Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙuri'un da ba za a iya bayaninsu ba a zaɓen Najeriya mai cike da taƙaddama
Lokacin da wani jami'in zaɓe ke sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na sashen da ya yi aiki a kudancin Najeriya, ba labari ne mai daɗi ba ga masu ƙalubalantar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyya mai mulki, Bola Tinubu.
Kuma kwanaki ƙalilan bayan an ayyana Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara - 'yan takarar da aka kayar sun shigar da ƙararraki game da sakamakon zaɓen.
Yanzu, wani binciken BBC ya gano shaidar da ke nuna cewa mai yiwuwa an yi maguɗi a waɗansu sakamakon zaɓe a muhimmiyar jihar Ribas da aka kai ruwa-rana.
Jami'in zaɓen da ya sanar da sakamakon, Dr Dickson Ariaga, bai mayar da martani ba da muka tuntuɓe shi.
Ga abubuwan da muka gano lokacin da muka yi nazarin sakamakon Najeriya da ake taƙaddama kansa.
Yaya ake ƙirga ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen Najeriya
A ranar 25 ga watan Fabrairu, 'yan Najeriya suka kaɗa ƙuri'unsu a dubban tashoshin zaɓe da ke faɗin ƙasar.
A dukkan tasoshin, ana sanar da ƙuri'un da kowanne ɗan takara ya samu a bainar jama'a, daga nan sai a ɗauki takardar sakamakon zuwa cibiyar tattara sakamako a matakin mazaɓa, kafin a wuce zuwa cibiyoyin ƙananan hukumomi.
Jami'in zaɓe daga kowacce ƙaramar hukuma, daga nan sai ya garzaya zuwa babban birnin jiha, inda ake sanar da sakamakon zaɓen a hukumance.
Karon farko a zaɓen Najeriya, hukumar zaɓe ta riƙa wallafa hoton takardar sakamakon zaɓen da aka yi ta intenet.
Hakan ta sanya, ana iya haɗa lissafi na alƙaluman duk sakamakon tashoshin zaɓen kuma a kwatanta da sakamakon da aka sanar a matakin jiha.
Abin da muka gano a jihar Ribas
Jami'anmu sun haɗa lissafin takardun sakamako na tasoshin zaɓe sama da 6,000 a jihar Ribas, inda 'yan adawa da yawa suka yi ƙorafi game da shi.
Yayin da sakamakon hukuma ya ba da rinjaye ƙarara ga Bola Tinubu na jam'iyyar APC mai mulki, lissafinmu na sakamakon ya nuna cewa Peter Obi na jam'iyyar Labour wato LP ne ya samu haƙiƙanin mafi yawan ƙuri'u a jihar da gagarumin rinjaye.
Mun gano ƙarin sama da 106,000 a ƙuri'un da a hukumance aka sanar cewa Bola Tinubu ya samu, lokacin da muka kwatanta da lissafinmu na sakamakon da aka fitar a tasoshin zaɓe - inda kusan aka ninka adadin da ya samu a jihar.
Saɓanin hakan, ƙuri'un Obi sun ragu da kusan fiye da 50,000.
Abu ne mai muhimmanci a bayyana ƙarara cewa ko da yake, mun bincike shafin intanet na hukumar zaɓe, don ganin kowacce takardar sakamako daga tashoshi 6,866 na jihar Ribas, amma ba mu iya samun sakamakon daga dukkansu ba.
Wasu an shigar da su cikin kuskure a intanet, wasu kuma sun ɓata.
Akwai kimanin kashi 5% na tasoshin zaɓe, da hotunan takardun sakamakon, suka yi matuƙar dishi-dishin da ba za mu iya karantawa ba.
A hankalce ana iya ɗauka cewa lissafin hukuma zai haɗa da irin waɗannan sakamako, tun da suna da takardun ainihi.
Akwai kashi 17% na tashoshin zaɓen da kwata-kwata ba a ɗora takardun sakamakon zaɓensu a intanet ba.
Da yawan waɗannan, suna iya kasancewa wurare ne da ba a yi zaɓen ba, saboda matsalolin tsaro ko kuma rashin kai kayan zaɓe.
