Hikayata 2022: Labarai 25 da suka yi fice

Hikayata
Bayanan hoto, Matan da suka samu nasara a gasar Hikayata ta 2021

A yau Alhamis alkalan Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta Mata ta BBC Hausa, wato Hikayata, suke tafka muhawara don fitar da labarai guda uku da suka cancanci lashe gasar a bana. 

Da ma dai alkalan sun tantance labarai 15 daga cikin 25 da aka tura musu kafin yanzu. 

Alkalan uku za su tattauna ne don tantance tsaki da tsakuwa a kan wadanda ko wannensu ya riga ya zaba a matsayin labaran da suka ciri tuta. 

Alkalan su ne Dr Aisha Shehu Maimota, gwana a fannin kagaggun labarai kuma malama a sashen Hausa Kwalejin Shari’a da ilimin Addinin Musulunci ta Malam Aminu Kano da ke birnin Kano, da Dr Bashir Abu Sabe na tsangayar harsunan Najeriya da ke jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua da ke Katsina da kuma Malama Hauwa Maiturare wadda masaniya ce kuma mai nazari kan kagaggun labaran mata a birnin Kano kuma mai sharhi a kan adabin Hausa. 

Nan ba da jimawa ba ne dai za a sanar da marubuta ukun da alkalan suka zaba a matsayin wadanda suka zama taurarin Hikayata ta bana, kafin daga bisani a sanar da Tauraruwar gasar ta bana. 

Wannan ne dai karo na bakwai da ake shirya wannan gasa da nufin bai wa mata damar bayyana abubuwan da ke damunsu a rayuwa. 

A bara dai Aishatu Musa Dalili ce ta ci gasar, kuma ta samu kyautar kudi dala 2,000 da lambar yabo.

Labarai 25 da alkalai suka zaba:

  • Garar Biki
  • Haihuwar Guzuma
  • Al’ummata
  • Tsoro
  • Jarabta
  • A Mace Ta Gari Ake Uwa Ta Gari
  • A Dalilin ASUU
  • Fitsarin Fa’ko
  • ‘Yancina
  • Jarumar Mace
  •  Adalci
  •  Siyasarmu Ce
  •  Mai Kyau
  •  Kaikayi
  • Nakasa Ba Kasawa Ba Ne
  • Ummati
  • Komai Nisan Jifa
  • Fargar Jaji
  • Na Tuba
  •  Auren Biyan Bashi
  •  Baccin Rana
  • Labarin Rayuwata
  • Rayuwa
  •  Wannan Rayuwa
  • Kuskurena

Hikayata
Bayanan hoto, Aisha Mohammed Dalil ce ta lashe gasar Hikayata a shekarar 2021