Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Ba a biya mu kudin aikin zaben 2023 ba'
Wasu daga cikin ma’aikatan wucin-gadi da suka yi aikin zaben 2023 a Najeriya sun koka kan rashin biyan su kudaden alawus-alawus na aikin da suka yi.
Ma’aikatan wadanda suka ce suna da yawan gaske a fadin kasar sun nemi hukumar zaben, INEC ta taimaka ta biya su hakkokinsu.
A watannin Fabarairu da kuma Maris din shekarar 2023 ne aka gudanar da zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisu da kuma gwamnoni a Najeriyar.
Daya daga cikin irin wadannan ma'aikatan na wucin-gadi daga jihar Kano ya shaida wa BBC cewa a jihar kadai akwai abokan aikinsa 80 wadanda ba a biya su ba.
"Mun rasa gane abin da yake faruwa, daga cikinmu akwai wadanda ba a biya alawus din aikin zaben shugaban kasa ba akwai kuma wasu wadanda na gwamnoni ne ba a biya su ba.
Wasu sun yi kokarin gano abin da ke faruwa amma sai aka fada musu wai matsalar ta shafi duk mutane da lambobin asusun ajiyarsu na banki ya fara da "0" ne suka samu matsalar;
To sai dai kuma wasu masu irin wannan asusun sun yi aikin zaben shugaban kasa kuma an biya su" A cewar ma'aikacin wucin-gadin na INEC.
Ya ce kara da cewa ba su fahimci yadda wannan matsalar ta shafi biyansu hakkokinsu ba.
Shi ma wani ma'aikacin na wucin-gadi da har yanzu ya ce bai karbi kudin aikinsa ba, ya ce a zaben 2019 ma akwai wasu da irin wannan matsalar ta shafa kuma har yanzu ba a biya su ba.
"Akwai wasu abokaina wadanda na sani har yanzu ba su samu kudinsu ba tun zaben 2019 don haka mu ma muna fargaba kar kudadenmu su makale" in ji matashin.
Ita ma wata matashiya da ta yi aikin zaben na wucin-gadi ta ce ko da kudin horo da ake bayarwa ma ba ta samu ba a aikin da ta yi na zaben gwamna da kuma na shugaban kasa.
BBC ta tuntubi shugaban hukumar INEC reshen jihar Kano Ambasada Abdul Zango kan wannan batun kuma ya ce mutane kalilan ne matsalar ta shafa.
"Mun biya kashi 96 cikin dari na kudadensu saura kashi 4 da ba a biya ba sun samu matsalar asusun ajiya ne.
Wasu ba su bada lambobin asusun ajiyarsu ba sai dai na abokai ko 'yan uwansu, kuma da yake da na'ura ake biya, idan ta samu sunan jikin asusun ajiyar kudi bai tafi daidai da sunan mutumin da ya yi aikin zaben ba kudin ba za su shiga ba" a cewar Ambasada Abdul.
Ya kuma kara da cewa hukumar zabe ba za ta ji dadi ba ko da kuwa mutum daya ne ba a biya shi kudin aikinsa ba.
"Duk wanda ba a biya ba ya shigar da korafinsa zuwa ga hukumar zabe domin a shigar da sunansa cikin kundin bayanai da ake tattarawa domin mun kafa wani kwamiti da zai warware wannan matsalar zuwa karshen watan Mayun shekarar nan ta 2023.
Dukkan wadanda BBC ta yi magana da su sun bukaci hukumar zaben ta INEC ta biya su hakkinsu saboda a cewarsu aiki suka yi na sayar da rayukansu.
Baya ga jihar Kano, akwai wasu ma'aikatan daga jihohin Najeriya da dama wadanda suka ce har yanzu su ma ba a biya su ba.