Sauran kuma a wannan rukuni, suna iya kasancewa inda matsalolin na'ura suka hana jami'ai ɗora hotunan takardun.
Don haka ƙarara za a iya samun ƙarin tasoshin zaɓen da aka shigar cikin sakamakon ƙarshe na hukuma, amma binciken BBC bai lissafa da su ba.
Sai dai, waɗannan daɗin takardun sakamako za su kasance ƙari ne a jimillar ƙuri'un da kowacce jam'iyya ta samu, ba ragi ba.
Amma abin da muka gano shi ne, an yi matuƙar rage ƙuri'un Jam'iyyar Labour ta Peter Obi a jihar Ribas - lamarin da ba za a iya bayani kansa ba, ta hanyar kafa hujja da rashin takardun sakamakon da aka shigar a lissafin BBC.
To mene muhimmin bambancin?
Yankuna biyu ne suka fi fitowa fili.
Na farko, shi ne ƙaramar hukumar Oyigbo, inda muka gano:
- Ƙuri'un Bola Tinubu sun ninka har sau shida a sakamakon hukuma da aka sanar idan an kwatanta da ƙuri'un tashoshin zaɓe da BBC ta ƙirga
- An zabge rabin ƙuri'un Peter Obi
Ƙaramar hukuma ta biyu, inda muka gano wagegen saɓani ita ce Obio/Akpor mai maƙwabtaka.
- Sakamakon hukuma na Tinubu shi ne ƙuri'a 80,239, sai dai mun gano ƙuri'a 17,293 kawai ya samu bayan haɗa lissafin tashoshin zaɓe
- Adadin ƙuri'un da aka sanar Peter Obi ya samu su ne 3,829 kawai, amma BBC ta gano cewa ƙuri'a 74,033 yake da su a takardun sakamako.
Ta yaya aka samu waɗannan bambance-bambance?
Mun so sanin ta yadda bambance-bambancen nan mai yiwuwa suka faru a yayin tattara alƙaluman.
Kamar yadda aka yi bayani tun farko, dukkan takardun sakamakon tashoshin zaɓe, ana haɗa lissafinsu ne a shalkwatocin ƙananan hukumomi.
Mun gano wata takardar sakamakon hukuma da aka tattara lissafin ƙuri'un yankin Oyigbo, wadda wani jami'in zaɓe da wakilan jam'iyyu suka sanya wa hannu.
An ɗauki hotunan takardar da dama kuma an wallafa a shafukan sada zumunta.
Alƙaluman da ke cikin takardar sun kusa yin kama da lissafin da muka yi na ƙuri'un da 'yan takarar biyu (Obi da Tinubu) suka samu.
Wannan na iya zama ɗaya daga cikin takardun sakamako 23 da aka tattara daga ƙananan hukumomin jihar Ribas, kuma aka ɗauka aka kai babban birnin jihar, Fatakwal, don sanarwa a hukumance.
Da yake bayani ta talbijin da rediyo kai tsaye a gaban dandazon lasifikoki ranar 27 ga watan Fabrairu, jami'in zaɓe na Oyigbo, Dr Dickson Ariaga ya bayyana sunansa, kuma ya ce ya yi aiki da Kwalejin Ilmi ta Tarayya ta Omoku.
A sautin da aka naɗa, kalmar "Omoku" ba ta fito sosai ba, to amma Kwalejin Ilmi ta Tarayya ɗaya ce kawai a jihar Ribas.
Dr Ariaga daga nan ya sanar da sakamakon da kowacce jam'iyya ta samu cikin jerin abajadi, ciki har da na dukkan ƙananan jam'iyyu.
Duka sun yi daidai da bayanan da ke cikin takardar sakamako da BBC ta samu.
Sai dai lokacin da ya zo kan Tinubu, ɗan takarar APC maimakon ya ce 2,731 kamar yadda yake rubuce a hotonmu na takardar sakamako, amma sai ya karanto "16,630".
Jam'iyyar LP ta Peter Obi kuma, alƙaluma a nan ma sun sake canzawa, inda maimakon 22,289 da aka gani a kan takardar sakamako, sai ya sanar da "10,784", ƙasa da rabin ƙuri'un ɗan takarar.
