An shigar da Netanyahu tiyata yayin da zanga-zanga ke tsananta a Isra'ila

Asalin hoton, AFP
Dubban masu zanga-zanga sun yi cincirundo a wajen majalisar dokokin Isra’ila a Birnin Kudus, kafin mataki na gaba na neman amincewa da shirin gwamnatin kasar mai cike da takaddama na yin sauye-sauye a bangaren shari’a.
A yau Lahadi ne za a fara muhawara a kan abu na farko kan sabbin matakan- wanda mataki ne da zai takaita ikon Kotun Kolin kasar kan soke duk wata doka da kotun ke ganin ba ta dace ba.
Yayin da ake gangamin, shi kuwa Firaminista Benjamin Netanyahu, wanda ya kafe kan yin sauye-sauyen na can kwance a asibiti za a yi masa tiyata a zuciya.
Bayan karin wata zanga-zangar da gangami aka yi ta yi a fadin kasar ta Isra’ila a jiya Asabar, a yau Lahadi, zanga-zangar za ta mayar da hankali ne kacokan a kan majalisar dokokin Isra’ilar, mai zaure daya.
‘Yan majalisar za su yi muhawara ne a kan dokar wadda idan aka amince da ita, za ta yi matukar takaita ikon Kotun Kolin kasar kan soke duk wata doka da hukunce-hukunce na gwamnati.
Shugabar jam’iyyar hamayya ta Isra’ilar ta labour, kuma tsohuwar minista
- Merav Michaeli ta gaya wa BBC cewa ta shiga zanga-zangar ne domin kasar tana wani siradi, wanda kuma tana bukatar ta bayyana matsayinta kan abin da ake ciki.
Ta ce, ''Wannan shi ne yaki na biyu na neman ‘yancin Isra’ila, kuma dole ne mu yi nasara a kai. Akidar kishin Yahudawa ta bayyana karara – gida ga al’ummar Yahudawa, ba tare da wani bambanci ga kowa ba, ba bambanci a tsakanin mace ko namiji, ko jinsi ko addini ko launi, ko ma duk wani abu.''
Ta kara da cewa, ''Idan ba mu yi yaki don wannan ba, wannan ba kasar Isra’ila ba ce – kuma dole ne mu yi nasara a kai
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shugabar ta jam’iyyar Labour ta ce, sauye-sauyen na da hadarin gaske da illa sosai ga kasarta da alummarta.
Sai dai kuma a wani lamari na sammatsi ga Firaministan Isra’ilar, Benjamin Netanyahu, ya bayyana a wani hoton bidiyo da ya fitar cikin dare , inda a ciki yake cewa ana dab da yi masa aikin zuciya domin makala masa wata ‘yar na’ura da za ta rika taimaka wa bugun zuciyarsa.
To amma ya ce yana da kwarin gwiwar cewa za a sallame shi daga asibitin da wuri har ya samu damar halartar zaman majalisar dokokin lokacin da za a kada kuri’a kan dokar sauye-sauyen a bangaren shari’a.
Duk da zanga-zangar da aka shafe watanni ana yi a kasar kan wadannan sauye-sauye, gwamnatinsa ta yi biris, sai ma kafewa da ta ke kara yi a kai da cewa ana bukatar sauyin domin dakile duk wani kokari na bangaren shariar wajen wuce gona da iri.
Yayin da su kuwa masu ja da sauye-sauyen ke cewa matakin zai bayar da kafa ga gwamnati ko bangaren zartarwa ya rika wuce iyaka ko yi wa mulki karen tsaye










