway sun sanya riga da ke magana kan hakkin dan dama a ciki da wajen filin kwallo, ko da yake tawagar ba ta yi nasarar halartar gasar da za a yi a kasar ba