Wa ya yi nasara, wa ya faɗi a zaɓen rabin wa'adi na Amurka?

Sa'o'i kaɗan bayan rufe rumfunan kaɗa ƙuri'a na farko, har yanzu ba a bayyana sakamakon wasu gundumomi ba a zaɓen tsakiyar zangon na Amurka, kuma har yanzu ana tababa kan jam'iyyar da za ta yi rinjaye a majalisar dattijai.

Ya zuwa yanzu dai jam'iyyar Republican na ganin haske, to amma ba za a ce ta samu gagarumar nasarar da take nema ba.

Ya zuwa yanzu sun rasa kujerar sanata ɗaya, a Pennsylvania, kuma za su buƙaci ta ƙwace jihohi biyu daga cikin uku, wato Nevada da Arizona da Georgia kafin ta ƙwace rinjaye a majalisar dattijan.

Ga wasu abubuwan da suka faru ya zuwa yanzu.

1. Republican na kan hanyar ƙwace rinjaye a majalisar wakilai

Duk da cewar jam'iyyar Democtrats ta samu nasara a wasu jihohin, amma akwai alamar cewa Republican ce ke kan hanyar ƙwace rinjaye a majalisar ta wakilai.

Sai dai ba a san irin tazarar da za ta bayar ba.

Wannan ya faru ne saboda ƙoƙarin da suka yi a zaɓen 2020, yanzu kujeru kaɗan ya rage Republicans ɗin ta lashe domin samun rinjaye.

Da zarar suka samu rinjaye ko yaya ne, za su samu damar dakatar da manufofin shugaba Biden kuma za su iya fara gudanar da bincike kan gwamnatinsa.

2. An ƙara zaɓen Ron DeSantis a Florida

Shekaru huɗu da suka gabata ne aka zaɓi Ron DeSantis a matsayin gwamnan jihar Florida, inda ya doke Andrew Gillum na jam'iyyar Democrat da ƙanƙanin rinjaye.

Bayan shekara huɗu yana mulki, inda ya yi amfani da tsari na masu ra'ayin mazan jiya, ciki har da batun ƴancin masu son yin sauyin jinsi, da adawa da kullen korona, yanzu ya sake samun nasara a cikin sauƙi.

Wannan zai bai wa gwamnan na Florida ƙwarin gwiwar tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa idan yana da buƙata.

A lokacin wani gangami da ya yi a daren ranar Talata, an ji mutane na sowa suna cewa zai yi mulkin ƙarin shekara biyu, wanda hakan ke nufin zai sauka ke nan bayan shekara biyu idan zai tsaya takarar shugaban ƙasa.

Amma idan yana son samun tikitin yin takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar ta Republican, hakan na nufin zai kara ke nan da tsohon shugaban ƙasa Donald Trump, wanda shi ma mazaunin Florida ne.

3. Trump na cikin tsaka mai wuya

Duk da cewar Trump ba ya cikin masu takara a wannan zaɓe, to amma tamkar yana ciki ne.

A yammacin da ya gabata, Donald Trump ya yi ƙwarya-ƙwaryar jawabi daga gidansa na Mar-a-Lago, inda ya yi iƙirarin cewa ƴan takaran da ya mara wa baya sun yi nasara.

To amma abin akwai sarƙaƙiya.

Yawancin manyan ƴan takaran Republican da Trump ya mara wa baya suna jin jiki.

A Pennsylvania Mehmet Oz ya rasa kujerar sanata.

Da alama wankin hula zai kai Herschel Walker dare a Georgia, sannan Blake Masters shi ne ke a matsayi na biyu a sakamakon da ke fitowa daga Arizona.

JD Vance na Ohio ne kawai ya samu nasara kai tsaye.

Da alama ƴayan jam'iyyar Democrats za su fara tantamar cancantar Donald Trump bayan wannan zaɓe, kuma idan har a mako mai zuwa ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa to zai iya shan wahala.

4. Ƴan takaran Democrats sun sha ƙasa

A 2018, Beto O'Rourke na Texas da Stacey Abrahams a Georgia sun sha ƙasa a takarar da suka tsaya amma sun yi farin jini wurin al'umma saboda rawar da suka taka a zaɓen.

Ƙoƙarin da suka yi wajen tara miliyoyin daloli na yaƙin neman zaɓe, da samun goyon bayan al'umma sun sanya ana kallon su a matsayin waɗanda za su fitar da jam'iyyar kunya a gaba.

Magoya bayansu sun zaci cewar za su yi nasara ba tare da wata wahala ba idan suka tsaya zaɓe a wannan karo, to amma dukkansu sun sha ƙasa.

Ms Abrams wadda Brian Kemp ya kayar da ita da ƙyar shekaru huɗu da suka gabata, ta ƙara shan ƙasa a hannunsa a wannan karo.

Mr O'Rouke ya sha mummunan kayi a hannun gwamnan jam'iyyar Republican Greg Abbott fiye ma da kayen da ya sha a hannun Sanata Ted Cruz a wancan karo.

Ya zama wajibi ga jam'iyyar Democrats su nemo wasu da za su shige masu gaba.