Yara 35 ne suka rasu sakamakon turmutsutsu a Ibadan - Ƴansanda

Asalin hoton, BBC Yoruba
Rundunar ƴansanda jihar Oyo ta ce an samu gawar ƙananan yara 35 sannan guda shida suna cikin yanayin mutu-kwakwai rai-kwakwai a asibitoci daban-daban.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Alhamis, rundunar ta ce ta kuma kama mutum takwas masu alaƙa da shirya taron da ya janyo turmutsutsun ranar Laraba, ciki har da tsohuwar mai ɗakin Sarki Ooni na Ife, Naomi Agunwusi.
Tun bayan mummunan turmutsutsu da aka samu a wata makarantar Islamiyya a birnin na Badun ake ta nuna yatsa ga tsohuwar mai ɗakin Sarki Ooni na Ife, Naomi Silekunola Ogunwusi da mai gidan rediyon Agidigbo FM, Oriyomi Hamzat waɗanda su ne ake yi wa kallon haddasa al'amarin.
Tsohuwar mai ɗaƙin Sarki Ooni na Ife, Naomi Silekunola Ogunwusi ce dai ke shirya wannan bikin na al'ada a duk shekara inda jama'a musamman yara ke haɗuwa lokacin hutu su yi wasanni da yi wa ubangiji godiya ta an shekara lafiya.
Bayanai sun nuna cewa wani gidan rediyo mai suna Agidigbo FM ne ya taka babbar rawa wajen tallata taron Misis Naomi na shekara-shekarar.
Rahotanni sun ce har lokacin da ake cikin turmutsutsun a wurin taron, gidan rediyon bai daina watsa shirye-shirye a kan taron ba wani abu da ake ganin ya ƙara sanya jama'a yin tururuwa zuwa wajen.
To sai dai shugaban darektocin gidan rediyon, Mista Abdulwahab, a wata sanarwa da gidan rediyon ya fitar ranar Laraba, ya ce Agidigbo FM ba ita ce ta shirya wannan taro ba.
"Ya kamata jama'a su sani cewa Agidigbo FM ɗaya ce kawai daga cikin gidajen rediyon da suka watsa shirye-shiryen gidauniyar WINGS Foundation", da Misis Naomi ke ɗaukar nauyi.

Asalin hoton, Others
Yadda turmutsutun ya kasance

Asalin hoton, Google
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Lamarin dai ya faru ne a farfajiyar wata makarantar Islamiyya a unguwar Bashorun da ke birnin Badin na jiyar Oyo ranar Laraba.
Tsohuwar mai ɗakin Sarki Ooni na Ife, Misis Naomi ce ta shirya taron kamar yadda ta saba yi a birnin Akure duk shekara.
Rahotanni dai sun ce tsabar zafin da ke filin da jama'a suka cunkusa ne ya haddasa ɗaukewar numfashi ga ɗaruruwan mutane musamman yara abin da ya sa su ƙoƙarin neman hanyar fita domin samun numfashi.
Wasu rahotannin kuma sun ce watsa shirin da ake yi a gidan rediyon na Agidigbo FM ne ya sa ɗaruruwan jama'a ƙara yin cincirindo zuwa wurin taro abin da ya haifar da turmutsutsu.
Har kawo yanzu dai babu wasu alƙaluma sahihai daga hukumomi dangane da adadin yaran da suka rasu ko jikkata, duk da wasu jaridun Najeriya na rawaito cewa ana fargabar yara fiye da 30 sun mutu.
Wata sanarwar kwamishinan watsa labaran jihar, Dotun Oyelade, ta ce an kwashi wasu daga cikin waɗanda suka samu raunuka zuwa asibitoci daban-daban da ke ƙwaryar birnin domin kula da lafiyarsu.
"Ana kira ga iyayen da ke neman inda 'ya'yansu suke da su duba asibitocin da suke kwance domin tantance ko suna wuraren'' inji kwamishinan watsa labaran jihar.
Gwamnan jihar ta Oyo, Seyi Makinde, ya wallafa wani sako a shafinsa na Twitter wato X, inda ya ce an ɗauki ƙwararan matakai don ganin hakan bai sake faruwa ba, kana za a gudanar da bincike don gano ainihin abun da ya faru.
Ya ƙara da cewa za a hukunta duk wanda aka gano yana da hannu a faruwar bala'in.
Turmutsutsu biyar da suka faru a Najeriya
Ba wannan ne karon farko da turmutsutsu irin wannan ke janyo mutuwar mutane a Najeriya ba. Ga wani jerin turmutsutsun da suka janyo rasa rayuka da jikkata a ƙasar.
- A watan Maris din wannan shekara wasu dalibai mata guda biyu sun mutu a Jami'ar Jihar Nasarawa da ke Keffi kusa da Abuja, a lokacin wani rabon tallafin shinkafa da gwamnan jihar ya yi. Akalla mutane 23 ne suka jikkata a lokacin.
- Bayan kwana uku a Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriyar, akalla mutane bakwai ne suka mutu a wani turmutsutsu na daban, yayin da wani dan kasuwa ke rabon tallafi.
- Kafin wannan, a watan Fabrairu ma kimanin mutane biyar sun mutu a Legas inda hukumar kwastam ta Najeriyar ta yi gwanjon shinkafar da ta kama a kan farashi mai rahusa.
- Turmutsutsu mafi muni da watakila za a iya cewa an samu shine a watan Mayun 2022 lokacin da mutane 31 suka mutu a wani taron bayar da tallafi da wata coci ta shirya a jihar Ribas, da ke kudancin Najeriyar.
- A shekarar 2014 ma yayin da hukumar Kula da Shige da fice ta kasar ke tantance masu neman aiki mutum dubu biyar, sai da mutum goma sha shida suka mutu, sakamakon turmutsutsu. Dubban daruruwan masu neman aiki ne suka yi dafifi a wurin tantancewar wanda manazarta suka ce ba a yi shiri sosai ba.











