Mbappe ya ci Juventus kwallo biyu a Champions League

Kylian Mbappe

Asalin hoton, Reuters

Kylian Mbappe ne ya ci wa Paris St-Germain kwallo biyu a wasan farko a cikin rukuni a Champions League, bayan da ta doke Juventus ranar Talata.

Kungiyar Faransa ta yi nasara a kan ta Italiya da ci 2-1 a wasan na hamayya da suka fafata.

Mbappe ya ci na farko bayan da Neymar ya saka masa kwallo, sannan ya zura na biyun bayan samun kwallo daga wajen Achraf Hakimi.

Dan kwallon tawagar Faransa ya kusan cin na uku rigis, amma duk kwallayen da ya buga daga sai su yi fadi.

Juventus ta zare daya ta hannun Weston McKennie wanda ya shiga fafatawar daga baya, Dusan Vlahovic ya samu damar farkewa, amma mai tsaron raga Gianluigi Donnarumma ya hana.

Juventus wadda ta yi ta kokarin farke kwallo, kadan ya rage Neymar ya kara na uku, sai dai Mattia Perin ya tare wadda ya so ya ci kungiyar Italiya.

Daya wasan rukuni na takwas Benfica ta doke Maccabi Haifa da ci 2-0.