Lokuta huɗu da turmutsutsu ya haifar da rasa rayuka a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Laraba ne aka samu wani turmutsutsu a jihar Oyo a kudu maso yammacin Najeriya, wanda ƴansanda suka tabbatar da mutuwar yara 35, sannan wasu suka jikkata.
An shirya taron ne - kamar yadda aka saba yi duk shekara - domin nishaɗin yara, sannan a raba musu kyaututtuka da kuɗaɗe da abinci, kamar yadda iyayen wasu daga cikin yaran suka bayyana.
Sai dai a bana, wannan shi ne karo na huɗu da aka samu irin hakan, inda turmutsutsun mutane a taruka suka jawo asarar rayuka.
Ga sauran lokacin da aka samu irin wannan turmutsutsu a Najeriya cikin shekarar 2024:
Rabon shinkafar kwastam a Legas

Asalin hoton, FB/Nigeria Customs
A cikin watan Fabarairun 2024 ne Hukumar kwastam ta Najeriya ta ƙaddamar da rabon shinkafar da ta ƙwace ga al'umma kan farashi mai rahusa.
Sai dai bayan fara rabon, rundunar ta fitar da sanarwar dakatar da shirin.
Wata sanarwa da hukumar kwastam ɗin ta fitar ta tabbatar da rahotannin da mutane suka bayar na cewa wasu sun rasa ransu yayin da wasu kuma suka samu raunuka sanadiyyar turmutsutsin da aka samu a ranar farko ta rabon shinkafara.
A cikin sanarwar, mai magana da yawun hukumar, Abdullahi Maiwada ya ce "dandazon mutanen da suka taru sun ɓalla shingen da aka gindaya domin samun shinkafar.
"Abin takaici shi ne a lokacin turmutsutsun an samu rasa rayuka da raunuka".
Dubban mutane ne suka yi wa ofishin kwastam da ke Legas domin sayen buhun shinkafa mai girman kilogiram 50 a kan kuɗi naira 10,000.
A lokacin farashin irin wannan buhun shinkafa ya kai naira 70,000 a kasuwa.
Rabon sadaka a Bauchi

Asalin hoton, AISHA ABDULLAHI FAMILY
A jihar Bauchi da ke arewa maso gabas, aƙalla mutum bakwai suka rasu lokacin da wani ɗan kasuwa yake raba kuɗin sadaka.
Cikin waɗanda suka rasu har da yarinya ƴar shekara takwas.
Wani attajiri ne ya tara mutane domin raba musu kuɗi kimanin naira 5,000 ga kwanne mutum.
Dandazon mutane ne suka taru domin karɓar sadakar, sai dai ba da jimawa ba abubuwa suka rikice.
Rundunar ƴansandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutum bakwai a lamarin, wanda ya faru a kan titin Jos Road a garin na Bauchi, sai dai mutane da dama sun ce adadin waɗanda suka mutu ya zarce wanda hukumomi suka bayyana.
Wani magidanci, mai suna Babangida Adamu, wanda ya rasa ɗiyarsa mai suna A'isha a sanadiyyar turmutsitsin ya shaida wa BBC cewa: "Ina zaune sai wata yarinya ta zo wurina tana kuka, ta ce min na je asibiti na ga abin da ke faruwa, ina zuwa sai na ga ƴata ta rasu. Mun yi jana'izarta tare da sauran waɗanda suka rasu."
Rabon shinkafa a Nasarawa

Asalin hoton, Nasarawa State University
A watan Maris, wasu mata ɗalibai biyu sun rasu a jihar Nasarawa da ke maƙwabtaka da babban birnin tarayya Abuja a wurin raba shinfaka da gwamnatin jihar ta shirya. Bayan mutuwar, aƙalla mutum 23 kuma sun jikkata.
A lokacin rabon kayan abincin ne dandazon mutane suka ɓalla shingen da aka gindaya domin samun abincin.
Hotunan bidiyo sun nuna yadda mutane suka ture jami'an tsaro inda suka kutsa cikin rumbun da shinkafara ke ajiye.
A wata sanarwa da gwamnan jihar, Abdullahi Sule ya fitar, ya ce ya kaɗu da labarin turmutsutsun.
Daga nan ya umarci hukumomin makarantar su yi bincike domin gano gano abin da ya haifar da lamarin.