Abu mai ɗaure kai game da Dickson Ariaga
Mun nemi iznin hukumar zaɓe, ko za mu iya magana da Dr Ariaga, amma ba su ba mu bayanansa ballantana su samo mana shi ba.
Mun kuma yi ƙoƙarin tuntuɓar sa ta hanyar jami'ar zaɓen da ta zauna kusa da Dr Ariaga, sai dai ta faɗa cewa ba ta da izinin magana da 'yan jarida.
Don haka, muka aika ɗan jarida Kwalejin Ilmi ta Tarayya da ke Omoku, mai nisan kimanin tafiyar sa'a biyu a mota arewa da birnin Fatakwal, inda ya ce yana aiki lokacin da yake gabatar da kansa.
Mataimakin shugaban kwalejin, Moses Ekpa ya faɗa wa BBC cewa: "Daga takardun bayananmu, kama daga takardun albashinmu da bayanan ma'aikatanmu, babu mai irin wannan suna a kwamfyutocinmu, kuma ba mu san wannan mutum ba."
Mun yi ƙoƙarin bibiyar sa a kafofin sada zumunta kuma daga bisani muka ci karo da wani shafin Fezbuk mai wani suna na wani mazaunin Fatakwal amma a adireshinsa na intanet (URL) yana amfani da sunan Dickson Ariaga.
Da muka kwatanta hoton da ke kan shafin da hotunan talbijin na Dr Ariaga ta hanyar amfani da manhajar Amazon Rekognition, mun yi dace, don kuwa sun yi daidai da kimanin kashi 97.2%, abin da ke nuna matuƙar yiwuwar cewa hotunan na mutum ɗaya ne.
Dr Ariaga bai amsa saƙonnin da muka aika ta hanyar wannan shafi ba.
Amma ta hanyar abokansa na Fezbuk mun yi nasarar magana da wani mutum wanda ya ce danginsa ne inda da farko ya ce zai taimaka mana.
Sai dai daga bisani ya daina amsa kiraye-kirayen da muka yi ta yi.
Martani daga hukumar zaɓe
Mun kai wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) waɗannan hujjoji da muka gano.
Mai magana da yawun hukumar zaɓe na yankin a Fatakwal, Johnson Sinikiem, ya faɗa mana cewa saboda "matuƙar ƙarancin lokaci da ma'aikata" sun ɗauki wasu mutane aiki ba tare da sun tantance takardun bayanan shaidarsu ba.
Da yake bayani kan Dr Ariaga, ya ce: "Idan ya gabatar da kansa a matsayin malami daga [kwaleji Omoku] amma aka iske saɓanin haka, to ya tabbata maras gaskiya."
Mun kuma tunkari shalkwatar inec a Abuja don jin amsarsu game da saɓanin da muka gano a sakamakon jihar Ribas.
Amma an faɗa mana cewa ba za su iya martani ba, saboda ƙararrakin da aka shigar don ƙalubalantar sakamakon zaɓen.
Tasiri a kan ɗaukacin zaɓen
Wannan wani al'amari ne guda ɗaya kawai a cikin jiha ɗaya ta kudancin Najeriya, inda shaidu ke nuna cewa an jirkita sakamakon zaɓen.
A karan kansu, sakamakon da aka canza, tabbas ba zai iya sauya akalar duka sakamakon zaɓen shugaban ƙasar ba.
Bola Tinubu ya lashe zaɓen shugaban ƙasa da ratar fiye da ƙuri'a 1.8m a kan babban abokin takara mafi kusa da shi, Atiku Abubakar na PDP.
Mun kuma duba wasu wurare, inda muka binciki sakamakon wasu ƙananan hukumomi na kudu maso yamma da arewacin Najeriya, sai dai ba mu samu irin wannan saɓani kamar na jihar Ribas ba.
Har yanzu dai, muna neman Dr Dickson Ariaga ya bayar da amsa ga abubuwan da wannan rahoto ya gano.
Ƙarin bayanan da rahoton ya tattaro daga Liana Bravo da Jemimah Herd da Jake Horton da kuma Kumar Malhotra