Tambayoyi da amsoshi kan Brazil a Gasar Kofin Duniya a Qatar

Asalin hoton, Getty Images
Brazil na fatan lashe Kofin Duniya na shida jumulla a wasannin da za a gudanar a Qatar daga 20 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan Disambar 2022.
Ga wasu tambayoyi da amsoshi da ya kamata ku sani kan Brazil
'Yan wasa nawa aka amince Brazil ta je da su Qatar?
A watan Yuni aka yanke shawarar kowacce tawaga ta je da 'yan kwallo 26 maimakon 23 a Gasar Kofin Duniya, bayan da cutar korona ta kai koma baya a fannin tamaula.
Lokacin wasu kan killace kansu idan sun kamu da annobar, sannan ga yawan rauni, bayan da 'yan kwallo ke buga wasanni da yawa.
Wadanne 'yan wasa ne za su wakilci Brazil a Qatar?
Ranar 7 ga watan Nuwamba Brazil ta bayyana 'yan wasa 26 da za su buga mata Gasar Cin Kofin Duniya da za a yi a Qatar.
Masu tsaron raga: Alisson (Liverpool), Ederson (Manchester City), Weverton (Palmeiras)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Brazil kan zaba tsakanin Alisson da Ederson, amma Alisson ne kan gaba, wanda shi ne ya tsare mata raga a wasannin neman gurbin shiga gasar kofin duniyar.
Masu tsaron baya: Bremer, Alex Sandro (both Juventus), Eder Militao (Real Madrid) Marquinhos (Paris St Germain), Thiago Silva (Chelsea), Danilo (Juventus), Daniel Alves (Pumas), Alex Telles (Sevilla)
Zakakuri Thiago Silver da Marquinhos suna daga cikin wadanda za su tsare bayan Brazil, an yi mamaki da aka tafi da Dani Alves, mai shekara 39.
Masu buga mata tsakiya: Bruno Guimaraes (Newcastle United), Casemiro, Fred (both Manchester United), Everton Ribeiro (Flamengo), Fabinho (Liverpool), Lucas Paqueta (West Ham United)
Guimaraes ya shiga tawagar kan rawar da yake takawa a Newcastle United, shi kuwa mai shekara 33 da ke taka wa a Everton, Ribeiro zai je Gasar Kofin Duniya a karon farko.
Masu ci mata kwallaye: Antony (Manchester United), Gabriel Jesus, Gabriel Martinelli (both Arsenal), Neymar Jr (Paris St Germain), Pedro (Flamengo), Raphinha (Barcelona), Richarlison (Tottenham Hotspur), Rodrygo, Vinicius Jr (both Real Madrid)
'Yan wasa tara aka gayyata a wannan gurbin kuma matasa masu taka leda a Turai, in banda mai wasa a Flamengo, Pedro, wanda ya taimakawa kungiyarsa ta lashe Copa Libertadores da cin kwallo 12.
Wasu karin bayanai da ya kamata ku sani
Matakin Brazil a jadawalin FIFA: Ta daya daga Agustan 2022
Matakin Brazil a nahiyarta ta CONMEBOL: Ta daya
Kofin duniya da ta dauka: 5
Ta halarci Gasar Cin Kofin Duniya 21 na karshen nan a Rasha a 2018
Yadda ta samu gurbin zuwa Qatar: Ta ci wasa 14 da canjaras uku ta daya a CONMEBOL
Kociyanta: Tite (Brazil) tun daga Yunin 2016
Fitattun ‘yan wasa: Neymar (Paris Saint-Germain / France), Marquinhos (Paris Saint-Germain / France), Vinicius Jr. (Real Madrid / Spain)
Wadanne fitattun 'yan wasa ne da ba su a Brazil a Qatar?

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Liverpool, Roberto Firmino ba zai je Gasar Kofin Duniya ba, duk da cewar yana gaban wadanda aka gayyata a gurbin da yake buga wa a yawan cin kwallaye da bayar wa a zura a raga a bana a Premier League.
Mai tsaron bayan Arsenal, Gabriel Magalhaes bai samu shiga tawagar ba duk da cewar yana taimakawa Arsenal, wadda yanzu ke kan teburin Premier League.
Dan wasan Aston Villa ba zai je Gasar ba, sakamakon jinya da yake yi.
Wadanne kasashe Brazil za ta kara da su a Qatar a wasan rukuni?
Brazil tana rukuni na bakwai da ya hada da Serbia da Switzerland da kuma Kamaru.
'Yaya jadawalin wasannin rukuni na bakwai yake?
Wasannin farko a rukuni ranar 24 ga watan Nuwamba
- Switzerland da Kamaru
- Brazil da Serbia
Wasa na biyu a rukuni ranar 28 ga watan Nuwamba
- Kamaru da Serbia
- Brazil da Switzerland
Wasa na uku a rukuni ranar 2 ga watan Disamba
- Kamaru da Brazil
- Serbia da Switzerland
Wadanne 'yan wasa ne suka buga mata Gasar Kofin Duniya a 2018?
Masu tsaron raga: Alisson (Roma), Ederson (Manchester City), Cassio (Corinthians).
Masu tsaron baya: Thiago Silva (Paris St Germain), Miranda (Inter Milan), Marquinhos (Paris St Germain), Marcelo (Real Madrid), Filipe Luis (Atletico Madrid), Fagner (Corinthians), Pedro Geromel (Gremio), Danilo (Manchester City).
Masu buga tsakiya: Paulinho (Barcelona), Casemiro (Real Madrid), Philippe Coutinho (Barcelona), Renato Augusto (Beijing Sinobo Guoan), Fred (Shakhtar Donetsk), Fernandinho (Manchester City), Willian (Cgelsea).
Masu ci mata kwalllaye: Neymar (Paris St Germain), Douglas Costa (Juventus), Gabriel Jesus (Manchester City), Roberto Firmino (Liverpool), Taison (Shakhtar Donetsk). (Compiled by Rohith Nair in Bengaluru, editing by Ed Osmond)











