Hotunan ganawar Buhari da Barkindo ƴan sa'o'i kafin rasuwarsa

A ranar Talata da daddare ne Allah Ya yi wa Babban Sakataren Kungiyar kasashen da ke da arzikin man fetur, OPEC, Dr Muhammad Sanusi Barkindo rasuwa.

Rasuwarsa ta zo farat ɗaya, bayan da a ranar Talatar da rana ya kai wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyara a fadarsa ta Aso Rock da ke Abuja, tare da tawagar shugabannin Kungiyar OPEC.

Ga wasu hotuna na ganawar tasa da Shugaba Buhari a fadar Aso Rock.

Barkindo da Buhari

Asalin hoton, SUNDAY AGHAEZE

Bayanan hoto, A ranar Talata da misalin karfe 11 na safe ne Sanusi Barkindo ya kai ziyara fadar shugaban Najeriya.
Barkindo da Buhari

Asalin hoton, SUNDAY AGHAEZE

Bayanan hoto, Ya je yi wa Shugaba Buhari bankwana ne na sauka daga mukaminsa na shugaban ƙungiyar ƙasashe masu arzikin fetur ta OPEC.
Barkindo da Buhari

Asalin hoton, SUNDAY AGHAEZE

Bayanan hoto, Shugaba Buhari ne dai ya umarci ma'aikatar kula da albarkatun man fetur ta kasar (NNPC) da ta shirya gagarumar liyafa ga Sunusi Barkindo
Barkindo da Buhari

Asalin hoton, SUNDAY AGHAEZE

Bayanan hoto, Shugaba Buhari ya ce masa: "Lokacin mulkinka a OPEC ya kasance cike da kalubale, kasancewar duniya na fama da matsalolin tattalin arziki wadanda suka shafi harkar man fetur.
Barkindo da Buhari

Asalin hoton, SUNDAY AGHAEZE

Bayanan hoto, ''To amma duk da haka ka nuna ƙwazo matuka a jagorancinka'' in ji Shugaba Buhari.
Barkindo da Buhari

Asalin hoton, SUNDAY AGHAEZE

Bayanan hoto, Shugaban NNPC Mele kyari na daga cikin wadanda suka yi wa Barkindo rakiya zuwa fadar Shugaba Buhari.
Barkindo da Buhari

Asalin hoton, SUNDAY AGHAEZE

Bayanan hoto, A jawabinsa, Barkido ya danganta nasarorin da ya samu a OPEC da shawarwari da kuma goyon baya da ya samu daga Shugaba Buhari tare da hadin kan mambobin kungiyar.
Barkindo da Buhari

Asalin hoton, SUNDAY AGHAEZE

Bayanan hoto, ''A lokuta da dama nakan tuntubeka, a matsayinka na tsohon masanin harkokin kungiyar OPEC'', in ji Sunusi Barkindo.
Barkindo da Buhari

Asalin hoton, SUNDAY AGHAEZE

Bayanan hoto, Ya kara da cewa duk kasar da na shiga a fadin duniya a matsayina na Sakataren OPEC tambayar farko da shugabanta ke yi min ita ce ''ina dan uwana Shugaba Buhari''?
Barkindo da Buhari

Asalin hoton, SUNDAY AGHAEZE

Bayanan hoto, Daga karshe ya gode wa Shugaba Buhari saboda damar da ya ba shi ta jagorantar OPEC, tare da yin alkawarin cewa Najeriya za ta ci gaba da rike matsayinta da aka santa da shi a kungiyar.