Mene ne zaɓen Amurka na tsakiyar zango? Bayani a sauƙaƙe

A ranar 8 ga watan Nuwamban 2022 ne Amurka za ta gudanar da zaɓen tsakiyar zango. Sakamakon zaɓen yana da tasiri ga sauran shekaru biyu na shugabancin Joe Biden, har ma gaba da haka.

Mene ne zaɓen tsakiyar zango kuma wane ne ake zaɓa?

Wannan zaɓe ne na ƴan majalisa, wanda ya ƙunshi majalisar wakilai da ta dattijai.

Ana gudanar da irin waɗannan zaɓuka ne bayan kowane shekaru biyu, kuma idan zaɓen ya faɗo a tsakiyar wa'adin mulkin shugaban ƙasa, ana masu laƙabi da 'zaɓen tsakiyar zango.'

Majalisar ce take samar da dokokin ƙasar. Majalisar wakilai ce take tattaunawa kan dokokin, yayin da ita kuma majalisar dattijai ke amincewa ko kuma soke dokokin, sannan ita ce ke amincewa da naɗe-naɗen muƙamai da shugaban ƙasa ke yi, sannan kuma tana da ikon binciken shugaban ƙasa.

Kowace jiha tana da sanatoci guda biyu, waɗanda ke da wa'adin shekara shida.

Su kuma ƴan majalisar wakilai suna da wa'adi ne na shekara biyu, sannan suna wakiltar ƙananan gundumomi.

Za a yi zaɓen dukkanin kujerun ƴan majalisar wakilan Amurka a watan Nuwamba, da kuma kashi ɗaya cikin uku na majalisar dattijai.

Haka nan za a yi zaɓen gwamnoni da na ƙananan hukumomi.

Wane ne zai iya yin nasara?

Jam'iyyar Democrats ce take da mafi rinjayen kujeru a zaurukan majalisar biyu a shekaru biyu da suka gabata. Wani abu da ya taimaka wa shugaba Joe Biden wajen samun amincewa na dokokin da ya gabatar.

To amma rinjayen da Democrats suke da shi a majalisar ɗan ƙalilan ne, wanda hakan ya sanya zaɓen zai yi zafi.

Sakamakon jin ra'yoyin mutane ya nuna cewa jam'iyyar Republican za ta iya ƙwace rinjaye a majalisar wakilai, sai dai da alama Democrats za su ci gaba da zamewa masu rinjaye a majalaisar dattijai.

Akasarin kujerun majalisar wakilan 435 ba su fuskantar barazanar sauya hannu zuwa wata jam'iyya, saboda haka nan kujeru 30 ne jam'iyyun biyu za su yi gogayya a kan su.

Wurare masu muhimmanci su ne yankunan karkara na jihohin Pennsylvania, da Ohio, da kuma North Carolina.

A majalisar dattijai kuwa da alama a kowace jam'iyya za ta iya yin nasara a kujeru 35 da za a yi takara a kansu.. Wurare masu muhimmanci su ne Nevada, da Arizona, sa Georgia da kuma Pennsylvania.

Yayin da ake sa ran cewa karawar za ta yi zafi, za a iya ɗaukar kwanaki kafin samun sakamakon zaɓen.

Waɗanne abubuwa ne ake taƙaddama a kai?

A farkon 2022 manyan abubuwan da ake tattaunawa a kai su ne batun shige da fice, da aikata laifuka, da kuma tsadar rayuwa, waɗanda za su janyo wa jam'iyyar Republican ƙuri'u.

Sai dai hakan ya sauya a watan Yuni, bayan da kotun ƙoli ta soke dokar ƴancin zubar da ciki, hakan ya ƙara wa Democrats farin jini, waɗanda su kuma ke goyon bayan bai wa mata ƴancin zubar da ciki, kuma suna amfani da wannan a wurin yaƙin neman zaɓe.

To amma a lokacin da batun hukuncin kotun ke sassautawa, ƴayan jam'iyyar Republican na taso da batun tashin farashin kayan masarufi, da shigowar baƙi da kuma hare-haren da ake kai wa al'umma.

Wane tasiri sakamakon zaɓen zai yi?

Zaɓukan tsakiyar zango kan zamo tamkar ma'auni ne na rawar da shugaban ƙasa mai ci ya taka, kuma sau da dama jam'iyyar da take mulki tana yin asarar kujeru.

Wannan ce damuwar shugaba Joe Biden, wanda karɓuwarsa a waurin al'umma take ƙasa da kashi 50% tun daga watan Agusta.

Idan jam'iyyar Democrats ta ci gaba da riƙe rinjayen, shugaba Biden zai samu damar ci gaba da ƙudurinsa na sauyin yanayi, da faɗaɗa shirin lafiya na gwamnati, da kare hakkin masu son zubar da ciki da kuma tsaurara mallakar bindiga.

Idan jam'iyyar Republican ta samu rinjaye a koda ɗaya daga cikin zaurukan majalisar dokoki, ƴayanta za su samu damar kawo ƙarshen waɗannan manufofi na Biden.

Kuma Republican za ta samu damar juya akalar kwamitocin bincike, saboda haka za su kawo ƙarshen binciken kutsen da magoya bayan tsohon shugaban ƙasa Donald Trump suka yi wa zauren majalisar dokoki na Capitol a ranar 6 ga watan Janairun 2021, duk da dai ana sa ran aikin kwamitin zai kammala ne a ƙarshen wannan shekarar.

Kuma za su iya ƙaddamar da bincike kan wasu lamurran, kamar na alaƙar kasuwanci tsakanin ɗan shugaba Biden da ƙasar China ko kuma janyewar dakarun Amurka daga Afghanistan cikin hanzari.

Haka nan shugaba Joe Biden zai rinƙa shan wahala wajen yin naɗe-naɗen gwamnati, ciki har da na shugaban kotun koli.

Samun rinjayen jam'iyyar Republican zai kawo cikas ga manufofin ƙasashen ƙetare na Joe Biden, musamman ma tallafin da Amurka ke bai wa Ukraine sanadiyyar kutsen ƙasar Rasha.

A nasa ɓangaren shugaba Biden zai zai iya yin amfani da ƙarfinsa na shugaban ƙasa wajen daƙile dokar zubar da ciki da shigowar baƙi da kuma na haraji.

Wane abu hakan zai haifar? Za a samu taƙaddama har zuwa lokacin zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisa mai zuwa.

Wane tasiri hakan zai yi ga zaɓen shugaban ƙasa na 2024?

Zaɓen tsakiyar zango zai iya bayyana wanda ake sa ran zai yi takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Republican a shekarar 2024.

Idan ƴan takara da ke samun goyon bayan Trump suka gaza yin tasiri a zaɓen, zai yi wahala jam'iyyar Republican ta ba shi damar sake yin takarar shugabancin ƙasa.

Su kuma gwamnonin jihohin Florida da Texas, Ron DeSantis da Greg Abbott na sa ran sake zaɓen su zai ƙara ingiza aniyarsu ta takarar shugabancin ƙasa.

Idan Democrats ta ci gaba da riƙe Michigan, da Wisconsin da Pennsylvania, hakan zai ƙara masu ƙwarin gwiwa wurin ganin an ƙara zaɓen Joe Biden karo na biyu a zaɓe mai zuwa.